CIBIYAR FASAHA TA ƘASA ƘARƘASHIN MA’AIKATAR SADARWA TA FITO DA SHIRIN ƘINƘISHE SABBIN FASAHOHIN KASUWANCI

 CIBIYAR FASAHA TA ƘASA ƘARƘASHIN MA’AIKATAR SADARWA TA FITO DA SHIRIN ƘINƘISHE SABBIN FASAHOHIN KASUWANCI:-

Agajahub publisher sunazo mukuda bayani akan sabon Gurbin Aiki daga CIBIYAR FASAHA TA ƘASA ƘARƘASHIN MA’AIKATAR SADARWA TA FITO DA SHIRIN ƘINƘISHE SABBIN FASAHOHIN KASUWANCI:-

Cibiyar nazari da ƙere-ƙeren kayan fasaha da samar da na’urori masu ɗabi’un ɗan adam, (NCAIR), ƙarƙashin hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ƙarƙashin jagorancin ma’aikatar sadarwa da tattalin arziƙin fasahar zamani, da haɗin gwiwar ma’aikatar alaƙar ƙasa da ƙasa ta ƙasar Japan, (JICA), sun fito da shirin ba da horo na tsawon watanni biyar domin horar da masu basira dabarun ƙinƙishe sabbin fasahohin fasahar zamani kan harkokin kasuwanci a Nageriya.

Waɗanda su ka cancanta su nemi shiga cikin wannan shiri su ne kamar haka:-

1. Duk wanda ya cika shekaru (18) a duniya, daga kowane fanni na: ƙere-ƙeren fasahohin noma na zamani da na lafiya da sauransu.

2. Duk wata/wani shi kaɗai, ko a ƙungiyance, waɗanda su ke da shiri da tsarin gudanar da kasuwancin ƙere-ƙeren fasahar zamani, ko su ke da wani abu na fiƙira da su ka samar wanda zai taimaki bunƙasar tattalin arziƙin Nageriya.

3. Duk wata/wani, su kaɗai ko a ƙungiyance waɗanda su ke da burin samar da wani kamfani a hukumance domin fara gudanar da harkokinsu na kasuwanci a tarayyar Nageriya.

Fa’idar da ke ƙunshe cikin shirin ga jama’a:-

1. Samun horon cigaba a zahiri da kuma ta hanyoyin sadarwa na zamani (Online). 

2. Samun wuri gami da damar aikin haɗin gwiwa a cibiyar ƙere-ƙeren fasaha ta ƙasa.

3. Samun jagoranci da nusarwa daga ƙwararrun masana kan fasahar zamani. 

Read this also

4. Samun dama kan harkokin yanar gizo-gizo.

5. Samun damar gano ɓoyayyun damammakin da mutum bai sani ba kafin shiga cikin shirin.

Waɗanda duk su ka cika wɗannan sharuɗa da aka zayyana a sama, za su iya neman shiga cikin wannan shiri ta hanyar shiga cikin wannan mahaɗa, (Link): https://ncair.nitda.gov.ng/?page_id=3613.

Za a rufe karɓan bayanan masu neman shiga cikin shirin a ƙarshen wannan wata na Janairu. Idan Allah Ya kaimu. Allah Ya ba da sa’a. Amin.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top