Yadda Zaku Duba Sakamakon Jarrabawarku ta WAEC A Sakon Message: Education

Yadda Zaku Duba Sakamakon Jarrabawarku ta WAEC A Sakon Message: Education

  Wannan tsarin yana daga cikin sababbin tsare-tsare da hukumar ta WAEC ta samar domin bunƙasa harkokin jarrabawar a faɗin ƙasashe guda 5, wadanda suke rubuta jarrabawar a nahiyar yammacin Afirka, da suka haɗarda Najeriya, Ghana, Sierra Leone, Gambia da kuma ƙasar Liberia.

  Tsarin bai keɓanta ga wani kamfanin sadarwaba, ma’ana kowanne irin layin waya kake da shi daga cikin layukan MTN, Airtel da kuma Glo, to zaka iya duba sakamakon jarrabawar taka da shi, matuƙar dai akwai katin kira da bai gaza Naira 30 ba a Asusun wayar ta ka.

 

   Abin da zaka yi kawai shi ne :

• Ka shiga gurin Rubuta sakon kar takwana ( Create New Message) na wayarka,

•Bayan ka shiga, sai ka Rubuta WAEC* Exam Number ɗinka*PIN ɗinka*Shekarar da kayi jarrabawarka

      Ga misalin yadda zaka Rubuta saƙon a ƙasa 

WAEC*4230204909*224466119002*2021

• Bayan ka Rubuta saƙon Message ɗin, sai ka tura zuwa lambar 32327, (Za’a cire Naira 30, daga cikin Asusun wayarka, kafin a turo maka Sakamakon Jarrabawar ta ka).

Abin Lura : Zaka sami PIN ɗinka a jikin Exam Card ɗinka.

   Kuma Idan kaduba sakamakon jarrabawar ta ka sau 3, to shikenan wannan PIN ɗin da aka baka na kyauta sun tashi daga Aiki, Saboda haka idan kanaso ka ƙara duba Sakamakon Jarrabawarka to dole sai ka sayi WAEC Scratch Card.

   Ku sani : Zaku iya duba Sakamakon jarrabawarku ta SSCE tareda G.C.E. dukka da wannan tsarin.

     Sannan yana da kyau ku lura da wadannan 

A1 na nufin Excellent.

B2 na nufin Very Good.

B3 na nufin Good.

C4 na nufin Credit.

C5 Itama tana nufin Credit.

C6 Itama tana nufin Credit.

D7 kuwa na nufin Pass.

E8 itama tana nufin Pass.

F9 Kuma na nufin Fail.

Wannan shi ne taƙaitaccen bayani game da yadda za ku duba sakamakon jarrabawar ku ta WAEC, ta hanyar saƙon Message.

    ASOF tana muku fatan samun Nasara.

Daga : MiMiftahu Ahmad PandahMiftahu Ahmad PandaaMiftahu Ahmad PandaAssistant ASOF National Secretary General).

Kebbi State University Ksusta to introduce medicine, medical doctor and other health courses.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top