Zamanin ƙaƙaba ƴan takara ya wuce, zaɓen Anambra darasi ne ga APC- Kawu Sumaila

 Zamanin ƙaƙaba ƴan takara ya wuce, zaɓen Anambra darasi ne ga APC- Kawu Sumaila

Tsohon hadimin Shugaban Ƙasa kan harkokin majalisa, Abdurrahman Kawu- Sumaila ya baiyana cewa zamanin ƙaƙaba ƴan takara a siyasar Nijeriya ya wuce.

Kawu-Sumaila ya kuma baiyana cewa ya kamata jam’iya mai mulki, APC ta ɗauki darasi a kan zaɓen gwamna na Anambra, inda ɗan takarar jam’iyar APGA, Charles Soludo ya lashe zaɓen.

Kawu-Sumaila ya yi wannan kira ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Asabar.

A saƙon da ya wallafa, tsohon wakilin Takai da Sumaila a majalisar wakilai ta tarayya ya ce shi bai damu da zaɓen fidda gwani na ƴar-tinƙe ko akasin hakan a APC.

“Ni ban damu da zaɓen fidda gwani na ƴar-tinƙe ko akasin hakan a APC ba. Amma dai, ya kamata mu faɗawa kan mu gaskiya. Zamanin ƙaƙaba ƴan takara ya wuce. Zaɓen Anambra dai ya kamata ya zame mana izina,” in ji Kawu-Sumaila

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top