Zaman Makoki complete Hausa Novel

 ZAMAN MAKOKI-Page1-

to-end
OCTOBER 23, 2016 | RASHIDATKARDAM | 2
COMMENTS
[4:53PM, 9/16/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
*Na*
*Ummieluff*
*Rash Kardam*
_Bissmillahi rahmanu rahim_
_Dukkan yabo ya tabbata ga ubangijin sama
da k’asa, mai raya kuma mai kashewa_
*Tsokaci*
_Wanna labari k’agagen labari ne munyi shi
sabida abunda yake faruwa a wannan zamani
namu a gidan rasuwa, in har yazo iri d’aya da
labarin ki/ka to sai ku gyara ba wai dan
tozarci mukayi ba sai dan samun gyara aciki
al’umma. Ya Allah muna rok’anka ka bamu
ikon farashi mu kuma gama lafiya Amin._
*Gamasu gyara k’ofa a bud’e take muna
sauraronku don ko da yaushe mu masu
kuskure ne sai fatan Allah ya yafe mana kuma
muna maraba da masu na gyara.*
*Jin-jina*
“`Jin-jina da duk wata k’ungiyan“`
*“`ONLINE HAUSA WRITERS“`* “`muna k’ara
gode muku da jin-jina muku gurin k’ara
d’aukaka rubutu da jajurcewa gurin kare
marban rubutu da hausa Allah ya k’ara
d’aukaka da basira Ameen.“`
*“`NAGARTA WRITERS ASSO“`*
*“`FIKRA WRITERS ASSO“`*
*“`EXCELLENT WRITERS“`*
*“`ONLINE HAUSA WRITERS “`*
*“`WISDOM HAUSA WRITERS “`*
*“`EXTREME HAUSA WRITERS“`*
*“`WRITERS WORLD ASSO“`*
“`Allah ya k’ara maku d’aukaka da Albarka
Ameen.“`
Page
*1~5*
Matashiyar narinya na hango bak’ace tana
sanye da hijab mai ruwan madara kalo d’aya
zaka masa ka gane ya d’an kwana biyu.
Yarinya bak’ace tana da d’an tsayi ko damuka
kalli fiskanta tana da madai-daicin fuska tana
da dogon hanci tare da k’aramin baki sai
fararen hakwaranta dake haskawa kalo d’aya
zaka mata ka gane nutsuwar da ke tattare da
ita tubarkalla mashaa Allah abunda mukace
kawai. Cikin sauri naga tunifi gidansu
Haneefa da ke Tudun wada hausawa road da
sallamanta ta shiga nan ta tarar da Auta tana
zaune a gefen Hajiya cikin girmamawa ta
gaida Hajiya. Da sakin fuska Hajiya ta amsa ta
zauna a gefe Candy ta ce”Auta wai ni sai
yaushe zaki rage son jiki”. Auta ta murmusa
ta ce“ sai randa zan girma kamar Aunty
Haneefa”. Candy ta murmusa ta ce“ah! Lallefa
da sauran aiki kenan”. Hira suke yi da Hajiya
da Auta da Candy. Amrah da K’urratu~ayni
suka shigo bayan sun gaida Hajiya suka
zauna.
Hajiya ta ce“ya na ganku duk kunyi jigum”.
Kurratu~aini ta ce“hmm rasuwa akayi anan
balayin bayan mu layin ‘yan kosai”. Hajiya ta
ce“innalilahi wa inna ilaihi raji’un waye ya
rasu haka?”. K’urratu~ayni ta ce“Malam Idris
na gidan su Sa’idu”. Hajiya ta ce“ayya Allah
ya jikansa da rahma”. Suka amsa da amin
Candy na jin haka ta mik’e da sauri ta
ce“Hajiya zan tafi sai anjimanku”. Cikin sauri
ta fito ta nufi layin ‘yan kosai da ke bayansu
cikin sauri ta nufi anguwan tun daga nesa ta
hango mutane zaune ga kulolin abinci wanni
sassayan ajiyar zuciya ta saki tana zuwa
rumfa da ake karb’an gaisuwa ta k’ak’alo
hawaye ta farayi ta rusuna ta gaidasu tukun
ta mik’e ta shiga cikin gidan tun daga nesa ta
hango drinks kala-kala a jere ga kulolin abinci
wasu na ci wasu na shan juice yayin da wasu
ke d’aki sai hira suke yi suna shewa tamkar
ba a gidan rasuwa suke ba, a haka ta k’ara ta
saki kuka a dai-dai k’ofar shiga d’akin tana
zuwa ta fara kuka ta na gaida mutane nan
suka amsa bayan ta musu ta’aziyya ta ja
gefen wata mai cin abinci ga namomi akai
tamkar a gidan biki take. Candy sai da ta
hadi’yi miyau don yanda k’amshin ke bugan
hancinta. Pherty ce ta fito ganin yanda Candy
ke kallon mai cin abinci ta ce“bai war Allah
zo ki karb’i sadakan abincin kema”. Cikin
sauri Candy ta mik’e sukaje gaban kulolin
abincin Pherty ta ce“mai kike so a saka
mik?”. Candy sai raba ido take ga taliya, ga
shefe(shinkafa), ga tuwon shinkafa miyar
taushe. Candy ta ce“asa min shinkafanan”.
Nan Pherty ta zuba mata tare da nama zuk’u-
zuk’u Futha da Ummu Abrar suka iso gun
d’auke da wani manyan plate kai ka d’auka
su goma zasuci abincin. Jellop d’in shinkafa
suka saka tare da nama kamar zai yi magana
ga kifi tukun suka d’au juice zasu tashi Candy
ta ce“ku d’an k’aramin naman nan da juice
d’in ba musu suka k’ara mata tukun suka
nufi wani rumfa suka zauna suna ci suna
zuba hira tamkar ba gidan rasuwa ba.
*_TAGWAYEN MARUBUTA_*
Coming soon….
[4:53PM, 9/16/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
_Ummieeluff _
&
_Rash Kardam_
Page~6/10
Bayan ta gama ciye’ciyenta ta zame ta kama
hanyan gida tana mai ciki da farin ciki, dan
ta koshi sosai ta jima bataci abu mai dad’i
irin wannan ba. Tana tafia tana
wake’wakenta harta iso anguwansu dake
tudun wada hausawa road..jikin wani gida ta
tsaya,wanda bangon gidan kadan ya rage ya
fad’i karamin gidane maidaici..sallama tayi
tun daga kofan gidan,sannan ta shiga, d’aki
kwaya d’aya ne ah tsakar gidan sai wani ginin
daya rushe daga gefe..da kuma d’an wani
akurkin kajinsu,sai kuma wani kichen d’in
langa’langa dake jikin akurkin d’akin.
Hango mahaifiyarta tayi nata faman hura
wuta yaki kamawa duk idanunta sunyi jajaye
abun tausayi,duk iskancin khadija tana
mugun son mamarta bata son taga tana shan
wahala..dan ita kad’ai take da ita aduniya. Da
sauri ta isu inda take “sannu mama kawo na
hura miki” ta kar’bi hura wutan,dataga baida
niyyan kamawa ta fita waje tsintan ledodi da
ruba sabida ta samu saukin hura wutan. Tana
shigowa ta had’a wutan ya kamaci kamar
wanda aka xuba masa petrol, ” ummah me
xa’a d’aura”? Nuna mata wani tsohon
tukunyan tower tayi “d’auki ki dumama mana
tuwun jiyane da bakiciba ya rage”..nan take
khadija ta ‘bata rai dan ah duniyanta ta tsani
d’umame ballema tuwun dawa..da miyan
kuka shar daga gishiri saidan magi dabai
wuce kwaya 2 ba. Ah xuciyanta tace “ohh
Allah ya taimakeni danaje gidan “`MAKOKIN
NAN“` naci abu mai dad’i son raina,da yanxu
saidai na kwana da yunwa” .
“Candy” maman ta kira sunan ta,d’agowa tayi
tana kallonta,”toh ki daura abincin mana
kikabar wuta naci bayan kinsa babu itacen”da
sauri ta d’aura tuwun akan wuta tareda xama
daga gefenta. ” waini ina kika shigane tun
safe kina yawo ah anguwannan”? Mamah
gidansu Haneefa naje ..shine su nana suke
fad’a mana anyi rasuwa anan layin yan
kosai,shine mukaje gaidasu”. “a’a kikaje dai
dan bayanda xa’ayi rasuwa ah anguwannan
ace ba’a sameki ah wajenba” wai me kike
samu ah xuwa gidan makoki ne? Candy tayi
shiru kamar ruwa ya cinyeta. “koh bada ke
nake magana ba,ki fad’a min dalilinki na
yawan zuwa gidan makoki da kikeyi? ” eyy
amm muna zuwa gaishe da sune fa’ bayan kin
gaishesu toh zaman me kikeyi? Ta zungoro
baki “muna cin shinkafa..ga kuma drinks
kala2″. Innalillahi wa’inna elaihi’raju’un”
mamah ta fad’a tareda rike baki.” yanzu
abunda kuke zuwa yi kenan ah gidan
makokin? Kai duniya abin tsoro yanxu
rasuwan ma baya bawa mutane tsoro saidai
aje ayita hira anacin abinci kamar gidan biki”
toh khadija Allah ya shiryeki..ki kumayi
hankali da xuwa gidan makoki..dan talauci ba
hauka bane.”toh toh mama basu bane suke
bamu..”oho nidai na fad’amiki kiyi hankali da
biyebiyen gidan makoki.
“`Shin wacece khadija (Candy?)“`
_khadija Abubakar Alkali_ shine cikakken
sunanta..mahaifinta malam Abubakar Allah
yamasa rasuwa tun tana qarama..bata wani
saba dashiba..dama sana’ansa shine facin
tayoyin mota da keke..bayan rasuwansa
Maryama watoh mahaifiyar ta kenan taci gaba
da d’aukan dawainiyar yarta tilo guda d’aya
khadaji wacce akafi sani da candy..candy
nason mamanta sosai sabida ta wahala akanta
ainun..kullum magananta mamana,banida
kowa aduniya sai mamana. Koh Aure batason
amata maganan sa sabida bata son rabuwa da
mamanta. Matsalanta d’aya masifan son xuwa
*Gidan Makoki* da Allah ya d’aura mata,koh
muce ta d’aurawa kanta.duk nisan inda taji
rasuwa toh insha Allahu xakuga candy
acan..burinta kawai abinci da
drinks..kowanne cikin kawayenta taji anyi
rasuwa toh xai sanar da dan uwansa..su d’ebi
juna xuwa gaisuwa kodako basusan suba..su
zarah B B ah gaba..na kalli rasheeda,itama ni
take kallo atare muka had’a baki wurin
fad’in,“`ikon Allah!“`
*TA GWAYEN MARUBUTA*
[4:53PM, 9/16/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
*Na*
*Rash Kardam*
*Ummieluff*
Page
*11~15*
Burinta kawai abinci da drinks..kowanne
cikin kawayenta taji anyi rasuwa toh xai
sanar da d’an uwansa.. Su d’ebi juna zuwa
gaisuwa kodako basusan suba..su zarah B B
da Aneesa da Munay a gaba.. Na kalli
rasheeda,itama ni take kallo atare muka had’a
baki wurin fad’in,“`ikon Allah!“` kuma duk
in ka gansu a gidan rasuwa sun iya yanka
manyan loma tamkar sunyi makarantar koyan
manyan loma.
Khadija tayi makarantar primary da ke Tudun
wada gata da k’ok’ari sosai tun tasowarta
mayyar Candy ce ita ko kud’i ka bata bata
damu ba gwara ka saya mata Candy milk
yafiye mata komai sai shinkafa(shefe) ko aika
taje bata wuce tayin shefe.
Ma haifiyar Candy tana k’ok’arinta gun yin
aikatau na gida da ‘yan kule-kulen kayan
miya don ta tsare mutuncinsu abu d’aya da ya
musu sauki gidan kansu suke bana haya ba
inda rayuwan tazo musu da sauki kenan.
Candy tana da kyau nagaban kwatance don
tun tana k’arama wasu ke zuwa kamun kafa
akan in ta girma suna sonta amma sam
Ummanta taki ta ce“sai in yarinya ta girma ta
amince da kanta tukunna”.
Da wannan kalaman take ja ma masu sonta
burki Umma ta kan d’aura ma Candy tallan
sabulu da omo lokacin tana primary haka
Candy zataje ta ajiye tallan ta kama carafke ko
tambo sai lokacin komawa gida yayi ta fara
zare ido ga kaya ajibge, in ta koma gida
Umma zatayi ta mata nasiha kuma da kud’in
da tayi ciniki dashi suke sayan abunda zasu ci
ga Candy bata iya hakura da carakfe. wataran
kuma ta nimi tsokana azubar da sabulum ta
dawo gida tana kuka.
Randa ‘yan mutuncinta suke kusa tayi talla
tasayar duka tukun ta dawo gida randa batayi
niya ba kuma inta zaga tayi d’an ciniki sai ta
je gidansu Auta ta kwanta ta shari baccinta
tun Hajiya na koranta har ta gaji ta daina in
ta gama baccin sai tasai sabulun naira d’ari
tukun Candy ta nufi gida.
*“`TAGWAYEN MARUBUTA“`*
[7:16PM, 9/16/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
*NA*
_Ummieeluff_
&
_Rash kardam_
Page
16~20
Tun hajiya na koranta harta gaji ta daina,data
gama baccin sai tasai sabulun naira d’ari
tukun candy ta nufi gida. Wata rana duk
cinikin datayi tana kashewa wajen cin candy
da awara,awajen kawayenta masu rashin ji
kamar ita. Tana shiga ta tarda mamanta
xaune tanacin gyad’a mai gishiri,da sauri
tanufi inda take har tana tuntu’be “laah
mamah aina kika siyo gyad’a”? Mamah ta
‘bata rai kamar bada ita takeba. “ni matsalana
dake kwad’ayi khadiya baki isa kiga mutum
nacin abuba,shikenan kin rinka tambayansa
kenan aina yasamu? Toh satowa nayi” nan
take candy ta ‘bata rai kamar ta had’iyi kota.
“toh mamah danna tambayeki inda kika samu
shine xaki rinka min fad’a” nina lura kwanan
nan ma ba sona kikeba,kullum sai kinmin
fad’a, nan take shagwa’ba ya motsa ta rinka
matsan hawaye tana bubbuga kafa.
Mamah tayi murmushi tana kallon candy dake
ta faman shagwa’ba wani kaunarta na sake
shiga zuciyanta..candy akwai rashin ji ammah
kullum addu’anta shine Allah ya shirya mata
yarinya. Janyo hannunta tayi” zonan yar
mamanta,idan banso ki ba inso waye? Ke
kad’ai Allah ya mallakamin danake gani
inajin dad’i,fad’an nan danake miki bawai
kiyayya bace kwad’ayinki yanada yawa,ke
kenan daga kinga abu ahannun mutum saikin
roka. Wannan hali naki Allah dai yasa kada ki
girma dashi..Allah ya yaye miki irin wannan
kwad’ayi”. Sannan ta d’auko gyad’ar kulli
d’aya ta bata nan take ta hau murna tana cin
gyadarta,tana d’an raira waka dad’in gyadar
na ratsata. Shiru mamah tayi tana kallonta
Allah sarki mutuwa mai raba tsakanin
masoya,tasan da mahaifinta nada rai da
khadija tagama jin dad’inta sabida shi mutum
ne mai zafin nema. Gashi babu yan uwansu
akusa balle su taimaka musu,basuda kowa su
biyun nan suke rayuwansu. Cikeda son juna.
Tana gama cin gyad’ar ta mike ta fice abinda
zuwa gidan su Aneesah abokiyar
fad’anta..tana shiga ta’tarda Anush nacin
shinkafa da manja habawa da sauri ta nufi
inda take ko sallamah babu tasaka hannu har
Anush ta tsorata..haka sukayita wawa akan
abincin har candy ta cinye tafara zare idanu
“akwai wani ne”? Haushi yasa Anush wanka
mata mari suka kwashi dambe suna
zage’zage.
*TAGWAYEN MARUBUTA*
[9:00AM, 9/17/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
*Na*
*Rash Kardam*
*Ummieluff*
Page
*21~25*
Haushi ya yasa Anush ta wanka mata mari
mai lafiya Candy ta ce “kutumelesi cabd’i yau
ba zan yarda in kuma na yarda na dan k’are
anan guri”.
Kafin Aneesa tayi wani yunk’uri tuni Candy
ta d’agata sama ta nuna kafin ta makata a
k’asa ta d’ale ruwan cikinta Candy sai jibgar
Aneesa ta ke kamar ta samu jaka. Ihun
Aneesa ne yasaka Mamanta fotowa da sauri
tana fad’in “lafiya Aneesa mai ya same….”.
Kasa karasawa tayi ganin Candy a kan Aneesa
tana jibgarta da sauri Maman Aneesa ta nufo
su Candy na nagin haka ta tashi da gudu tayi
k’ofar gida ta rik’e k’uugu ta ce“Aneesa kalli
nan wuuuu!”. Ta mata gwalo ta ce“ehe naci
shinka fa na more haushi ya kasheki.
Ran Maman Aneesa in yayi dubu ya b’aci ta
kalli Candy ta ce“kanda kike ko wa naga
fitsaranki ya soma yawa fa”. Candy ta
kyalkyale da dariya ta marairaice murya ta
koyi yanda Maman Aneesa tayi magana ta
ce“lah kuji bata iya fad’a ba wai Kanda
hahaha!!!”. Ta kece da dariya ran Maman
Anee ya k’ara kufula ta juya zata duba bulala
Candy ta lallab’o tazo ta zuba ma Aneesa dun-
du tare da mari ta yanka aguje tayi k’ofar
gida ta mata gwalo ta ce“na daki banza aha
gobe ina zo cin shinkafa mutum ya hanani ya
gani in masa wanda yafi na yau”. Ta sake
gwalo ta fita da gudu Maman Aneesa bak’in
ciki y isheta tamkar ta kurma ihu ta
ce“Aneesa d’auko gyaleki yau gidansu Kanda
zamuje Aneesa ta ce“to Mama amma sunan
ba Kanda ake cewa ba Candy ne kinga har
tana kwaikwayan maganarki”.
Wani tsawa Maman ta daka mata ta ce“rufe
min baki sai yanzu kika iya maganan nan ina
ta dakaki in banda ihu ba abun da kike mana
kin kasa ramawa mtsss!!”.
Fuuuuu Maman ta fita Aneesa ta rufa mata
baya zasu kai k’aran Candy.
Candy tana fita bata zarce ko ina ba sai gun
carafke da nan suka fara carafke yayi dad’i
Candy ta nason cin gyad’a ta mik’e ta ce“tun
d’azu sai cinyeki nake tunda ‘yar bashi muke
yi dan haka a gyad’anki zan fanshe bashi na”.
Kafin ya rinya ta mik’e Candy ta d’ibi gyad’a
tasaka gudu tamkar k’afanta zai tab’a keyarta.
Sai da tayi nis sosai ta zauna akan wani
hakali ta fara cin gyad’anta tana ‘yar wak’a ta
sai da ta cinye ta ce“yanzu ina zn a nufa?
Gashi yau ba wani Gidan da ake “`ZAMAN
MAKOKI“` bare naje”. Wata zuciya ta ce“ki
koma gida kiga halin da Ummaki ke ciki sai ki
d’an taya ta aiki ma”. Murmushi tayi ta
ce“Allah sarki Umma na kina sona nima ina
k’aunarki Allah ya bani kud’i in gina miki
k’aton gida kaman Garin Bauchi.
*“`TAGWAUEN MARUBUTA“`*
[6:01AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
“`NA“`
“`Ummieeluff“`
&
“`Rash kardam“`
Page
26~30
Murmushi tayi tace “Allah sarki ummana kina
sona nima ina k’aunarki Allah yabani kud’i
in gina miki k’aton gida kaman garin bauchi.
Bata wani bata lokaci ba ta kama hanyan gida
ahanyanta na tafia ne ta gamu simbiat
“yauwa yau wana kama?” simbie ta kama
zazzare idanu dan tasan halin mugunta irinna
candy. ” ina tambayanki wana kama? Jiya ina
rokanki alewan madara kika hanani kika
gudu,toh yanzu kinga babu kowa dagani saike
in lakad’i banza in more” simbie ta soma
komawa da baya tana neman hanyan gudu.
Candy na binta “aiyau sai kinci na jaki
watarana idan na rokeki abu ki hanani” nan
ta cabko wuyan riganta,tun kamin ta fara
dukanta simbie ta suma kuka. “kai meya
had’aku” sukaji anfad’a daga bayansu.
Ammah candy koh ah jikinta taki sakin
wuyan riganta. Mutumin ya tsinko bulala
yana zuwa,dataga yayi kusa sai ta saki wuyan
simbie tareda faska mata wani zaz’zafan mari
dayasa simbie sakin ihu ta tsuguna. Taruga ah
goge gobema kimin rowa ki gani.
Tana shiga layin gidansu ta hango Anush ta
mamanta sun nufo hanyan gidansu,da sauri ta
buya jikin wani bishiya dan kada su ganta
“kambu ammah idan Aneesa tasa ran mamah
ya baci saina mata d’an karen duka” suna
wucewa tabi bayansu,basu gantaba ahankali
take binsu har suka kawo kofan gidan. Ko
sallama babu suka shiga cikin gidan.Allah
sarki baiwar Allah tanata tsince’tsincen kara
da zata had’a wuta.kawai taga mutane ah
kanta kerere. ” ah ah maman Aneesa ce
sannu da zuwa ga wurin zama” tafad’a tana
kokarin shin fid’a musu tabarma. “Kinga ba
zama ya kawoni gidanki ba, nazone kijama
yarki kunne kada ta sake dukan min d’iya”
shiru tayi tana sauraron abinda take fad’a.
Yama za’ayi yarinya da gidan ubanta ahanata
sakewa, kinsan Aneesa bata iya fad’a ba tana
zamanta tanacin abinci wannan kande d’in ta
shigo ta cinye mata abinci hakan bai isheta
ba ta kara mata da duka” ina mata magana
zatamin rashin kunya ta gudu,ai talauci ba
hauka bane”.idan ran mama yayi dubu to
yabaci. “Yanzu khadijan ce taje tayi miki
rashin kunya har gida”? to dan Allah kiyi
hakuri idan tazo zanmata fad’a” matsowa tayi
wajen Aneesa “kiyi hakuri kinji mamana
insha Allah bazata sake dukankiba”.
“Inama zata sake ganinta, ki sakawa yarki ah
kwa’kwalwarta idan nasake ganin kafanta ko
wucewa tayi ta kofana to sainasa an karya
mata kafa” janyo Aneesa tayi kamar zata cire
mata hannu suka fice daga gidan. Candy dake
labe tayi saurin buya dan karsu ganta. Suna
wucewa ta fad’o cikin gidan da sauri. Yanda
taga fuskan mamah tasan ranta yayi mugun
baci. Da sauri ta isa wajenta “mam”…kamin ta
karasa mama ta wanka mata mari. Cikeda
tsoro candy ke kallonta dan mama bata
dukanta, ta manta yaushe rabonda aka zegeta
balle harya kaiga mari.
“khadija meyasa kike son sa kanki ah bakin
mutanene?,bakisan harshe guba bane,kullum
saikin nema min abun magana a
anguwannan. Haba khadija saikin kasheni, da
bakin ciki tukunna zakiji dad’i” da sauri ta
dago kanta dan batason ana am’bata mata
mutuwa musam’manma mamanta. haka
mamata rinka mata fad’a shiru tayi ranta
abace..ta kudurta aranta idonta idon Aneesa
saita koya mata hankali tunda tasa mamanta
bacin rai.
*TAGWAYEN MARUBUTA*
[6:01AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
*Na*
*Rash Kardam*
*Ummieluff*
Page
*31~35*
Candy ganin ran Umma ya b’aci sosai gashi
bata son abunda zai b’ata mata rai rusunawa
tayi ta ce“Ummana dan Allah kiyi hak’uri
bazan sake ba Ummana karkiyi fishi dani
kinga bani da kowa sai Allah sai ke kinji
Ummana”.
Umma duk jikinta yayi sanyi Candy ta gama
kashe mata jiki a hankali ta furta “zo nan
Khadija kece ai amma in kikabar neman
tsokana to zamu zauna lafiya da ke”.
Candy ta ce“Umma zan bari in dai zakiyi
farin ciki”.
Umma ta ce“sosai ma zan so ganin hakan
Allah ya miki Albarka”. Candy ta amsa da
”amin”.
Bayan kwana biyu ana zaman lafiya da Candy
talle in ta d’auka ma Umma take ta kan zaga
da ikon Allah ya k’are ta dawo gida ko
gidansu Autar Hajiya bata zuwa yanzu bata
shiga harkan kowa.
BAYAN KWANA BIYU…
Candy kamar abun kirki har Umma tana
murna d’iyarta ta nutsu komai cikin girma
take yi da nutsuwa.
Yau ta dawo daga talla ta hango Aneesa cikin
sauri ta zaga ta bayanta ta ajiye tallan tukun
ta shak’o ta, sai da talasa Aneesa tukun ta
mak’ureta ta ce“in kika fad’a a gida ko wa
Maman ki sai na fasa wannan bakin”. Sake ta
tayi ta d’au tallanta tayi gaba. Tun daga nesa
ta hango motan gawa an wuce da shi zuwa
makabarta a gur-guje ta sayar da sabulun ta
ce“Umma barin je gidan su Munay bata jin
dad’i zan gai data”.
Umma tace“to karki dad’e kice ina gai data
Allah ya sauwaka”. Candy ta amsa da “Amin”.
Tana fita tayi gidan su Munay da Sallama ta
shiga ta gaida Maman Munay ta ce“Inna
Munay na nan kuwa?”.
Maman Munay ta ce“ki duba d’akinta
tananan ta na baccin rashin zuciya”. Da sauri
Candy ta shiga tana zuwa ta d’ana wa Munay
duka ta ce“ke tashi yau mun samu gun zuwa
zamuje cin shefe(shinkafa)”. Da sauri Munay
ta tashi ta ce“da gaske ki keyi ne?”. Candy ta
ce“eh wallahi dazu naga an wuce da motar
gawa amma ban san wani gida bane kawai sai
mu gan-gara kasan layi in munga gidan sai
mu shiga”.
 *“`TAGWAYEN MARUBUTA“`*
[6:01AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
*NA*
*_Ummieluff _*
&
*_Rash Kardam _*
Page
*36~40*
Candy tace “eh wallahi d’azu naga an wuce da
motar gawa,amma bansan wani gida bane
kawai sai mu gan-gara kasan layi in munga
gidan sai mu shiga”.
Munay tace “toh yanzu ta wani layi zamu fara
neman gidan”? Gashi wlhy dama yunwa
nakeji,kinga umma kubewa ta dafa koh
alfarman wake babu,kwanciyan nan da kikaga
inayi na bakin ciki ne” candy ta fashe da
daria “kaji yar iska yanzu dabance miki anyi
rasuwa ba, da ashe mutuwa zakiyi da
yunwa,dan nikam na daure naci kwad’on
garin kwaki”. “Toh yanzu dai tashi muje”.
Munay ta janyo hannunta “ke tsaya kefa
bakida wayo,yanzu idan umma ta tambayeki
me zamuce”? Candy tayi shiru ta d’aga kai
kamar me tunani.”ammah fa kawata kin kawo
shawara,toh yanzu me zamu ce da ita”?
“Yauwa zo muje nasan mezan ce da’ita”. Suka
fito atare munay na kokarin saka hijabinta.
“Ummah bari muje mu gaida Asea B Aliu
kawarmu mamanta bataji dad’iba jiya aka
sallamota daga asibiti”. “Eyyah toh idan kunje
ku gaidata da jiki,Allah yakara mata sauki”
atare suka had’a baki wajen fad’in”Ammen”
sannan suka fice da gudu. “kai ammah kin
taimakemu da yau umma bazata bari inje ko
inaba” yanzu ta ina zamu fara kenan gashi
bamusan gidan ba” kumafa, muje mud’an
zagaya mugani”. Haka suka rinka yawo cikin
anguwan shiga nan,fita can har suka gaji
basuga inda ake zaman makokin ba. Zama
sukayi kofan wani gida ishin ruwa ya
ishesu..sun rasa ina zasu shiga su samu
ruwan sha.
Can saiga mai saida pure water.da sauri
candy tace “me ruwa” da karfi cikin sauri ya
iso wurin. Cikin kakkarfan murya candy tace
“bamu na naira goma”,ta d’auki d’aya tana
kallon Munay”ke kina kallona bazaki sha
bane” munay ta kalleta dan tasan cikinsu
babu mai sisi, ammah yaya ta iya ta d’auki
guda d’aya tasha itama. Yauwa jiramu anan
bari mu karbi canji a wancan shagon, ta nuna
masa wani bangare,kamin yaron ya juyo taja
hannun munay suka kwasa aguje yaron na
binsu, suna gudu har suka bace mishi da
gani,yaja musu Allah ya isa.
Da kyar suka ‘buya wajen wani gida suna
nishi..Munay tace “ammah ke yar iska
cefa,kisa musha ruwa ammah bamuda ko
sisi”Ke dalla ja dagacan idan kikace zakisha
abu sai kinada kud’i toh ashe zaki mutu wata
rana”. MunaY zatayi magana sukaji kukan
wata mata daga gefensu ta wuce tana
kuru’ruwa. Munay ta kalli candy suka had’a
baki wajen fad’in laaa ga gidan da ake zaman
makokin can. Suka kwasa aguje zuwa gidan,
suna isowa kofan gidan sukaga gidane nagani
nafad’a,anata shigar da drinks katin-
katin..Candy ta rike baki jiki na rawa taja
hannun Munay zuwa kofan gidan.
*TAGWAYEN MARUBUTA*
[6:01AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
*Na*
*Rash Kardam*
*Ummieluff*
Page
*41to50*
Candy jikinta na rawa ta ja hannu Munay
suka nufi k’ofar gidan rasuwan suna zuwa
suka gaida mazan da ke *“`ZAMAN
MAKOKI“`* a k’ofar gidan. Kayan drinks ake
shiga da shi ga manyan jeep suke tsayawa
suna ta’aziya suna shiga zauren suka
mammatsa idonsu suka fara hawaye kafin
suka shiga da kuka.
Ga wasu suna zaune sai brush suke da naman
saniya manyan tsoka ga wata rantsatsen
abinci kai ka d’auka gidan biki ne.
Wata Hajiya ce ta shigo ta sha less ta sha gayu
kai ka d’auka zab’en kyawawa zata sai wani
takun k’asaita take in ka ganta bazaka dauka
a gidan mutuwa ta ke ba.
Ga wanni lafiyayyen kamshin da ke tashi
tamkar tayi b’arin turare. A hankali ta taka
zuwa d’akin da ake karb’an tana gai dasu
tukun ta dan zauna. Candy da ta sake baki sai
kallon matar take yi don ta gama burgeta,
Munay ce ta zun gure “ke zo muje muyi
abunda ya kawo mu tukun”. Gurin da suka ga
ana d’iban abinci nan suka nufa ba kunya su
Candy suka saka hannu suka d’au plate suka
zuba abinci naman kai d’in kuwa kamar da
gayya suka saka tsaban had’ama goran Fanta
bibbiyu suka dauka. Gefe suka koma suka
fara jan abinci wata Mata ne ta shigo ita ma
cikin shiga ta alfarma sai da ta shigo ta hangi
wannan Hajiyar nan fa suka fara aika ma
junansu da kallon-kallo. Kowacce a tuanninta
ta gama kure adaka amma kashh!! Sai gashi
sun ga juna kuma duka cikin shigan ba rai ni
dalilin da yasaka suka fara kalon-kalo ma
junansu.
Munay ta kalli Candy ta ce”kiga wa’yannan
matan kallon da suke majuna kamar ba gidan
rasuwa ba kuma inaga hakan baya rasa
nasaba da sun dauwanka mai kyau shiyasa
suke kallon-kallo ma junansu”.
“Mtss abun da bai dameka ba dad’in ji gareka
ina ruwan mu. Kowa yayi abunda ya ficce sa
mu ba gashi cin shefe(shinkafa) shi ya kawo
mu, kawai muyi mu tafi”.
Mai sayar da pure wata ya bi su Candy bai
gansu ba nan ya tafi yana kuka don ya san sai
an dakesa a gida amma duk randa yaga Candy
sai ya tara mata jama’a ta bashi kud’insa.
Sai da suka kai gejin k’oshi kafin suka
sud’ad’e suka bar gidan .
Candy na dawowa gida ta canza fiska da
sallama ta shiga sai da ta gai da Umma kafin
ta ce”kai Umma gsky Munay tana jin jiki
amma da sauki har an mata allura ma”.
Umma ta ce”ayya Allah ya bata lfy gobe zanje
na dubata in Allah ya kai mu”.
Idon Candy yayi tsuru-tsuru jin gobe Umma
zataje duba Munay take wata dabara ta fad’o
mata cikin sauri ta ce”la! Umma ai basai
kinje ba ma naji kamar Mamanta ta ce gobe
da safe zasu je Gashuwa”.
Umma ta ce”ayya! Allah ya sauwake ya kai su
lafiya”.
Bayan kwana biyo komai na tafiya wa Candy
lafiya suna zaune a k’ofar gidan su Autan
Hajiya nan suka ga wasu Christian sun wuce
da motar gawa acikin akwati da alama daga
asibiti suka d’auko za’aje bikin birne shi. Da
sauri da lakato Munay ta ce”kaa kalli mu
hanzarta mubi bayansu don kar su mana nisa
da alama ba daga unguwan nan suke ba”.
Munay ta mike da sauri ta ce”aikam don
yunwa nake ji sosai”.
Candy ta jata suka fara sauri suna bin motar
kasancewar bata gudu sosi motar a slow take
tafiya.
Candy ta kalli Munay ta ce”nifa kinsan duk
randa banci shinkafan gidan Mutuwa ba bana
jin dad’i ji nake kamar ba abinci naci ba
shiyasa nake ala-ala ayi mutuwa.
Ganin motar ta fara gudu yasa suma suka
saka gudu.
Motar gawan ta nufi Abuja Road Magajin
garin dai-dai Wushishi road ta tsaya, nan
suka ga ta faka a k’ofar wani gida aka fito da
gwan aka shiga gida basu dad’e ba sai ga
motoci aka tafi gun da za’ayi biki.
Mutane sun fito sai ihu suke yi suna kira
jejous name Candy ta ce”kai nifa yau naka sa
kuka fa”. Munay ta ce”ni ma idona kyamas
yau”.
Candy kamar wacce ta tuna wani abu ta waro
hannu zaninta sai ga *ROB* ta ce” mud’an
shafa wannan abakin idon mu zai yi hawaye
na Umma nane da ta aiken”. Nan fa suka goga
kan kace me sai ga hawaye suka fara ihu
suna aka shiga mota gun da suka je an sake
speakers sai tashi da kida yake yi ga kayan
abinci ga su minti da Coc ga Fanta da Mirinda
nan jikinsu ya d’aurawa sai bari yake yi sun
ga abun nema. Suma ayarin suka bi suka fara
rawa aka gama suka ci abinci sannan suka
d’ebo goran Fanta kowa bibbiyi a hannusu
suka nufo gida.
Umma da ke jiran *ROB* harta cire rai can
sai ga Candy ido yayi jajazur alamar taci kuka.
Da sauri Umma ta taso ta ce”lafiya Candy”.
Candy ta mutsuka ido ta ce”naje shagon
Kabiru mai provision *ROB* dinsa ya kare
ganin kinaso shiyasa nace barin je kasuwan
bacci na sayo miki, to a hanya ta tadawowa
wani mai mashin ya bugeni ganin banji ciwo
yabani hakuri ya sai min Fant”.
Ajiyan zuciya Umma ta sauke tace”ai barka
tunda bakiji ciqo ba kuma da bai wahalar da
kansa ba yasai abu”.
Candy ta ce”ai shi yayi niyya ya ban”.
Umma ta ce “to angode Allah ya kare na
gaba”.
BAYAN SHEKARA BIYU….
Yau su Candy ke bikin kammala makarantar
primary sun yi shiga ta alfarma Candy ta
samu kyaututu ka kasancewarta hazika mai
kokari acikin dalubai gifts ta samesu da haka
suka gama ta dawo gida Umma sai da tayi
hawayen murna.
Bayan kwana biyiu sakamako ya fito Candy
taci kamarantar gwamnati na jeka ka dawo da
ke Kabala Costain ranar murna a gunta ba’a
magana wai ita ce zata bababn makaranta ta
gama primary da hakan ta nufo gida cike da
murna.
*“`TAGWAYEN MARUBUTA“`*
[6:01AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
Page 51~60
Tun daga k’ofan gida take ihun kiran sunan
Umma!! ta shigo aguje sukaci karo da Umma
tana nufo inda take.” kai Khadija harkin
tsorata ni wlhy,wane irin kirane wannan sai
kace makauniya, ke kullum ba kya sanin kin
girma kenan” dariya Candy ta fashe dashi “kai
haba Umma daga kiran sunanki saiki tsorata
haka,toh yau kiran naki ba fad’a na janyo aka
biyo niba”. Hmm” Umma tayi ajiyan
zuciya,”toh Allah dai yasa hakan ne”. Tsalle
tayi ta d’ane cinyanta yau u
Ummah na gama primary d’ina kuma naci
makaranta ta jeka ka dawo dake kabala
costain,kinga kenan mafarkina zai zamo
gaskia,dama kullum burina kenan,Banason
naje makarantan kwana sabida bazan iya
rabuwa dakeba Ummana”.
“Uhumm Khadija yaranta ke damunki,kina
yawan mantawa da akwai aure da mutu….”
Da sauri ta rufe mata baki “ballema bazaki
mutuba muna tare har karshen rayuwanmu”.
Tana kai wa nan ta nufi d’aki aguje dan cire
uniform d’inta.
BAYAN SHEKARA UKKU!!
Su Candy an zamo manyan mata komai na
budurci yasoma bayyana ajikinta. Cikin sauri
tafito sanye da uniform d’inta tayi kyau sosai
abinta.”umma nizan wuce dan na kusa yin
latti,”toh yar umma da fatan kin cinye
d’umamen dana baki, Candy tad’an bata fuska
“eyy na cinye umma”,Sannan tafara tafiya
umma tace “zo Khadija gad’an guntun naira
ashirin ko zaki sai wani abu amakaranta”. Ta
karba tareda godiya “toh Allah kiyaye hanya”
Tace “amin”. sannan ta kama hanyan tafiya
abinta. Taku take cikeda nutsuwa ahankali
kamar bata son taka kasa. Rasheeda ta
kalleni, ” Ummielurv ammah kina kallon
abunda nake kallo kuwa”? Juyawa nayi na
kalleta “wlhy kuwa kinga yanda Candy take
tafiya a nitse kamar da gaske”. “Nidai ban
yarda Candy zata iya canza halinta ba” inji
Rash. Da haka dai harta shiga makaranta ta
nufi ajinsu wato JS3A tana zuwa aka fara
mata ihu. Tana d’aga musu hannu harta zo
wajen zamanta. Ta kalli Rabi’at SK “ke
matsamin awajen zamana, ai kinsan nice da
lungu amma kullum saiki zauna min awaje”.
Yanda kuka san bada mutum take magana ba
haka Rabee’at ta manna mata.haushi yasa ta
kai mata mari tasss!!, kake ji karan marin, sai
da wutan idanun Rabee suka d’auke na
wucin gadi. Nan take kokawa ta kaure, babu
wanda yayi kokarin rabasu dan kowa na
tsoron kada fad’an yadawo kansa. D’ane
ruwan cikin Rabee’at tayi ta rinka kai mata
naushi aciki kamar tasamu jaka. Tun tana
kokarin kare kanta harta kasa karfinta yakare.
Cikin sauri malamin ya shigo ajin ya daka
musu tsaya. Kowa yasamu nutsuwa nan take
Candy ta nutsu dan babu wanda take tsoro
aduniya irin Malam Muh’d tsawa yadaka mata
“u again Khadija, come here ma frnd”. Da
sauri ta matso kusa dashi jikinta na rawa
kamar mazari dan tasan yau ubanta zata ci.
Yasa aka d’aga Rabee tare da zaunar da ita
akan kujeranta. Tana mai da nunfashi. Malam
Muh’d yasa Candy up n down tun tanayi tana
dariya harta fara kuka da majina. Malam
Muh’d najin kukan har tsakar kanshi ammah
babu yanda zaiyi, yana son ya hukunta’ta
tukun tayi hankali. Tun tana kukan ahankali
harta wage baki,ta soma ihu. Tsawa yadaka
mata “will u keep quit?”. Kai ranan Candy taci
kuka ta gode Allah. Sanda yagama darasin sa
na lissafi sannan yace taje ta zauna. Da kyar
take tafiya zuwa wajen zamanta. Tsayawa yayi
yana kallonta cikeda tausayawa. azuciyansa
yasan hukuncin da yayi mata yayi tsauri da
yawa. Ba yanda ya iya ne Candy bata ji sosai.
Da aka tashi kawayenta irinsu Mamu da
Kausar suka fara bata hakuri. Kausar tace
“kai ammah Malamin nan dan rai nin
wayone,in ba dan iska ba me yasa zai baki
irin wannan punishment d’in”. Mamu tace
“rashin imani mana”.wlhy idan ba kici uban
Rabee ba baki burgeniba, Shigiyar yarinya
anan da kike kukan fa dariya take miki”.
Kausar tayi karaf tace “wlhy malam Muh’d sai
mun”…” Candy ta daka mata tsawa “dan Allah
ya isa tun d’azu Malam Muh’d ina ruwanku,
ni daya wahalar banji haushi ba balle ku,
Kowa taji buzzir dake
d’uwawunta,munafukan banza, ina kuma
dad’i kukaji dayake punishing d’ina”
“mustew!!”. ta karya kwana zuwa bin layin
gidansu tana di gisa kafa.
*TAGWAYEN MARUBUTA*
[6:01AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
*NA*
*Rash kardam*
*Ummieluff*
Page
*61to70*
Jan k’afarta take yi har ta iso k’ofan gida. Sai
da ta tsaya k’ofar tana tunani shiga don yanda
take jan k’afar. Ta kai minti goma a gun kafin
ta shiga cikin gidan da sallamanta.
Umma da ke fama da itace a murhu sai
hayaki yake yi idonta duk ya kaɗa yayi ja-
jazur. Ta joyo tana fifita wuta ta amsa
sallaman Candy ganin k’afarta na ɗin gishi, da
sauri Umma ta yarda abun fifita, ta nufo
gunta ta na ce wa”lafiya Candy mai ya faru
dake naga k’afarki na ɗingishi?”.
Idon Candy ya ciko da kwalla Umma ta ce”ki
faɗa min mana Candy duk hankalina ya
tashi”.
Hawayen da Candy ke mak’alewa ya zubo,
cikin muryan kuka ta ce”Umma ba Malam
Muh’d bane don yaga muna faɗa da Rabeer’at
ya dake ni, kuma ita ce da niman tsokana”.
Umma ta ce”kai amma Allah yayi ma Muh’d
ɗinnan albarka da ko zan ganshi da na gode
masa”.
Candy ta zunɓuro baki ta nufi ɗaki.
Umma ruwan zafi ta juye ma Candy ta kai
mata bayi. Ta je ɗakin ta ce”ki je ki watsa
ruwan zafi zaki ji daɗin jikinki”.
Candy ta mike da kyar ta nufi bayi ruwan da
zafi haka ta ringa watsawa tana faɗin
“washh!!. Sai ta yarfe hannuta sabida zafi.
Tana gama wankan ta ɗauro zani ta fito sai
taji daɗin jikinta, man zafin da ummah ta
ajiye matane,ta shafe dukkan jikinta
dashi,sannan ta ɗan samu sa’ida, tayi sallah
taci abinci ta sha maganin ciwon jiki,ta
kwanta barci mai nauyi ne ya ɗauketa.
Candy bata farka ba sai bayan sallah la’asar,
ta tashi tayi sallah ta ɗanji daɗin jikinta. Yau
zama tayi ko k’ofa bata fita ba dan k’afarta
yana ɗan taɓata har yanzu.
Zama tayi ta zabga ta gumi tana tunanin
kalan dukan da zatayi ma Rabee’at in ta
kamata.
Washe gari bata je makaranta ba sabida yanda
k’afarta ke taɓata amma da sauki.
Malam Muh’d yana zaune a gindin bishiyar
da yasa ba zama yana kallon wucewarta. Duk
ya damu yanda yaga ‘yan latti nata wucewa
babu alamanta wani karin abun haushi kusan
k’arfe tara ba labarinta. Duk sai yaji zaman
Makaranta ya ishesa. A can k’asar zuciyansa
kuma cewa ya ke”gaskiya nima ban kyauta ba
hukuncin dana bama Candy yayi tsauri inaga
hala k’afarta ne ya da meta”.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaɗaga kai
ya ga har an rufe gate ɗin makaranta. Jiki ba
kwari ya mike ya nufi office, yana mai jin
haushin kansa sosai akan hukuncin da ya
mata.
A cikin aji Mamu da Kausar Lurv suna zaune
jigum Mamu ta ce”Kausar ki ga har 9:00 yayi
Candy bata zo ba ko lafiya”.
“Hmm”. Mamu ta sauke ajiyar zuciya ta
ce”nima Kausar tun ɗazu nake tunani anya ba
k’afarta bane ya dame ta?”. Kausar ta ce”in
kuma ta wahala Mamu sai mun daka Rabee’at
don ita ce silla, sabida kinga asali gurin
zaman Candy ne ta zauna, shi kuma wannan
mugun Malami ya dake ta”.
Mamu ta ce”nifa yanzu haushi yake ban ya
wani saka mana ido baran Candy ma kusan
kulum sai ya bata punishment”.
Kausar ta ce”ke dai bari kawai in an tashi
zamu bi gidansu mu gani”.
Malam Muh’d ya tsinci kansa cikin nadaman
abunda ya mata da wannan tunanin har aka
tashi daga makaranta. Jiki ba kwari ya nufi
gida abunsa.
Mamu da Kausar suka bi gidan su Candy nan
suka samu k’afar yayi sauki, ta kuma shaida
musu gobe tana zuwa makaranta.
Sallama suka mata suka tafi gida.
Washe gari Candy ta tafi makaranta cikin
shirin kota kwana don sai ta rama abunda aka
mata akan Rabeen Gwaggo….lol..
Malam Muh’d ganin Candy yau yaji sanyi a
ransa. Bakar gilashinsa ya mannata wanda ke
kara masa kyau, hakan kuma yake basa
daman kare ma Candy kallo. Yarinyan tana
burgesa gata da k’ok’ari sai dai bataji abunda
ke haɗa su da ita kenan kuma baya sake
mata.
Aji suka shiga akayi ka nan suka zauna ana
musu karatu sam Candy bata nuna ma
Rabee’atu Gwaggo komai ba. Hakan yasa su
Rabee da kwayenta sai dariya da zunɗe suke
ma Candy.
Ana tashi Candy ta ja su Mamu suka laɓe a
wani gida suna kallon su Rabee sun ɗau
hanyan gida suna dariyan mugunta akan
dukan da akayi ma Candy suna dariya suna
faɗa. Sai da suka shiga lungu Candy ta fito da
sauri su Mamu ma suka biyo bayanta tana
zuwa ta sha gabansu take ido ya raina fata.
Rabee tana shirin artawa da gudu Candy ta
cafko ta ta haɗa ta da bango nan ta fara
jibgarta kamar ta samu jaka. Sai da ta
lallasata su Mamu kuma sukaji da yan koren
Rabee. Su Rabee sai hawaye, Candy ta
ce”saura naji kun sanar da wani ko ya je
kunnen Malam Muh’d hahaha!!”. Tasaki
dariyan mugunta kai ta gir-giza musu alamar
kun san sauran.
_*“`TAGWAYEN MARUBUTA“`*_
[6:01AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
“`Umieelurv
&
Rash kardam“`
Page 91-100.
Duk masifa da tsiwan da ta ɗago domin ta
masa tana ɗaga kanta sukayi ido huɗu nan
take ta nemi masifan ta rasa. Rass!!! Taji
kirjinta ya buga arba da tayi da kyakkyawn
saurayi, ajin farko wan da duk wata mace ke
fatan samunsa. Wani sanyi ya sauka
azuciyanta. OMG tafaɗa azuciyanta nan take
ta sakar masa ta wani tattausan murmushi
daya daɗa fito da kyawunta azahiri. Kafa mata
kyakkyawan fararen idanunsa yayi sai
murmushi fararen hakoransa suka baiyana.
Candy wani daɗi ya mamaye mata zuciya dan
bata taɓa tsammanin babban yaro kaman
wan’nan zai kulataba,ga kyau ga kuɗi aina
gama caɓawa arayuwa in siyama na sabon
gida mai kyau nasan Ummana zataji daɗi.
*** ****
“ah’aaam” yayi gyaran murya wanda sai
yanzu Canday ta dawo daga duniyan tunani
data shiga. “Tunanin me kikene Beauty?.”
Wani daɗi taji da taji ya ambaci kalman
beauty taji kamar ta saka ihu. Ina bakin
Candy yaki rufuwa sai murmushi take, da
kyar ta tattaro nutsuwanta “ah! ah!! Babu
komai sauri nake shiyasa Ummana tana
jirana.” “Alright dear nima banso tsayar dake
akan titi hakaba, sabida ba mutunci,ammah
ganinki yasa nakasa juran tafiya ba tare dana
miki magana ba” shiru Candyƴ tayi tana
sauraron daɗin muryansa. “Toh yanzu dai ba
wannan ba gidanku zaki nuna min sai anjima
na dawo muyi magana na fahimta ko?”. Cikin
sauri Candy tace “eee’ee hakane” cikin sauri
ta kwatanta mishi gidansu ko irin jan class
ɗinnan babu taga mai kuɗi. “To sai anjima
beauty inasha Allahu zanzo anjima
inganki,ammah in bazaki damu ba muje
mana in ajiyeki.” Candy ta ɗanyi jim kaɗan
sannan ta ɗago kai tana kallonsa “please
beauty don’t say no” ya faɗa cikin karamin
murya. ahankali yafito daga motan yanzune
taga zahirin kyawunsa tafiya yake cike da
kasaita harya iso ɗaya bangaren tareda buɗe
mata kofa ” bismilla muje”. Cikin sauri taje ta
shiga motan wani kamshi ya bugi hancinta
nan take ta lumshe idanunta… Sanyi takeji
yana shiga jikinta gashi ta rasa ta inane
wannan sanyi ke ratsata haka dube-dube
tasama dan ganin inda sanyin ke fitowa. Tana
kak’kare jikinta da hijabin dake jikinta,Tama
manta tana tareda wani. ahankali ya furta
“o’oo am so sorry beb bari na rage Sanyin AC
da alama yana damunki” {haha su candy ba’a
taɓa shiga mota me Ac ba lol!} Dai-dai kofan
gidansu ya ajiyeta sukayi sallama ta fita daga
motan tana tafiya ahankali su Candyƴ harda
canza salon tafiya kallonta yake tareda dukan
siterin motan da karfi yace “shez so beautiful,
i think i’ve found my missin wyf” ahankali
yake drivin harya bar layin.
“Assalamu Alaikum” Ta shiga gida da
sallamanta Umma tagani tana soya kaji masu
yawan gaske. Ihu ta shiga gidan dashi “eeee
Ummana waya bamu kyautan kaji”? “Ah! Ah!!
Khadija aikatau aka bani gobe akwai biki da
za’ayi abayan layinmu, yaya kin dawo daga
makarantan yaya karatu”?. “Lafiya kalau
Ummu, amma yanzu dai yunwa nakeji wlhy
ina abincina”? Da hannu Umma ta mata nuni
da inda abincin yake. Candy na cin abincin
tana kallon kaji da Umma keta faman soyawa.
Can taga bazata iya jurewa ba tace “Umma
kazan bazamu ɗan-ɗana bane”? “Kinga bana
son sakarci kajin mutane ne zamu ɗan-ɗana
toni badani ba wannan sakarcin”. Candy taji
kamar ta fashe da kuka dan bakin ciki har
idanunta suntara hawaye,(kunsan idan
mutum ya kwaɗaito da son abu ba’a bashiba
yanda yakeji)Tana nan zaune kamar mage.
Ummah najin an’kiran sallan la’asar ta mike
dan zagayawa bayi. Candy na ganin haka ta
isa bakin murhun taɗau cinya babba guda
ɗaya. “keee Khadija me kikeyi abakin
murhun”? Da sauri ta juyo “babu fa Umma
kawai nazo gyara miki icen ne.” “Muga
hannunki!” Candy taki ta fara kowama baya
ahankali “nace muga hannunki ko bakya
jine”? Da sauri candyƴ ta arce ta gefenta
aguje.” Zaki dawo ki sameni”.
*** *** ***
Misalin “`7:30pm“` wani ɗan almajiri yashigo
gidan “Assalamu Aleikum wai ana sallama da
bauti” Umma dake alwalan sallah isha’i tace ”
ayyah yaro ba gidan bane babu bauti agidan
nan” mikewa yayi zai fita Candy tayi carap
tace “aihoo Ummah nasan gidan su nan suke
kwanan’nan suka kauro anguwan nan” bata
jira ansan Umma ba taja hannun almajirin
suka fice “zo in’nuna maka gidan” suna fita
tana hango motan bata bita kan almajirin ba
tayi wajen da sauri. Da sallamanta ta’isa
wajen kamar abun kirki,ya ansa fuskansa
ɗauke da murmushi. azuciyanta tace “wai
wannan baya gajiya da murmushi ne? “Barka
da zuwa Sarauniyar kyawa’wa” Tayi ɗan
murmushi “barka dai ina wuni” Ta gaidasa,
“Shigo mana daga ciki” har tayi kamar zata
shiga sai ta tuna da sanyin da ke shiga jikinta
ɗazo sanda taji ɗan mura-mura. “a’a nan ma
yayi wlhy” fitowa yayi daga motan cikin wani
lal’lausan farin shadda wanda yaji zubi kamar
bada kuɗi aka yisu ba. tsayawa yayi daga
gabanta yana murmushi “as u wish ma
beauty” “Kamar dai yanda nafaɗa miki ɗazu
ina ganinki naji kinyi min,da farko dai ni
sunana Abdoul-wahab ina zuwa garinnan tym
to tym dan duba yan uwana, Ah Abuja nake
aiki ni Manager bank ne FCMB wato first city
monument bank, ina shigowa garin nan dake
nasoma arba sai naji ajikina lalle na samu
matar aure. Idan bazaki damuba zansu sanin
wacece ke”?. Cikin muryanta mai matukar
sanyaya ran mai karatu tace “sunana
Khadija,ammah amfi sanina da Candy”.
“Woaw!!!” Ya faɗa yana mai tafa hannu tattare
da murmushi “what a nice name Khadija”.
Yanda ya furta sunan yasake sa Candyƴcikin
wani shauki. Nan dai taɗan labarta masa
labarinta. “Toh Khadija bana son rikeki da
surutu da yawa dan naga 8:00 yawuce yanzu
kozan iya samun number ki”? Cikin sauri ta
ansa “banida waya fa”. “toh babu damuwa
beauty insha Allahu zan samo miki waya
wanda ya dace dake”. Cikin motan yakoma
miko mata kuɗi yayi wanda tunda take bata
taɓa ganinsuba balle harta rike irunsu, nan
take hannunta yaɗau rawa kamar mazari.
“karbii mana beauty” Sa hannu tayi carap har
tana yakushinsa da kyar ta tat’taro yawun
bakinta da nutsuwar ta kamin ta iya furta
“nagode”.
Tana shiga cikin gidan ta ɓoye kuɗin cikin
zaninta. “Aww harkin dawo hala gidan da
nisa” “Eee” kawai ta ceda Ummah. Sannan
tabi lafiyan gado lumshe idanu tayi tana
kallon kayatac’cen murmushinsa wani ihu ta
saki tareda rungume pillow a’hankali ta furta
wannan shine “`Mr Smiles•“`
Kuci gaba da kasancewa tareda mu
*TAGWAYEN MARUBUTA*
[6:01AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
*Rash Kardam*
*Ummieluff*
Page 81-90
Ahankali kaunan Candy ya soma mamaye
zuciyan Muh’d tun yana iya ɓoyewa har ya
kasa controlling feelings ɗinsa gashi baya son
raini koh kaɗan. Ko yaya soyayyan zai
kasance oho.
Gashi in ya zauna bai da tunani sai na Candy
in kuma bai sata a ido ba ranan bai da zaman
lafiya. Ya ringa sintiri tsakanin aji su Candy
da office ɗinsa. Har sai ya ganta kafin ya
samu sauki a cikin zuciyar shi don wannan
al’amari ya dawo mishi kamar jaraba sai ya
ganta ko ya ji muryanta.
* * * *
Wasu daga cikin ɗaluɓai sun soma zargin
wani abu, don yanda Malam Muh’d yasa ma
Candy da ‘yan group dinta ido. Abu kaɗan
zata yi zai hau faɗa ko punishment, ga wani
mayen kallo da yake aika mata ta cikin
glashin sa. Candy ko tamkar bata san Allah
yayi halitta a gun ba damuwar gabanta take
yi. Don ita hasalima haushi Malam Muh’d ke
bata. Wani zubin in suna zaune da su Kausar
takan ce mata “Candy nifa ina ga Malam
Muh’d sonki yake yi, Kiga irin kallon da yake
miki ga kuma irin yanda ya samu gaba ina
ganin salon nashi soyayyan kenan”. Mamu ta
nisa “kin san Allah Kausar nima na jima ina
wannan tunanin ga dukkan alamu ya faɗa
tarko sonki Candy”.
Wanni uwar hararan da Candy ta aika ma su
Kausar yasa su jan bakinsu suyi shiru. Cike
da masifa ta mik’e ta rik’e kuugu ta wani gir-
giza jikinta kalo ɗaya zaka yi ma fiskanta
kasan ta kai iya bangon kuluwa don har
bakinta yana wani ɓari, idonta ya juya kalar
ruwan madaran kwando bala’i ne kaɗai a
cikinsa. Kallon da ta musu sai da hantan
cikin Kausar ya juya Mamu kam kame-kame
ta fara tana bama Candy hakuri don ta san
karon su baya kyau.
“Kausar ki kama gutun mutunciki ki ja
zummar bakinki ki min shiru kin san Allah
duk lokacin da kika kara min zance wannan
mutumin sai na lahira ya fiki jin daɗi”. Kausar
wani miyau ta haɗiye don gaba ɗaya kayan
cikinta juyawa suke yi. “To wai ke a likitan
luv ko to inaga likitanci ki bai tafi dai-dai akai
na ba don banjin son Malam a rai na ina ma
zan kai mungu da shi to bari kiji ki kuma
buɗe kunnuwanki da kyau……..”. Maganan ne
ya makale mata a fatar baki, sakamakon jin
kiran da Malam Muh’d ya kwala musu, don ya
hango su, kira ya kwala musu don yaga
alaman Candy warning take musu. Jin kiran
Malam Muh’d ya sa Candy ta soma matsse
kafa don wani irin fitsarin da taji yazo mata.
Tabbas ta san gwamuwarsu bazata yi kyau ba.
Ganin yada take masu Kausar zai ɗauka
dukansu zata yi.
Ko da suka je sai ya kasa sa su aiki ko
tambayansu. Hannu yasa a aljihu ya ciro
gudan ɗari ɓiyar sabuwa ya ce”kuje school
shop ku sayo min lai dan pure water mai
sanyi”. Ya na juyawa Candy ta zauke wani
sassayan ajiyar zuciya wanda yaso bama
Kausar dariya amma ta make a cikinta sanin
halin kawarta Candy. Bayan sun sayo ruwan
suka kai masa ya amsa ya nufi office ɗinsu da
shi, su Candy kuma suka koma aji a haka har
aka tashi kowa ta nufi gida.
* * * *
Wata mota kirar Frado na hango fara tass tare
da bak’ak’eɓ glass a jiki ta fe ya ke mai motar
a hankali yana jin wakarsa kalo ɗaya nayi ma
fiskansa na gane tsantsan farin ciki gami da
jin daɗi dake shimfiɗe a fiskansa. A hankali
yake bin wakar tare da gir-giza kansa alamar
wakar tana sanya sa nishaɗi da sanyaya masa
zuciya. Gayen matashi ne baki mai dogon
hanci yana da faɗin kirji ga manyan ido masu
fiskan mace, yana da sajen da ya kara kawata
fiskansa. Wanda duk inda ake son namiji ya
kai. Abdoul-wahab namiji ne mai ji da kwalisa
gami da ji da kansa kalo ɗaya zaka masa
kasan yana cikin hutu da naira sun zauna
masa.
Tun daga nesa ya hango cikin tafiyar ta mai
ɗaukan hankali a nitse ta ke tafiyar tamkar
hawainiya in ka kura ma tafiyarta ido ka
ɗauka tausayin kasan take ji ko mu nan sai da
ta tafi da tunanin mu. Kalo ɗaya yayi ma
bayanta yaji wani abu ya tsarga masa a
zuciyarsa tunda ga kwanyar kansa har yatsan
kafarsa. Take yaji wani irin abu yana fisgansa
gudun mota ya kara yazo dai-dai gabanta ya
tsaya. A hankali ya buɗe motar ya fito ya tsaya
a gabanta tare da harɗe hannusa a kirji ya
zuba mata ido tamkar wani waye don
yarinyan ta gama tafiya da shi.
Kanta a sunkuye tana tafiya jin mota ya tsaya
a gabanta dummm!!! Taji kirjinta ya buga
wani irin ruwan kwandon bala’in masifa ya
zo mata cike da mafisa da wani tsiwa ta ɗago
wanda har kwayan idonta na wani kala-kala.
Tana ɗagowa karaf suka haɗa ido take taji
wani sanyi ya sauko mata tunga kanta har
tafin kafarta. Duk masifa da tsiwanda ta ɗago
ido dasu take ta nimesu ta rasa sun gudu.
Tirkashi lallefa masu karatu zamuso jin wacce
yarinya ce wanna.
*“`TAGWAYEN MARUBUTA“`*
[6:01AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
*“`Rash Kardam“`*
*“`Ummieluff“`*
Page 101-110.
Tana shiga cikin gidan ta ɓoye kuɗin cikin
zaninta. “Aww harkin dawo hala gidan da
nisa” “Eee” kawai ta ceda Ummah. Sannan
tabi lafiyan gado lumshe idanu tayi tana
kallon kayatac’cen murmushinsa wani ihu ta
saki tareda rungume pillow a’hankali ta furta
wannan shine “`Mr Smiles•“`
Sai da ta gama tunane tunane “`Mr Smiles“`
ta tashi ta cire kayan jinkinta, wani dogon
riga ta dauko na bacci ta sanya tukun ta hau
gado tayi addu’a ta kwanta cike da tunanin
saurayinta. Washe gari ya kamata talata ranan
Candy da wuri ta shiya zuwa makaranta a
cikin kudin da “`Abdoul Wahab“` ya bata ta
dauko dubu ɗaya da biyar ta ɓoye a cikin
littafinta. Umma ta kalli Candy ta ce”yau
bazaki karya bane?”.
Take Candy ‘yan hanjinta suka motsa. Cikin
yanayin rashin kuzari ta kalli Umma ta
ce”zanci amma yau cikina ke ɗan juya min
kamar ya ɓaci”.
Cikin alhini Umma ta ce”ashsha! Ashsha!!
Sannu to ki rage ciye-ciye gudun karya kara
ɓata miki ciki. Gashi ba wani kuɗi a hannuna
da kin je chemist ki sayo magani. Yanzu ki
ɗan shafa toka a saman cikinki zakiji dama-
dama”. Duk Umma ta damu akan Candy.
Candy ta ɗauko kwanon abinci taci kaɗan ta
mike ta ce”Umma na tafi sai na dawo” Ta sa
kai ta fita.
Tana fita ta nufi wani shagon da ke kan
hanya ta sai cake da nutric milk gora uku ta
bashi kuɗin ta nufi makaranta. Tana zuwa ta
samu ba a wani zo ba, hakan yasa ta ciro
cake ɗin taci sannan ta ajiye wa su Mamu
nasu.
Ba da daɗewa ba su Mamu suka zo nan fa ta
mika musu tare da basu labarin komai. Su
Kausar sun matukar tayata farinciki da addu’a
alkairi, a haka suka ɗau darasin ranan har
aka tashi a makaranta.
A hanya taga wani karamin restaurant nan ta
tsaya tai musu take away biyu na jelop rice da
yaji naman saniya akai da maltina gwan-
gwani hudu. Ta saka a leda ta nufo hanyan
gida.
Tana zuwa k’ofar ta ja ta tsaya nan tunaninta
ya dawo cikin zuciyarta ta ce”yanzu in an
tambaye ince a ina na samu”. Kai ta ɗaga tana
nazarin abun can ta saki wani lallausar
murmushi ta nufi cikin gidan da karfin
gwuiwa tana zuwa kwaɗa sallamanta da karfi
“Assalamu’alaikum”
Umma ta amsa mata da
“Wa’alaikumusalamu”. Ta na shiga kallo daya
tayi ma Ummanta ta gane ba abbinci. A
hankali ta zauna a tabarma tare da faɗin
“washh!! Yau na gaji”. Umma ta kalleta cike
da kulawa ta ce”sannu ya makarantan?”.
“Alhamdulilah!!”. Candy ta faɗa tare da miko
ma Umma laida.
Umma ta kalleta ta ce”miye aciki kike miko
min?”. Cikin muryan shagwaɓa Candy ta
ce”Umma ki buɗe ki gani tukun”.
Umma tana buɗewa taga take away cikin
kallon tuhuma ta ce”ina kika samo wanan?”.
Candy tayi murmushi ta ce”Ummana munje
debate ne yau aka rarraba mana nikuma na
ɗau har biyu nasan muna da bukata”.
Umma ta ce”kinsan ba kyau haka kowa
ɗaɗɗaya aka bashi ke ki ɗau ɓiyu”.
“Umma ai na faɗa ma Aunty mu ni bazanci a
gun ba zanzo dashi gida shiya ma na ɗau biyu
kuma ta sani tace ba matsala”.
Umma na jin haka ta sauke ajiyar zuciya nan
suka ci abimci harda barin saura suka kora
da drinks abunsu.
Haka Candy tayi ta gudanar da rayuwa cikin
kwana uku sai tai dabara sun ci abinci mai
kyau. Ba tare da Umma ta gane ta ba.
Yau ta kama jumma’a da yamma Candy taci
kwaras ɗinta da atamfar sallanta ba laifi tayi
kyau sosai. Littafin turanci ne a hannunta
tana dubawa wani yaro yazo da sallama.
Candy ta ams yaron ya ce”wai ana sallama da
Candy a waje”.
Umma ta ce”inji waye haka?”.
Yaron bai daɗe ba ya dawo ya ce”wai inji
“`Abdoul wahab ne”.“`
Candy ta ɗan kalli Umma ta ce”kaje kace ina
zuwa”. Yarin yana fita, Umma ta ce”Khadija
yaushe kika fara hira ban sani ba?”.
Candy ta maraice fiska ta ce”Ummi na kiyi
hakuri wallahi yana da hankali sosai”. Nan
taba ma Umma labarinsa, Umma ganin yarta
Candy tana son *ABDOUL WAHAB* yasa ta
aminta ta bata izinin fita tare da fatan alkairi.
Candy tana zuwa k’ofar gida ta canza salon
tafiyarta tamkar wata hawainiya cikin
nutsuwa da takama ta ke tafiya. *Abdoul
wahab* zuba mata mayatattun idon sa yayi ya
kasa ɗauke kansa daga kallonta. Cikin
zuciyarsa ko cewa yake”gsky duk cikin matan
zamannin banga kamar Candy ba komai nata
dabanne ga aji tabbas nasan nan gaba gogewa
kaɗan zatayi ta zama mace mai class, mace
wuce raini, mace nuna ma sa’a”.
Wani lallausan murmushi ya sakar mata dai-
dai lokacin da ta karaso gurin. Cikin yanga ta
kara make murya ta ce” *Mr Smiles* ka yini
lafiya? Ya jumma’a?.
Abdoul wahab mutuwar tsaye yayi sabida
yanda Candy ke sarrafa bakinta da sunan da
ta kirashi da shi. “tabbas baki yi karya ba
sunan ya dace dani kuma ya min daɗi gaskiya
ni mutum ne mai yawan murmushi.”
Candy tayi wani fari da ido kai ka ɗauka wata
babbar macece yanda take iyaye, duk ta rikita
Abdoul wahab. Cikin kan-kani lokaci suka
kara sabawa hira suka yi sosai.
Sai dab Magriba Abdoul Wahab ya mata
sallama tare da mika mata wasu manyan
laidoji guda biyu.
Candy ta ki karɓa sai da taga ya bata rai kafin
ta amsa ta masa godiya ta shiga gida.
Ko da ta shiga Umma faɗa tayi mata na karɓan
kaya, nan ma tayi bayani ma Umma akan taki
shi ya dage daga karshe Umma ta sanya ma
abun albarka kafin suka buɗe kayan da ke
ciki kamar haka; riga da skirt guda biyu
dogon riga biyu sai atamfa wanda aka dinka
biyu da takalma uku da poss uku sai kayan
shafe-shafe. Abun dai son barka don kowani
kaya Candy tasaka zai haska ta bana wasa ba.
Umma taji dadi ta kara godiya da sanya masa
albarka.
Candy kuma rawan kai zai karu kenan tunda
ansoma yin kaya masu kyau…lol..
Bayan kwana biyu Abdoul Wahab yayi mata
sayya na kayan makulashe sosai. Ya sai mata
waya Samsung Galaxy.
Tun daga wanna rana suna makale da juna a
waya har ya koma gun aiki.
Munay ce ta shigo cikin hanzari ta gaida
Umma nan ta tambayi Candy Umma ta
ce”tana daki”. Ba tare da bata lokaci ba
Munay ta shiga ta samu tana gyara daki tana
ganinta suka rungume juna dan murna.
Munay ta ce”Candy kin kusa gama aikin ne?”.
Candy ta ce”eh shara kawai zanyi shikenan”.
“Ok to kiyi muje wani gida ne a kayi rayuwa
can unguwan Mu’azu”.
Cikin zakwadi Candy ta ce”da gaske?”.
Munay ta ce” eh kai har an kai gawar ma yau
kwana daya”.
Candy ta ce”kai wolla har ina jin yawuna ya
tsinke na kwana biyu banci abincin *Gidan
rasuwa* ba”.
Munay ta ce”ni ma haka”.
Ba tare da bata cokaci ba ta gama aiki suka
zuga ma Umma karya suka fita. Suna zuwa
gidan rasuwa kamar abun arziki sukai ta
kuka har sai da aka kawo musu abinci sukaci
sannan suka mike suka bar gidan.
Zuciyansu dauke da farin ciki kal!! Kamar an
musu albishir da gidan aljannah.
“Oh!! Muko mukace Hali a jikin rai, mai hali
baya fasa halinsa a ko ina yake”.
*“`TAGWAYEN MARUBUTA“`*
[6:01AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
“`Ummieelurv
&
Rash kardam“`
Page 111-120
Misalin 8:00am Candy na bakin gate na
makarantan su tun daga nesa tasan yau zataci
duka sabida tayi latti. Malam Muh’d ta gani
da wani zabge’gen dorina yana dukan ɗalibai,
tun daga nesa ta soma tafia a karkace tana
matse cinyoyinta da alama fitsari takeji sosai.
Abun har daria ya bamu. _Kneelin down_ aka
saka su ammah na Candy dan rashin kunya
samun qaramin dutse tayi ta zauna akai babu
wanda yake kallonta. Layi’layi ake dukansu
har akazo kan candy nan take jikinta ya
ɗauki’rawa idanunta suka canza launi nan
take hawaye yasoma zubowa. ” kee ni kikeson
inzo inda kike da kaina ne”? Cikin saurin
Candy ta mike sai ganin dutse yayi a bayanta
“owk wato gaki mai wayo kenan kowa nakan
kneel ke kina zaune to punshment ɗinki will
be double.” Iho ta saka “Malam dan Allah kayi
hakuri wlhy na rantse ban zaunaba harna
rantse Malam.” Yanda Candy ke rantse-rantse
taso bawa Malam Muh’d dariya amma sai ya
gintse. Aga bulalan yayi ya zabga mata sau
ɗaya ta mike tsaye tana rokonsa da kyar ya
bula’leta sau ukku. “Mugu kawai haka zaka
kare”, Sannan ta wuce aji tana harare-harare
kowa a ajin sanda ya nutsu.
“`BAYAN SATI BIYU“`
Da dare Candy na kwance tun safe yau basuyi
waya da Mr smiles ɗinta ba duk sai taji babu
daɗi. Da misalin takwas da rabi taji rurin
wayanta kamar bazata ɗauka ba ammah sai
tayi tunanin shine. Tana ɗagawa kuwa sai
sunansa ta gani bayyane jikin screen ɗin
rangaɗa’ɗau. Wani lallausa murmushi ya
baiyana akyak’kyawan fuskanta. “Hi
handsome! Av’been waitin for ur call since
morning,hope all is well with u”? Shiru taji
bai ansa taba sai can taji yace “kiyi hakuri
dan Allah yau ina cikin tashin hankali mara
misaltuwa” mikewa tayi daga kan gadon
“OMG meke faruwa haka?wani abune
yasameka?” Ta jero masa waɗannan
tambayoyi. “mum ɗina ce ta rasu ɗazu da
asuba.” “Innalillahi-wa’inna-ilaihi raju’un”
candy ta furta tareda dafe kirji. (0o ikon Allah
yau Candy ce da jajanta mutuwa) “meya
sameta ko dama batada lafia ne”? “lafianta lau
wlhy,ɗazu da safe taketa complaining ciwon
kai,sai tasha magani daga can shikenan bata
tashi ba.” Candy ta zaro ido hankali tashe dan
mutuwan ya tsorata’ta. Ahankali ta furta
“Allah ya rahamsheta yasa ta huta” muka
haɗa baki wajen faɗin {“first in history.”} “ki
sanar da mama dan Allah jibi sadakan ukku
zanzo sai muje ki gaishesu,” “to shikenan zan
sanar da ita Allah kara hakuri.” “Ameen” yace
tareda katse wayan.
“`WASHE GARI“`
Candy na kwance aɗaki tana game da wayanta
sun gama waya kenan da Abdoul. Taji an faɗo
ɗakin pamm kamar an wurgota har Candy ta
tsorata ta yasar da wayan tana neman hanyan
ɓuya. “mustew ammah miemie-bee ni bansan
ke wace irin sokuwa bace wallahi,bakisan
irin haka zai iya saka mutun cikin wani hali
bako,yanzu da hawan jini gareni da na
mutu.” bee batayi magana ba ta sanu waje
daga gefen Candy ta zauna tareda dafata
“kawata yau ko zagina kikayi bazai dameni
ba,dan nazo miki da daɗa’ɗan labari” candy ta
tashi zaune tace ” ke dan Allah”? “Eƴƴ mana
ba har zagina kike ba, wani yasuwa akayi
anguwan mu, Kinga kuɗi kawata wallahi
masu kuɗine na hakika kinga ruwan juice da
kaji da ake goge hakora da wanke makoshi.
“mustew shine kike son kasheni sabida ɗan
wannan”? Toh bazani ba dallah ki kyaleni ina
cikin jimamin mamar mijinda zan aura ta
rasu.” wangale baki miemie-bee tayi cikeda
mamaki Candy gidan *Zaman makoki* nefa”
“ke ba gidan zaman makokiba ko inane bani
zuwa ayau” da kyar dai bee ta zuga Candy
zuwa gidan makokin da aƙe. wannan shine
karo na farko da Candy taji bataso zuwa gidan
zaman makoki ba. Gidan su Munay suka je
tare da sanar mata komai cike da murna ta
zaro hijab suka fita.
Suka kama hanya sai kofan gidan suka bi
mutanen da ke ta shiga gidan suna shiga
cikin gidan Candy tayi mutuwar tsaye dan
yanda taga gidan tsaruwa iya tsaruwa ya
tsaru wanda yasata sakin baki tana kallon
gidan. Cikin gidan suka nufa nan ne suka
sake ganin haɗuwan gidan ammah kowa kuka
gani cikin gidan yana cikin bakin cikin
rabuwa da mamacin. Abinci aka kawo ga
paper soup, gasasshen nama,da kuma drinks
ammah babu wanda yayi masa kallo biyu. Su
candy sai zazzare idanu akeyi matan tace
“bismillah mana” tana nufin su sami wajen
zama dan gaida yan uwan mamaci. Ammah
ina su a’tsammaninsu ancene suci abincin,
habawa suka rufu akan abincin kamar ba
gobe basu lura da irin kallonda ake musuba.
Wata yar budurwace ta shigo ganin su Candy
kasa magana tayi ta tsaya tana ganin ikon
Allah.
Candy ci take ba sassauci ganin cikinta
yasoma dauka sai ta zaro wasu laidan Walima
kwaya biyu ta soma juye abincin aciki dai-dai
nan wata mata suka shigo da gani kamanin
su dayane ko muce ma yarsa ce, tare da
*Abdul-wahab* suka shigo dakin cikin razana
Candy ta dago ga laida ta shake shi da
shinkafa da nama. Turus *Abdul-wahab* suka
tsaya. “Yasalam” Candy ta ce take yayan
hancin cikinta suka soma juyasa shikenan yau
mai aukuwa ra auku. Abin kunya agidan
*SURAKAI.*
*TAGWAYEN MARUBUTA*
[6:02AM, 9/21/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
“`Ummieelurv “`
&
“`Rashida A Kardam“`
Page 121-130
Kasa magana Abdoul yayi dan besan me zai ce
ba shi da kansa kunyan yan uwansa ya
kamashi he’iz speechless ammah kina ganin
idanunsa kinsan akwai matsala dan ransa
yayi mutukar ɓaci da abunda Candy tayi masa.
Shin wannnan wace irin macece?
Shin mema yakaishi neman yarinya irin
Candy?
Shin meyasa bai yi bincike ba kawai ya afka
soyayyah da ita?
Shin me yan uwansa zasu ɗauke sa?
Mutuminda bai san abunda yake yi ba mana.
Wani zuciya ya sanar dashi. Kallon Candy
yake da disappointment a kwayan idanunsa.
Baiwar Allah kuma jikinta yayi sanyi sosai
wanda bata taɓa tsammanin akwai rana irinta
yau da abu irin haka zai sameta ba. Wayyo
Allah nashiga ukku. Yanzu yaya soyayyanmu
zai kasance?
Anya kuwa Abdoul wahab zai yarda da
aurena ayanzu?
Anyan yan uwansa zasu sake yarda dani
kuwa? Innalillahi-inna’ilaihi Raju’un ya Allah
ina neman mafita agarwka.
Da kyar Abdoul wahab ya buɗi baki yace
“Yanzu Khadija abunda kika yimin kin kyauta
kenan? Yaya za’ayi kizo gidanmu ki zubda
min mutunci ki kuma zubdawa kanki
mutunci,wane irin rayuwane kika sawa
kanki? Kina ganin abin burgewa ne kizu
gidan makoki kike cin abinci kina
nishaɗi,bakya tunanin kema wata rana naki
zai iya rasuwa azo gidanku amiki irin abinda
kika min yaya zakiji kenan?”. Ee’e nasan bai
kamata azo gidan makoki ayita ihu da
koke’koke marasa amfaniba,hasalima anfison
ku zauna daga gefen wacce akayiwa rasuwan
kuke ɗan hira dan yaɗan rage mata kunci da
takeji agame da rashin da akayi mata. Ammah
kirasa abunda zai saki nishaɗi sai zuwa gidan
makoki bama dan jajanta musuba a’a ke
kawai dan kice abu mai daɗi. Baki damu
dame yan uwan mamacin zasu jiba ganim
suna bakin ciki,keko kina farin ciki.
Kiduba wannan mahaifiyata ce tarasu duk da
naji zafin rasuwan’ta ammah abinda kika min
yafi yimin zafi dan kin nuna baki damu da
damuwana ba, ya nuna bakya *tare’da ni*
kenan,mahaifiya tace ba taki ba, haka
Khadija abunda zaki saka min dashi kena?
Duk irin tsananin so da kauna dana nuna
miki,na kudiri niyar mayar dake u’war
ya’yana,ashe Allah yataimake ni daban aureki
ba kika haifamin yara masu irin halayenki,
Kaichona.” banda kuka babu abinda Candy
take Arayuwa bata taɓa soyayya ba sai akan
Abdoul,bayan Ummanta babu wanda take
jinshi har’a zuciyanta irinshi. Abdoul shi
kaɗai nakeso banajin zan’iya kaunan wani
kamarshi gashi yanzu abinda yasameni
kenan. Kai Allah na tuba. Mikewa tayi jiki
asanya’ye ta isa garesa “Abdoul nasan nimai
laifice agareka ammah ina rokonka dan Allah
kayi hakuri,nayi maka alkawarin daga rana
irinta yau na daina abinda nakeyi matukar ka
yafe min kuma ka yarda zaka aureni wallahi
harna rantse maka bansan nan gidanku
bane,Abdoul ni yarinyace bansan komaiba
banda sonka,dakai nasan me ake nufi da
kalman so, *So ɗaya tak* nake maka dan
Allah kayi hakuri.” tana kaiwa nan ta fashe
da kuka abun gwanin tausayi miemie-bee
banda zare idanu babu abinda takeyi awajen
duk abinnan dayake faruwa tana rike da
ledanta data ɗura zalalan tsokan naman kaza
aciki. Kuka Candy take har tsungunawa
agaban Abdoul tana rokonsa daya yafe mata.
Ɗagota yayi cike da so yana share mata
hakaye “ki daina kuka beauty na,yaranta ke
damunki na yaff-” bai karasa ba wacce muke
tsammanin yayar sace tayi karap ta buge
hannun Abdoul tareda fashewa da kuka “Ashe
bakada hankali Abdoul,ashe zaka iya zaban
soyayyah over mahaifiyarmu wacce ta
kawomu duniya.” kuka take harda majina ita
adole batason Candy “idan har kana sonta to
saida kazaɓa ko mu ko ita-” “a’a haba ya’ya ki
daina wannan zancen dan Allah yaya ma zaki
soma faɗin irin waɗan’nan muna’nan
kalaman.” wani kallo yawatsawa Candy “tashi
kije nagode kema wata rana zakiji irin yanda
naji nima” kuka take tana rokonsa ammah
yaki sauraronta badan ranshi nasoba yakori
Candy koran kare daga gidansu idanunsa sun
rine jajaye.
“a’a dawo mana ki ɗauki ledanki wazaki
barmawa”? Candy ko kallon inda Yake batayi
ba wannan shine karo na farko da Candy ke
ganin kaza da idanunta ammah ta barshi
bataci kota sace ba. “kee zoki ɗauka mata”
sukace da mie-mie ko kunya babu ta juya zata
koma wani irin shaka Candy tayi mata ta
rinka janta kamar tinkiya har suka fice zuwa
bakin gate. Suna fita tayi wulli da ita tareda
watsa mata kyawawan mari guda 2″ Ammah
dai miemie-bee Allah ya isa tsakanina
dake,har duniya ta naɗe bazan yafe
mikiba,sanda nace miki bazan zoba kika nace
sanda nazo yanzu me kika janyo min kenan”?
Miemie dake kuka tace “wallahi candy kiyi
haKuri bansan haka abun zai kasanceba.”
‘dan uwarki da kika sanin ma kin mutunta
nine inace komawa kikayi niyyanyi dan ɗauko
min leda,wallahi kika sake magana zan
ɓabɓallaki munafuka kawai.” miemie zatayi
magana candy ta ɗaga hannu kamar zata
mareta ta gudu.
Kuka take ta shiga gida yanda umma taga
idanunta da yanda take kuka yasata rikicewa
“ƙhadija meya sameki kike irin wannan kuka
haka”? candy babu ansa sai kuka tanason ta
faɗa mata tana tsoro “ummah mamar kawata
ce ta rasu shiyasa nake kuka” “aiya addu’a
yakamata kiyi ba kuka ba kirinks mata
addu’a, dafatan dai bakiyi halinkin a gidan
zaman makokin ba”?zaro idanu tayi cike da
tsoro kamar umma ta ganota. Da haka dai
tarinka lallashinta ranan ai candy batayi
bacciba,tana rufe idanunta photon abinda
yafaru take gani adanunta. Tashi tayi ta
zauna tana jimamin rabuwa da mr smiles
ɗinta.
****
Tun daga wannan ranan Abdoul bai sake bi ta
kanta ba. Don yan uwansa sun rabasa da ita.
A haka har akayi bakwai ya koma bakin
aikinsa.
****
Candy duk ta rame ga yawan tunani Umma
tayi faɗan har ta gaji sai addu’a take mata.
Candy kulum cikin zuba ido take ko Abdoul
zai dawo shiru.in takira wayansa baya ɗauka,
daga karshe ma yayi blocking ɗinta. Wani
sa’in taci kuka a ɗaki ita kaɗai duk damuwan
duniya ya isheta. Saukin da ta sami yanzu
sam Malam Muh’d baya shiga sabgarta. Ya
rage tsangwanta..
****
*BAYAN WATA BIYAR…*
Haka rayuwan Candy ya ci gaba da tafiya ga
Ummanta yanzu bata da ishashen lafiya yanzu
wataran ita ke wankin kuɗin, don ta sama
musu abunda zasu ci dana maganin
Ummanta. Kullum cikin kuka take da rokon
Allah ƴya tashi kafaɗun Ummata ya bata
lafiya.
*TAGWAYEN MARUBUTA*
[8:50PM, 9/22/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
_Rash Kardam_
_Ummieluff_
“`Page 131-140“`
Jikin Umma kara tsanani yake yi, Candy duk
ta rame kullum cikin kuka ta ke gashi ba yan
kuɗi a hannunta. Ga shi yanzu Abdoul ya fita
harkanta duk da yanzu bata kansa take ba, ta
jinyan Umminta take. Wani sa’in da kyar ta
ke samun aikatau tayi kafin ta samu kuɗin
magani, rayuwansu ta dawo abar tausayi ga
al’umma. Boko ta bar zuwa sai su Mamu da
Kausar da ke ɗan leko ta. In sunzo suna bata
ɗan kuɗaɗen da suka tara wani sa’in har
kukan murna take yi don tabbas su Kausar
kawaye ne nagari masu halin kirki.
****
Malam Muh’d duniya ta masa kunci tun randa
ya samu labarin Candy tayi saurayi ranan har
kuka sai da yayi *MAFARKINSA*
tana soyayya da wani tasan mai ya kawo sa
teaching makarantansu? Anya tasan ko shi
waye? Idan kuɗi ta ke so yana da miloyin da
zai sayi soyayyarta harma yayi yawa.
“Candy sabi da na kasance *TARE DA
KE* na bar gata na da yan uwana nazo gare
ki. Bana iya bacci sai da photon ki a idona,
zuciyata na cike da kaunarki,kaunarki tamkar
makullin rayuwata ce”.
Ya share wasu zafafan hawaye tare da furzar
da iska mai zafi.
“Ina sonki Candy naga kina tsananin son
Abdoul-wahab bazan rabaki da abunda kike
soba, ya zama dole na yi nesa da ke naje naga
iyaye na ko zan sami sassaucin suyan da
zuciyata ke min”.
Mi kewa yayi ya fara har-haɗa kayansa ya bar
wanda zai saka kaɗai a waje. Wanka ya shiga
bai daɗe ba ya fito sauri-sauri ya gyara jikinsa
ya sanya kaya tare da fesa turaruka masu
sanyin kamshi. Cikin gidan ya shiga ya musu
sallama, ɗakinsa ya dawo ya ɗauki jakarsa ya
rataya ɗaya a kafaɗa, ɗaya hannun kuma wani
katon photon Candy ne wanda aka zana masa
ya zuge trolley ɗinsa ya saka a ciki. A hankali
ya janyo trolley ɗin tare da manna bakar glass
a fuskansa. Yana fita bai zarce ko ina ba sai
gidansu Candy ya ɗan ɓuya a lungu har yazo
yaga wucewarta. A hankali ya rinka binta ba
tare da ta sani ba yana ɗaukarta photo. Wayar
sa ce ta soma ruri cikin hanzari ya ɗaga
bayan sun gaisa daga ɗaya bangaren aka
sanar masa saura minti talatin jirginsu ya
tashi. Cikin sauri ya katse wayar yana wai-
wayen Candy har ya tsari ɗan acaɓa sai
Airport yana zuwa bai daɗe ba aka masa
abunda ya dace jirginsu ya ɗaga zuwa Saudia.
Ganin jirgin ya tashi na juyo da sauri na kalli
Ummieluff.
“Wai nikam waye ne wannan Malam
Muh’d ɗin? Iyayensan suna inane da zama?
Naji yace zai sai soyayarta da miliyoyin
kuɗaɗe?. Kai na ya kulle ina da tambayoyin da
nake niman amsa”.
Ummieluff ta sauke ajiyar zuciya tare da wani
gwauron numfashi.
“Yanzu kawai jirgin online network zamu
hau mu bisa inaga hakan zai fi mana zaurin
cimmasa don mu samu labarin da muke son
ji”.
 Murmushi nayi mata wanda sai da kumatu
na ya lotsa.
“Yauwa kawalli haka za’ayi”. Na faɗa mata.
Tsalle mai kyau mukayi sai cikin jirgi Online
Network take ya lula da mu cikin gajimare
gudu yake yi salansar jirgin tana bulbula
hayaki…lol. tamkar murhum da aka garkama
motar icce bata ci. Ba tare da ɓata lokaci ba
muka hango jirginsu M Muh’d.
Munyi tafiya mai nisa kafin muka iso jiddah
nan jirgin mu ya sauka.
Muh’d na sauka mota ya shiga zuwa cikin
garin Makka nan mahaifinsa ke da zama.
Tafiya mai nisa sosai sukayi wanda sai da
suka kwana a hanya.
Notice kunsan jirgi bata sauka a Makka sai
Jiddah. Kar wasu suga munsa hakan
wa’yanda basu san da hakan ba.
Yana sauka ya sake hawa taxe zuwa wani
katafaren unguwa. Dai-dai wani kofar gida
mai kyau na gani na fada suka tsaya. Ya ciro
kudi ya basa bai tsaya jiran sauran ba ya nufi
gate ɗin ya kwan-kwasa mai gadi ya leko
ganin Adnan ne ya washe bakin da sauri ya
buɗe masa ya shigo.
“Ranka shi daɗe kai ne haka ko labarin
zuwanka banji ba a gun Hajiya”.
Murmushi Muh’d yayi mai bayyana
kyansa.
“Eh nine suma basu san da zuwana ba sai
yanzu inna shiga ciki”.
Mai gadi ya masa sannu da zuwa. Muh’d ya
nufi cikin gida.
Hajiya Fatima da suke falo da Abban Muh’d
da sauri suka mike cikin farin ciki suke
tambayar lafiyansa.
“Abbah da Ummie lafiyata lau haka mutanen
9ja ma duk kalau suke sunce a gaida ku”.
Cewar Muh’d.
“Mashaa Allah”. Su Abba suka faɗa a tare.
Bayan ya huta ya ci abinci nan sukayi hiran
yaushe gamo har kusan shaɗayan dare kafin
yaje ɗakinsa ya kwanta.
Da safe Ummie da kanta ta haɗa masa
breakfast mai lafiya bayan sun karya suka
taɓa hira nan take tambayarsa Candy da ke
yawan bata labarinta. Cikin dabara ya kawar
da zancen suka ci gaba da wani hiran.
*WAYE MUH’D ADNAN(ADEEL)*
Muh’d Adnan haifafen Saudia ne amma
Mahaifiyarsa yar Gombe ce sai Mahaifinsa
Alhaji Aliyu yahya haihaffen ɗan Mai
dugurine karatu ne ya kawosa kasa mai
tsarki. Wanda a zuwan Fatima(Ummieluff)
Ummurah suka haɗu har suka fara soyayya
cikin ikon Allah akayi aure. Daga nan ta dawo
Madina da zama. Sun daɗe da Aure kafin
Allah ya azurtasu da ɗa guda ɗaya tilo wato
Muh’d Adnan suna kiransa da *Adeel.* Adeel
ya taso cikin gata har Allah yayi mahaifinsa ya
kammala Masters ɗinsa ya fara ɗan aiki a
Madina. Bayan wasu shekaru kasancewar ya
rike gaskiya da Amana. Nan Allah ya haɗashi
da wani balarabe mai suna Alhashim.
Alhashim ya kasance mai kuɗi ne sosai yana
da rijiyan man fetur. Ganin gaskiyan Alh
Aliyu yahya yasa ya ɗaukosa ya ɗaurasa a
harkan ba da daɗewa ba shima ya bun kasa
ya haɓaka. Ganin hakan yazo gida 9ja ya buɗe
gidan mai da campany yin shinkafa da sugar.
Bayan wasu shekaru lokacin Adeel ya girma
suka zo 9ja ganin yan uwa. Nanne suka ga
campany ba wani ci gaba hakan yasa Adeel
yace zai zauna tunda ya kammala karatunsa.
Wannan shine dalilin zuwansa 9ja da zama.
Bayan wasu watanni ya ga komai na campany
ya zama dai-dai hakan yaji yana da sha’awar
koyarwa hakan yasa yayi interview na
teaching yaci bayan nan ya fara koyarwa yana
kula da Campany su. Ananne ya ga Candy har
ya fara sonta. Kuma wannan shine dalilin da
yasa bai koma Saudi da wuri ba sai da Candy
ta fara soyayya da Mr Smile. Dalilin da yasa
yaji kasan Nigeria ta gun duresa ya shirya
barin garin ba shiri. Har ya taho kasar da
iyayensa suke wannan shine tarihinsa.
*******
Jikin Ummin Candy kara tsanani yake yi
wanda hakan yasaka suka je Asibiti. Gado a
ka basu likitoti sunyi caa akan Ummi amma
abu ya faskara nan suka sa mata drip ganin
Candy tana cikin wani hali yasa basu sanar
mata komai ba. Da kyar suka barta ta shiga
gun Umminta. Ummi ta kama Hannun Candy
ta rike cikin nishi da muryan marasa lafiya
wanda jiki yayi tsanani ta soma cewa.
“Khadijatu ki buɗe kunnuwar ki kiji mai
zance miki”. Tari ta ɗanyi kafin ta dafe gefen
kirjinta ta lumshe ido ta buɗe.
“Khadija ina son ki kasance mai hakuri da
juriya a rayuwanki. Kar kiyi wasa da ibada
duk rintsi-duk-wuya ki rike amana gaskiya da
zumunci. Karki manta da tarbiyan da muka
baki koda bayan raina ki kasance mai yi min
addu’a da mahaifinki da sauran musulmai. Ki
kasance mai taimako a duk inda kika ga mai
neman hakan matsawan bai saɓa wa addini
ba. Dan Allah kar ki kina niman faɗa ki rinka
hakuri duk inda kika samu kanki. Aaah!
aaah!! Tayi tari ta cije leɓenta sabida zafin da
take akirjinta.
Candy ko in banda kuka ba abinda take yi
cikin zuciyarta ko sai furta “ina! Umma zaki
tashi bazaki mutu ba”.
“Khadija ni kam ba tashi zanyi ba tawa ta
kare ki kara hakuri a duk inda kika sami
kanki. Kasancewar ba wanda zaki zauna a
gunsa in kin samu miji kiyi aure. Ko zaki yi
karatu sai bayan kinyi aure don gidan mijikin
shine mutunciki. Martaban mace shine gidan
mijinta..dan Allah khadija ki daina zuwa
gidan *ZAMAN MAKOKI*Wanda nasan ya riga
yazame miki jika ayanzu”. Cikin sauri candy
ta suma girgiza mata kai” wallahi ummuh
nadaina daga yau” murmusawa ummah tayi
sannan ahankali ta furta “Allah miki albarka”
Nasiha sosai tayi ma Candy.
Candy in banda kuka ba abinda take yi.
Ummi ta fara wani irin tari tana kakari tana
salati idon ta suka soma kafewa a sama.
Candy ganin haka ta kurma kara tana kiran
“Ummi! Ummina!! dan Allah kar ki tafi ki
barni in kin tafi wa zan zauna dashi. Ko kin
manta ke ce gatana,da ke kaɗai nake gani
nayi murmushi banda kowa sai Allah sai ke.
Ummi karki tafi ki barni ina zan saka kaina?
Ina zan zauna? Abba ya tafi kema so kike ki
bisa? Zaki bar Candyn ki mai kaunarki. Ummi
in nice na dai na rashin ji zan zauna da kowa
lafiya zan na duk abunda kike so”.
Wani irin kuka Candy take yi mai tsuma
zuciya tana jijjiga Umma. Likitoci ne suka
shigo suka rike ta tana fisgewa tana kiran
Ummanta.
Duk fuskata ya jike da hawayen tausayi na
ɗago karaf naga Ummieluff itama kukan take
yi abun gwanin ban tausayi. Rayuwa kenan.
*“`TAGWAYEN MARUBUTA“`*
[5:34PM, 9/24/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
_Rash Kardam_
_Ummieluff_
*_page 141-150._
Wani irin kuka Candy take yi mai tsuma
zuciya tana jijjiga Umma. Likitoci ne suka
shigo suka rike ta tana fisgewa tana kiran
Ummanta. Suka fita da ita waje tana wani irin
kuka mai tsuma zuciya ɗauke da tausayi a
ciki. Dai-dai lokacin sai ga Baban Munay yazo
duba su da Mamanta sun iso suka taras da
rasuwan Ummin Candy jikinsu yayi sanyi.
Maman Munay har ta fara kuka ita ta rike
Candy Baban Munay yasa su a keke Napep
suka dawo gida. Shikuma ya samo mota da
wasu bayin Allah suka dawo da gawanta gida.
Rayuwa kenan dukkan wani rai sai ya ɗan-
ɗani mutuwa.
A haka aka shirya Umma nan a kazo za’afita
dan mata Sallah akaita gidanta na gasky.
Candy na ganin haka ta kurma kara tana bori
tana ture masu riketa da gudu taje ta rike
makaranta tana kuka “Umma pls ki tashi kice
wasa kike min kin ga zasu tafi da ke. Banda
kowa sai Allah sai ke in kin tafi ya zanyi.
Wayyo Umma na mai kaunata ki tashi daga
yau zan ji duk abunda zaki ce min. Ko gidan
makoki ma na bar zuwa ki yarda dani Umma
sauko mu tafi ɗaki”.
Duk wanda ke gun sai da ya zubar da hawaye
don Candy abun a tausaya mata ne bata da
kowa yanzu sai Allah. Baban Munay yayi
karfin halin janyeta daga makaran tana
turjewa aka shiga da ita ɗakin su.
Maman Munay ta ce“Khadija kiyi hakuri kin
san abunda kike haramun ne ba kyau. Yin
kuka kana kururuwa ga mamaci kina da
sanin ki mai yasa kike haka? Ayanzu Umma
addu’a ki tafi bukata ba kuka ba. Ki sani duk
kaunan da kike mata Allah da ya karɓeta yafi
ki sonta ki yi hakuri addu’a zaki mata”.
Nasiha sosai ta mata mai ratsa zuciya.
A hankali Candy ta bar kukan sai sauke
zuciya take tana hawayen.
Bayan an kai Umma makwancinta na gsky.
Gida ya cika fam da yan gaisuwa.
Da yamma aka kawo abbincin sadaka kala-
kala Candy bata taɓa jin ta tsani cin abincin
gidan mutuwa ba sai yau. Tana zaune ta
hango fiskokin da bazata manta da su ba.
Wato *Ummu Abrar da Futha da Pherty* suka
shigo bayan sunyi gaisuwa suka nimi tabarma
suka zauna. Basu daɗe da zuwa ba Candy na
halkance da su taga sunyi gun kuloli nan
suka buɗe suka fara duba abinci har suka zo
kan wanda ya musu suka cika plate.
Take zuciyar Candy ya soma suya a rasuwan
Mahaifiyarta wasu suka zo cin shinkafan
gidam rasuwa. Asai daman haka ake jin idan
aka maka rasuwa kaga wasu ba dan Allah
suka zo ba? Bata idar da tunani ba taji
shewar su da sauri ta ɗago kai wasu ta gani
suna tsaye da su *Pherty,* *Futha* da
*Ummu Abrar* sunci kwaliya kamar masu
zuwa paty, sun daɗe suna hira kafin wayanda
suka shigo kafin suma suka je suka ɗau plate
suka ɗibi abincin suka nimi gu suka zauna.
Candy ɗaki ta koma ta barke da sabon kuka
lalle yau taji ɗacin da ake ji in an maka
wannan abun tabbas sai yau take dana sanin
zuwanta *GIDAN MAKOKI* da take yi yau
taga ilar abun da ciwonsa.
Washe gari bayan sun karya ta na zaune
Maman Munay ta liko ta ce“Candy wasu na
waje zasu miki ta’aziyya ki same su a zaure”.
Jiki ba kwari Candy ta mike ta fito daga gefe
ta ga wani ya haɗa kunu da kosai ga ɗan
wake a plate duk shi ɗaya ta wuce shi ta fita.
Wasu Malamansu na boko ne suka mata
gaisuwa tare da nasiha sosai. Kafin suka mata
sallama suka tafi ta mike zata shiga gida
kenan taji wannan bawan Allah wanda ya
ɗibo kunun nan ya ce“Alhamdulilah kai tun
da nake zuwa *ZAMAN MAKOKI* Ban taɓa
koshi irin na yau ba, aoohh!”. Yayi gyatsa
yana murmushi.
Sam bai ma lura da Candy ba. Laida sa ya
zaro daga aljuhu yafara juye kosan yana cewa
“kai amma Allah yasa wata ta kara mutuwa a
wannan gidan wani sati don na sake dawowa
na sha koko da kosai da kayan tea, da ɗan
wake haka nake so gsky *ZAMAN MAKOKI*
irin na wannan gidan a kwai daɗi……”.
Kasa karasa magar yayi sakamakon ganin
Candy tana hawaye a gabansa. Cikin ɓacin rai
ta fisge ledar zuciyarta na mata wani irin
suya.
Cikin kunar rai ta ce” amma tirrr! Da halinka
wannan halin ba mai kyau bane anya kana
tuna zaka mutu anya kana tsoron Allah
kuwa? Baka tunani kai ma akwai randa zaka
mutu a maka haka? Shin iyalanka zasu ji
daɗin in sunga hakan?”.
Hawaye ta share “kaicona ni Candy kasani da
bani da abunyi da ya wuce bin gidan mutuwa
don nayi *ZAMAN MAKOKI* don kawai naci
abincin mutuwa na koshi. Ni har gidan
Christer ina zuwa. Ban taɓa tunani ya zasuji
zafin abun, kunci ko ɗacin abun, sai jiya da
aka fara min na gani tabbas nayi nadama da
dana sani. Sai gashi kai har kana kara min
addu’a a gidan asake mutuwa”.
Wasu zafafan hawaye ta sake sharewa ta ci
gaba da cewa.
“Yau nayi nadama gami da danasani kuma
nayi alkawarin canza ɗabi’una. Bawan Allah
kaji tsoron Allah ka tuba ka dai na don in
baka gyara ba wataran zakayi danasani kamar
yanda nake yi yanzu”. Bata jira amsan sa ba
ta sa kai ta shiga gida.
Bawan Allah nan jikinsa duk yayi sanyi yana
mai-maita kalaman ta ya fita a zauren. Tare
da yin alkawarin daga yau ya bar wannan
halin.
A haka har akayi sadakan bakwai aka watse
Candy duk ta dawo shiru-shiru da ita bata son
yawan hayaniya sosai ko cikin sa’aninta in ta
zauna ita kaɗai sai dai kaji tana azukar ko ta
ɗauko al-qur’ani tana karatu. Rayuwa kenan
Candy ta dawo kamar ba ita ba ta bar zuwa ko
ina. Duk ta rame kulum tana cikin tunani, in
ta tuna abunda tayi a gidansu Mr Smile sai ta
zubar da hawaye gashi itama an mata. Ta
naso ta kirasa ta basa hakuri tarasa yanda
zata yi.
*BAYAN KWANA BIYU….*
Candy sai da ta nimi gidansu *Ummu Abrar
da Futha da Pherty* taje ta musu nasiha kan
zuwa *ZAMAN MAKOKI* wanda sai da suka
zubar da hawaye. Suka mata alkawarin sun
dai na zuwa. Tun ga ranar suka fara mutunci
suna kawo mata ziyara.
Haka rayuwan Candy ya kasance ita kaɗai a
gida. Maman Munay tayi-tayi ta koma gidansu
taki kasancewar makwabta suke hakan yasa
kulum suna tare da Munay.
******
Adeel duk yana cikin damuwa yana zaune a
Madina ne amma hankalinsa na 9ja gun
Candy Kulum bai da hiran da ya wuce na
Candy duk wanda yasan shi to zai san labarin
Candy. Hakan yasa Umman sa tana murna
tilon ɗanta ɗaya ya samu macen aure hakan
yasa tun bata bata ga Candy ba taji tana sonta.
*BAYAN WATA BIYAR…*
Muh’d(Adeel) ne kwance akan gadonsa.
Idonsa na kallon P.O.P dakin yana sana’arsa
na tunanin Candy. Sam ya kasa tsinana komai
bai da aiki sai tunanin Candy, wayar sa ne
yayi kara har ya tsinke bai ɗauka ba.
“mtssw ni fa bana son hayaniya shiyasa na
ma cire layin da aka sanni na saka sabo”.
Wayar ne ta sake kara kamar ba zai ɗauka ba
sai ya ɗaga number 9ja ya gani da sunan
Ahmad akan wayar. A hankali ya ɗaga wayar.
“Assalamu’alaikum”.
“Wa’alaikumusalam Adeel ina ka shiga ne
kwana biyu ina ne man wayarka?”.
“Hmmm!!”. Ya sauke gwaron numfashi.
“Ahmad ban son hayaniya ne tun da na bar
9ja na rasa Candy na rasa farin ciki na shiya
banson hayaniya”. Muh’d (Adeel) ya faɗa.
“Muh’d(Adeel) haba ya kake abu kaman bana
miji ba? Ko da yaushe ka kasance mai amsan
kaddara da hakuri. Kuma in har *Rabo ya
rantse* to ba makawa sai ka auri Candy. Ko
kamanta *Matar Mutum Kabarinsa* wani baya
taɓa auren matar wani. Na kai ina ta niman
number ka don in sanar maka da Candy ta
rabu da Abdoul wahab”.
Cikin razana mai ɗauke da farin ciki Adeel ya
ce.
“what?!! Mai kake son faɗa min ne? Kana
nufin cewar yanzu Candy basa tare da
Abdoul?”.
Ahmad ya ci gaba da cewa “eh sun daɗe da
rabuwa ga mahaifiyarta Allah ya mata
rasuwa”.
“Innalilahi wa inna ilaihi raji’un”. Abunda
Adeel yake nana tawa kenan.
“Adeel a yanzu Candy bata da kowa sai Allah
kuma yanzu ne ya kamata ka zo ka bayyana
kanka in da halima ayi muku aure da ita. Don
tana bukatar tai mako gaggawa”. Ahmad ya
faɗa.
“Allah ya jikanta ya mata rahma. Ahmad satin
nan zamu zo ni da Ummie na da Abbah na ayi
mai yiwuwa”.
“good haka za’ayi sai najika”. Cewan Ahmad.
“ok to nagode bye”.
Adeel da sauri ya tashi ya nufi falo nan ya
samu Ummie da Abbansa ba tare da ɓata
lokaci ba yasanarsu komai.
Abba ya nisa ya ce.
“dole mu fara shiri satin nan zamu 9ja in
Allah ya yarda ai *YAYA DA DUKOYA BA’A
KETARSU* koda ba sonta kake ba abun a tai
maka mata ne. Zamu iya kokarin mu ganin an
samo fangin iyayenta”.
Da farin ciki Adeel ya bar falon ya fara shiri
zuwa 9ja gun abar kaunarsa.
A satin su Abba suka gama shirya komai don
yau Alhamis jirginsu ya daga zuwa 9ja. Ko da
suka sauka a mai duguri garin su Abban
Adeel. Nan aka zo aka ɗaukesu bayan sun
huta suka ci abinci. Nan Abban Adeel ya
sanar ma danginsa akan gobe zasu Kaduna
aha ka kowa ya watse.
Washe gari suka bi jirgi sai garin Kaduna. Ko
da suka isa gidansu kanin baban Adeel suka
sauka. Abban Adeel ya sanar musu komai
basu dau lokaci ba suka je gun Baban munay.
Abban Adeel suka sanar masa da komai. Yayi
farin ciki ya ce.
“Yanzu ni ba zance komai ba in har yarinya
ta amince ba matsala ni zan tsaya mata har
ayi aure amatsayin mahaifinta”.
Godiya sukayi nan Abban Munay ya shiga
gida ya kira Candy. Ko da ta zo nasiha ya
mata sannan ya ce.
“Khadija wani bawan Allah ne yazo yana
sonki sunansa Adeel suna da zama a Madina.
Adeel ya dade yana sonki amma ya kasa gaya
miki. Har lokacin da yaji kinyi saurayi ya bar
kasan sabida ke. Sai daga baya yasamu
labarin komai har da rasuwan Ummanki
dalilin da yasa yazo kenan”. Ya karashe
maganan ya na kallon fiskan Candy.
“Khadija ina shawarta ki da kiyi amfani da
damanki don wannan masoyi ne na gaskiya
kuma kiyi kokari ki bi umar nin Ummanki
tace tanaso kiyi aure”.
Candy tana kuka tace“Abba na amince tunda
na san bazaka taɓa zaba min abunda zai cutar
dani ba”.
“Allah ya miki albarka”.
Ya mike ya sanar musu da ta amince ba
matsala. Na suka tsayar da maganan aure nan
da sati biyu. Kuma sun dau nayin komai
zasuyi sannan suna son ta dawo gidansu
Munay gaba daya da zama. Don za’a gyara
gidan tunda mallakinta ne.
Godiya Abban munay yayi sukayi sallama
suka tafi.
Adeel bai taba zuwa gun Candy ba itama bata
damu da tasan kowa ye mijinta ba.
Bayan kwana biyu za’a fara aikin gidan hakan
saya tasoma tattaro kayanta zata dawo
gidansu Munay. Wata akwati ta dauko a kasan
gadonsu duk tayi kura da tsatsa. Da har ta
barta, kawai sai taji tana son ta ga miye a
cikin a kwatin tayi ta balla kwadon ta kasa.
Sai da ta samo tabarya ta rinka dukan
akwatin ya balle. Da sauri ta buge wani
takarda ta gani da rubutu duk jirwayen ruwa
ya bata. Tana kara dago wasu photo ta gani
na Ummanta da wanda take tsammanin shine
mahai finta. Takardan tasoma warewa ta fara
karanta shi kamar haka.
*TAGWAYEN MARUBUTA*
[10:23PM, 9/24/2016] Rash Kardam:
*ZAMAN MAKOKI*
_Rash Kardam_
_Ummieluff_
*_Last page_*
Ni Ahmad Alkali hai fafen ɗan garin Sokoto ne
zamane ya kawo ni nan Kaduna. Amina
(sunan Ummin Candy) duk randa ki ka ga
wannan sakon ku tafi garin Sakoto unguwan
G.R.A gidan Malam Alkali. Sananne mutum ne
in kinje ki gabatar da kanki da abunda ke
cikinki ki gwada masa wannan photo zai gane
ku. Ni kam tawa ta kare ki rike min amanar
abunda ke cikinki ki kula da ita ki bata
tarbiya tamkar ina raye daga mijinki Ahmad
Alkali. Sai mun hadu a darusalam.
Hawaye da ya wanke wa Candy fuska na farin
cikin sanin danginta bata san lokacin da ta
ruga da gudu ta shiga gidan su Munay tana
kiran.
“Abba! Abba!! Abba!!!”.
Tana haki ta iso gabansa ta mika masa ta
kardan yana gama karanta wa ya saki
murmushi tare da fadin
“Allahu Akbar! Allah kenan mai yanda yaso
wato bai so Amina taga dangin mijinta ba sai
yarta kuma bayan ranta. Tabbas ba sanya
yanzu zan sanar da iyayen Adeel a sati nanna
zamu tafi”.
Waya ya kira ya sanar musu da komai.
Cikin murna suka ce a jibi zasu wuce in Allah
ya yarda.
Bayan kwana biyu Abban Adeel da kansa ya
sama musu motoci biyu daya shiga Ummie da
sirkanta tana rike da hannuta dayan kuma
Baban Munay da Mamanta da Munay.
Ko da suka isa Sokoto basu sha walaha ba
suka samu gidan tabbas babban gida ne suna
zuwa suka bukaci ganin Alhaji Alkali suka
sanar masa da komai.
Yan uwa suka hadu masu kuka nayi masu
murna nayi Alhaji Alkali yana rike da hannu
jikarsa. Ya kuma yi na’am da auren yace a
garin Sokoto za’a daura nan yace a ci gaba da
shirin biki.
*WAYE ALHAJI ALKALI*
A Alkali haifafen dan garin Sokoto ne babban
alkali ne. Yana da yara biyar Fatima ita ce
babban yarsa tana Auren Soja wanda suke
kiranta da *(Mrs Umar Soja)* Sai kuma Saeed
da ke aiki a Bebeji suna kiransa da *(Ya
Saeed Bebeji).* sai Abdol-raheem da ke aiki a
jega suna kiransa da *(Ya raheem jega)*.
Tukunna *Ahmad* (Baban Candy). Sai
auntansu Lubabatu tana aure a kano.
Sun kasance su kaunar junansu. Rana daya
aka nimi Ahmad aka rasa ya fita fatauci sun
shiga kunci da damuwa tun suna zuba ido har
suka hakura. Wannan shine takaitacen
tarihinsu.
Duk wani shiri ya kan kama saura kwana
biyu biki.
Adeel sun kawo lefe na gani na fada kowa ya
gani sai ya yaba.
Alhaji Alkali walima kawai ya yarda ayi shi.
Ranar jumma’a bayan sallah jumma’a dubban
mutane suka shaida aure Muh’d (Adeel) Aliyu
Yahaya da Khadija(Candy) Ahmad Alkali.
Akan sadaki dubu dari haka taro ya watse.
Da yamma Candy tayi walima wanda ya
hallaci mutane da dama kuma akayi nasiha
mai tsuma zuciya.
Bayan gama walima iyayenta suka mata
nasiha suka bi jirgi zuwa Kaduna don a gun
Adeel ya gina gidan da zasu zauna. Gida ne
mai kyau sosai gwanin burgewa. Su Candy da
Auta suka zauna sai da amgwaye suka zo.
Nasiha sosai suka musu kafin suka tafi.
Adeel ya taso a hankali yazo kusa da Candy
cikin salon kauna ya ce “Amarya ba kya laifi”.
Har kwanyanta taji muryan kuma akwai ida
tasan muryan amma ta rasa ganewa ga nauyin
da take ji bare ta dago ta gansa.
A hankali ya yaye gyalen tare da tallabo
habarta ya ce “Khadija dago kiga mijinki”.
Cikin sauri ta dago wata zata gani Malam
Muh’d ido ta murtsuke ko idonta ke mata
gizo. Ja da baya ta fara tana hawaye.
Adeel ya sauka kasa ya saka gwuiwarsa a kasa
ya fara bata hakuri yana fada mata irin
kaunar da ke mata tun haduwarsu. Sam yaki
kulasa jiki ba kwari ya koma dakinsa.
Sannu a hankali Adeel ya soma koya ma
Candy soshi har suka shaku sosai. Wanda har
sukan iya zama gu daya suka kwana a gado
daya.
Zaune suke kamar yanda zuka saba cikin
dabara da salo Adeel ya soma shafata yana
sarrafata ganin kujera ya kasa musu ya daga
ta sai gado a hankali ya soma zame mata
kayan jikinta. Ganin haka muka bar dakin da
sauri. Amatsayin mu na surkai….lol..
Washe gari Adeel shi ya gyara ko ina ya hada
musu abun karyawa kar kuso kuga ta rairaya
da kauna a gun Adeel da Candy.
******
*BAYAN SHEKARA HUDU*
Adeel na hango da Candy tana rike da hannu
wata yarinya wanda kamanta sak na Adeel,
yarinya mai kyau da ita. Sun sauka a kofar
wani gidan da akayi rasuwa Candy ta shiga
ciki bayan tayi ta’aziya nan ta hango masu
halin irin nata a da, gunsu ta nufa ta soma
musu nasiha sosai ta ciro kudi mai yawa ta
basu ta fito ta tafi gidan su Munay suka je
suka gaida Maman Munay da Babanta nan ma
Alheri sosai suka musu daga nan suka shiga
gidan Hajiya ta gaida ta ta mata alheri suka
tafi. A mota Adeel ya ce“My Candy wai yaushe
za’ayi ma Khairat kanwa ne ko Kani?”.
Ido Candy ta juya ta ce“oh Abban khairat da
wuri haka yaushe aka yaye ta”.
Murmushi yayi “gaskiya ina ga zan kara kai
mi don ina son ganin yara na da yawa dan
haka yau ki shiya duk dare sau shida zanna
duty”.
Ido ta zaro ta marairaice fiska “wayyo Abban
khairat ina zan iya shida fa”.
Dariya yayi sosai yace“kaga raguwa kawai”.
Itama dariyan tayi.
*ALHAMDULILAHI*
Nan muka kawo karshen wannan littafi mai
suna *ZAMAN MAKOKI* kuskuren da ke ciki
Allah ka yafe mana amin.
*TSOKACI*
Wannan labarin ba wai mun yi shi da ni
shadantarwa bane ka dai a’a akwai sakon da
mukae son mu isar. Kusani yan uwa yanzu
mafi yawanci badan Allah ake zuwa *ZAMAN
MAKOKI* ba, sai dan su je cin abinci ko su
saka zani mai tsada suna gasa ko gasan kawo
abinci mai yawa da kyau. Wanda hakan
haramun ne ko mai mutum zai yi yayi domin
Allah. Dan Allah masu wannan halin kuji
tsoron Allah ku dai na kunga yanda ya faru da
Candy a wannan labari ya Allah ka bamu ikon
gyarawa amin.
*SADAUKARWA*
Wannan littafin sadaukarwa ne gareka ɗan
mu abin kaunar mu ɗa ɗaya tilo ga
*Ummieluff* wato mai suna *MUH’D* *_
(Adeel)_* Allah ya raya mana kai bisa sunnan
Annabi mu. Ya Allah ka albarkace shi da
sauran ya ramu amin.
*TUKWUICI*
Wannan Littafin tukwuici ne gare ku:
Sanah I .S Matazu
Maryam Alkali(Mamu)
Khadija Ahmad Alkali(Candy Uwa ta gari)
Kausar Luv
Ummu Abdoul
Autar Hajiya
Munay
Futha
Aneesa Abubakar Rimi
Aisha Mazoji
Saeed Bebeji
Abdoul-wahab(Mr Smile)
Abdoul Raheem Jega
Aneesa (Anush)
Ummu Abrar
Aisha Muh’d(Maman Abdoul shakur)
Mrs Umar Soja
Haneefa Usman
Manshat
Afreen
Zee Maman Khady
Khdeey
Maryam garba
Simbielurv
Bintu zaif
Serdieylurv
Nuceeluff
Memie bee
Queen Memie
Zahrah BB
Mesha Luv
Ummi Aisha
Lubee Mai tafsir
Miss Hafsy
Mrs Saif
Rabee’at Sk mash
Fancy (mrs sadiq)
*GAISUWA TA MUSAMMAN*
Ga dukkan online hausa writers.
*GODIYA GA GROUPS*
MAMAN ADNAN HAUSA NOVELS
RASH KARDAM HAUSA NOVELS 1,2,3
DAN DALIN LUBIEE MAI TAFSIR
FENNAT NOVEL
MAMU NOVELS
DUNIYAR LITTAFI
HAUSA NOVELS
DUNIYAR MAKARANTA
KHALEESAT HAIYDAR NOVELS F/B
ANEE NOVELS
DAN DALIN AUTAR HAJIYA
RAI DANGIN GORO
MRS SHAMSUR NOVELS
DA SAURAN WAYANDA BAMU AMBATO BA
AMANA AFUWA. KUNA RAMMU KUMA MUNA
KAUNAR KU.
WRITERS WORLD ASS
SIMBIELURV NOVELS
*UMMIELUFF*
*RASH KARDAM*
Ku ka sance dani a sabon littafina mai suna
*TAR KON KAUNA* yana nan tafe ba da
jimawa ba.
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top