Dr. Mansur Sokoto yayi kira zuwaga Masu Ruwa da Tsaki dasu Umurci Limamai domin Gudanar da Kunuti a masallatai domin samun saukin Matsalolin Tsaro
Dr. Mansur Sokoto |
Dr. Mansur yakara da cewa
” Qunutun Nawázil
A irin wannan lokaci da jinainanmu da dukiyoyinmu da mutuncinmu suka rasa daraja, aka mayar da kisan jama’a ba komai ba, satar su domin neman kudin fansa kamar halastaccen abu, cin zarafin iyalan jama’a da kona dukiyoyinsu suka zama kamar ba komai ba. Ba mu tsira a titi ba, ba mu tsira a gida ba. A irin wannan yanayi ne aka shar’anta yin kunuti a cikin sallolin farilla.
Lallai ne shugabannin Musulmi; mai Alfarma Sarkin Musulmi da shugabannin manyan kungiyoyin addini su umurci limamai a dukufa ga yin “Qunutun Nawázil” a cikin sallolin farilla.
Zamu yi bayanin yadda ake yin wannan Qunuti in Allah ya so.
Check Also this out
How To Apply For CBN’s 5 Billion 100 for 100 PPP Loan For Business People 2021/2022
Ku dakace mu.”
You may also like
Muna goyon bayan wannan Kira na Dr. Mansur Sokoto da fatar Allah ya kawo mana sauki a Arwwacin Nigeria, Nigeria, AFRICA dama Duniya baki daya.