YADDA ZAKAYI ONLINE TRAINING NYIF IDAN SUN TURAMA SAKON GAYYATA DAGA NYIF.

 YADDA ZAKAYI ONLINE TRAINING NYIF IDAN SUN TURAMA SAKON GAYYATA DAGA NYIF.

Daga Ahmed El-rufai Idris 

Da farko idan ka samu sakon gayyata karbar horo acikin imel adireshin dinka da kayi rijistar neman rancen asusun saka jarin matasa najeriya NYIF. 

ka natsu ka duba da kyau akwai link acikin sakon da aka tura maka a imel dinka zakayi amfani dashi wurin downloading ZOOM METTING Application,da shi zakake kallon duk abubuwan da ake yi. 

Zaka shiga application na zoom domin kayi rijista, akwai username da password naka da aka tura maka acikin sakon dake akan imel dinka, kana shigar dasu application na zoom zai bude zaka shiga kana Kallon duk abubuwan da akeyi a Class din.

Ana so ka halarci training din sannan akwai karuwa sosai zai amfani ka Kuma idan kana sauraren training din kar ka sauka daga kan wayar, ko kayi call, dan zai mayar da kai baya.

zasu turo maka link da zaka cike attendence form din.Idan kuma basu turo maka a lokacin ba, sai kayi hakuri zasu tura maka ta email daga baya, bayan kwana biyu.Idan ka cike attendance form, daga nan zasu turo maka Certificate ta email dinka.Shike nan, sai kuma batun kudin,zasu aika da sunan ka da lambar dake jikin certificate da duk abin daya shafi ka izuwa Nirsal Microfinance

Wannan shirin na asusun saka jarin matasa najeriya NYIF shiri ne da shugaba Buhari ya kawo domin taimaka wa matasa daga kan masu shekaru 18 zuwa 35, domin a basu rance su gina kansu, su farfado da sana’o’i domin samun hanyar rayuwa.

Shugaba Buhari ya bayar da Naira biliyan 75 ne akan wannan shirin ta hannun Ministry of Youth And Sports Development, karkashin jagorancin Mr. Sunday Dare.

Duk shekara za’a bayar da Naira biliyan 25 ga matasan Nigeriya, kudin zai kare ne a dai dai lokacin da Baba zai sauka I gayyata ba kada su damu kansu suyi hakuri za’a tura musu insha Allahu, kada mu manta yau aka fara gudanar da karbar horon nan, binciken da nayi shine za’a cigaba da turawa mutane har zuwa karshen satin nan, abin dasu batch by batch ne Allah yasa kowa ya samu wannan rancen kudin.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top