Yadda ɗan adaidaita ya tsinci ₦230,000 kuma ya mayarwa fasinjan abinsa: Abun A Yaba

 Yadda ɗan adaidaita ya tsinci ₦230,000 kuma ya mayarwa fasinjan abinsa

Mutanen kirki ba sa ƙarewa a doron ƙasa.

Yayin da al’umma ke cikin halin damuwa na rashi da talauchi, da neman abin da za’a kai baka don a rayu.

Hakan bai sanya jarimin saurayin nan wato SANI MUSA, wanda akafi sani da (Na Bara) mai sana’ar adaidaita sahu (keke napep) mayar wa OBINNA da kudin sa da ya manta dasu a keken da yake sana’a da ita ba jiya litinin a garin Zaria.

Wannan lamarin ya faru ne yayin da direban keke napep din wato SANI yaga daurin bakar leda lokacin da yake sauke fassinjar sa a kasuwan dan magaji, inda ya tambayi matar da zata sauka ko nata ne ledar tace masa a’a.

Sai direban ya tafi da ledar bayan ya tsaya don duba maine ne a ciki yaga tarin zunzurutun kudi har N230,000 tare na’urar lissafi wato calculator da littafi mai dauke da sunayen mutane.

Jarimin matashin bai qasa a guiwa ba, sai ya garzaya gidan Radiyon KSMC wato Queen Fm Zaria don a cigita ko Allah yasa mai kudin yazo ya amsa abin sa.

Da yin sanarwan babu jimawa OBINNA mai sana’ar siyar da magunguna a Chemist suka garzayo don haduwa da wannan matashi wato Sani kuma ya bashi kudin sa kamar yadda kuke gani a hoton dake biye.

Obinna ya bayyana cewa shi kansa an aike shi ne don yakai saqo ba tare da sanin mai ke cikin ledar ba, sai da ya tabbatar ya mance da ledar a Keke napep da ya hawo daga Emanto zuwa Pz

 

Inda ya sanar wa mai gidan shi abin da ya faru, babu jimawa sai sukaji labarin ana cigiya inda suka je don ansar kudin nasu.

A don haka muke addu’an Allah ya yawaita mana matasa irin SANI MUSA wanda suke tsoron Allah ta hanyar kiyaye dokokin sa. Ameen

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top