YADDA ZAKA IYA JUYA KATIN DAKE LAYIN WAYARKA ZUWA KUDI, KAKUMA TURA ZUWA BANKINKA

 YADDA ZAKA IYA JUYA KATIN DAKE LAYIN WAYARKA ZUWA KUDI, KAKUMA TURA ZUWA BANKINKA

Sau da yawa mutane suna samun kyautar katin waya daga

wajen abokai ko ‘yan’uwa amma sai suyi ta faman neman

wanda zai siya amma su rasa.

Wasu kuma suna samun katin waya ne ta hanyar amfani da

wasu manhajoji na waya (phone application) irinsu (Share it)

(JumiaPay) da sauransu, wa’danda suke bada kyautar katin

waya idan aka saukesu akan waya (install) ko kuma idan anyi

wani aiki da sukace ayi (task), amma sai su gaza samun mai

siyan katin a cikin sauƙi.

Check this also

Four Steps to Receiving N5000 for the previous 6 months under a cash transfer program under the guidance of the Federal Government RRR (Rapid Response Register)

Sannan kuma mafi yawan hanyoyin da ake mayar da katin

waya zuwa ku’di anayin transfer ‘dinshi ne kafin kuma ka jira a

saka maka shi a cikin asusunka (wallet), wani lokaci yakan

dauki tsawon lokaci kafin ku’din su shigo maka kamar yadda

(DataWay) sukeyi, kuma sai wanda yake da register dasu yake

samun damar yin hakan ma.

Check this also

An Sake Bude portal Na Daukar ‘Yan Sanda (Police) Duba Wadannan Muhimman Abubuwa Guda 11 Kafin Ka Cike Dakuma yadda Zakuyi Kucike

To ita wannan hanyar da zan nuna maku duk ba haka take ba,

tana da sauki kuma kai tsaye ku’dinka zasu shigo cikin asusun

bankin ka.

Da farko dai zaka shiga wannan link dake kasa ka dauko wani app mai suna “TINGTEL AIRTIME”.

https://play.google.com/store/apps/details?id=tingtel.android

Bayan ka saukeshi akan wayar sai ka bu’deshi, kafin ka fara

komai sai ka tabbata kasan lamabar sirrinka ta transfer a

layinka wanda kake da ku’din a ciki, kuma ka tabbata yana

akan saman wayar da ka sauke manhajar (app) ‘din.

MTN suna saita lambar sirrin transfer ne kamar haka: idan

baka ta6a yiba zaka danna *600 * 0000 * sabon lambar da

kakeso * sai ka Æ™ara maimata ita lambar da ka za6a ‘din #, sai

ka danna wajen kira.

Su kuma Airtel zaka iya shiga ta cikin saitin “Sim Tookit” saika

saita shi.

Hanyoyin da zaka bi wajen saita manhajarka na “TINGTEL”

sune:

Gida na farko idan ka shiga zasu tambayeka yare, wanda zaka

barshi akan “English” sai ka danna “continue”

Gida na biyu shine wajen da zasu tambayeka.

First name, last name sai username daga nan sai “promotion

code” shi kuma za6i ne, zaka iya barinshi karka saka komai,

daga nan sai ka danna “signup”

Gida na gaba kuma zasu ce maka ka saka “code” guda hudu

na sirri wanda zaka kiyaye account ‘dinka dashi, idan ka danna

“set passcode” zasu ce ka kara danna su lambobin da ka saka

a baya, sai ka kara danna su, wato kayi “verify” kenan.

Gida na gaba shine wanda zakayi register na layin da zaka

dunga tura ku’di dashi zuwa asusunka na banki “bank

account”, zasu tambayeka kasa lambar layinka na gidan sim

na farko (sim one) bayan ka gama idan kana buƙatar kayi ma

layinka na biyu shima zaka iya, idan kaso kuma zaka iya

wucewa gaba idan ka danna “skip”, zasu turo maka wasu

lambobi a layinka wanda kayi ma register da app ‘din, idan ka

saka lambobin shike nan ka gama.

Bayan ka gama komai zai bude maka wasu za6uka (options)

anan kuma sai kaje wajen “airtime sell” idan ya wuce zai nuna

maka wani waje da aka rubuta “credit to” ananne zaka saka

lambar bankin da kakeso ka tura ku’din naka, sannan kuma

sunan bankin, daga nan su da kansu zasu bayyana maka sunan

mai asusun bankin da kasa lambar bankin, sai ka danna “next”.

Idan layukan da suke cikin wayarka biyu ne, sai ka za6i wanda

ku’din suke ciki zaka tura, bayan ka za6a sai ka saka adadin

ku’din katin da kakeson su tura maka a matsayin ku’di cikin

bankin ka, ananma zasu nuna maka iya ku’din da su kuma zasu

chajeka a matsayin aikin da za suyi maka, nan ma bayan ka

gani idan ka amince sai ka danna wajen da aka rubuta

“transfer”.

Daga Æ™arshe zasu tambayeka “pin” wanda shine kadai abunda

ya rage maka, wannan shine “pin” naka na layinka wanda kake

transfer dashi, da zaran ka saka shi kuma sai ka sake danna

inda aka rubuta “transfer” shikenan zaka ji ku’dinka sun sauka

cikin asusun bankinka.

Check this also

Ma’aikatar Ilimi Ta Tarayya Ta BuÉ—e Shafin Cike Tallafin Karatu Na Bangarorin Ilimin Yarjejeniyar [Bilateral EducationAgreement (BEA)] Zuwa Ƙasashen Russia,Morocco, Hungary, Egypt, China, Serbia da Romania

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top