HIRAR WATA MA’ABUCIYAR SOYAYYA

HIRAR WATA MA’ABUCIYAR SOYAYYA

HIRAR WATA MA’ABUCIYAR SOYAYYA

Mako biyu da suka gaba ta ne na samu zantawa da wasu daga cikin Masoya inda suka fayyace yanda rayuwar soyayyarsu ta kasance. A yau ma jagorar shafin MUHIEBERT INDIA ta ci karo da daya daga cikin Hadaddun Masoya MUNAYA ADO wadda ta fayyace gwagwarmayar da ta sha cikin Soyayya, ga yadda hirar ta kasance:

Barkanki da kasancewa a wannan shafi na Soyayya da shakuwa.

Yauwa barka kadai

Da farko za mu so mu ji cikakken sunan ki da kuma takaitaccen tarihinki

To ni dai sunana Maimuna Ado Hassan wadda aka fi sani damunaya), An haife ni a unguwar Yakasai da ke cikin birnin Kano. Na yi firamare dina a Crown Science and Commercial Collage, sannan na yi sakandire a Pragmatic Collage da ke Dan’agundi. Yanzu haka ina Northwest Unibersity da ke cikin birni da kewaye.

Da kyau! Munaya, Shin malama Munaya kin taba yin soyayya?

Eh! Na taba yi.

Za ki kamar shekara na wa da fara yin soyayyar?

Eh! zan kai shekara hudu

Da kyau! Da samari nawa kika fara soyayya ko kuma kike soyayya da su?

Read this also

Da guda daya ne

Shin kin taba fuskantar kalubale cikin soyayya?

Eh! sosai ma na fuskanci kalubale sosai

Ko za ki iya fadawa masu karatu irin kalubalen da kika fuskanta?

Kalaman soyayya masu dadi na 2022

To da farko kalubalen da na fuskata shi ne, mun fara soyayya da shi ya nunan so ni ma kuma na nuna masa na yarda da shi sosai kuma na saba da shi sosai ina, ganin a lokacin ba zan iya rabuwa da shi ba, kwatsam lokaci daya na ga ya canzan ba tare da wani daliliba ya daina kirana a waya ya daina zuwa gidanmu kuma ni wallahi ban san me na yi masa ba a lokacin haka na dau waya na kira shi kuma zai daga mu yi hira sosai amma fa shi ba zai kira ni ba ni kuma a lokacin ina sonsa sosai ba na ganin laifinsa ko na ce ba zan kara kiransa ba sai na kasa. Haka dai muka ci gaba da yi har dai ni ma na gaji na dai na kiransa amma still, duk da haka ina son shi don wani lokacin in na tuno shi nakan shiga cikin damuwa sai kuma daga karshe da na dage da addu’a sai Allah ya yaye min ya kuma kawon wani mai kauna ta.

Toh! Ya ya za ki kwatanta irin damuwar da kika shiga a lokacin da kika tsinci kanki cikin rashinsa, lokacin da kike ba shi kulawa shi ba ya ba ki?

E! to, na shiga damuwa sosai don a lokacin har ramewa sai da na yi bana iya bacci ba na iya cin abinci sosai saboda ba karamin so nake mai kuma a lokacin zan ji an ce ai yanzu wane wance yake so sai in ji ba dadi sosai kuma abin takaici sai ya je yarinka cewa ni na yaudare shi.

Lallai kin sha fama a soyayya, ya kuma bayan da kika rabu da shi wanne irin damuwa kika shiga?

Eh! na shiga damuwa kuma soyayyarsa tana nan cikin zuciya ta ba ta ragu ba sai karuwa da ta yi kuma da yake dama a lokacin da mu ke tare da shi akwai wadanda suke so na to soyayyar wannan din ce ta hana ni kuka, to a lokacin ne kuma suma suka samu damar nuna bajintarsu tun ba na kula su saboda a lokacin ina ganin ba zan kara soyayya ba. Har dai na cire damuwa a raina na fauwalawa Allah shi ne nake kula su to a cikinsu ne na samu wanda ya fi wannan sona,tun da dama an ce mahakurci mawadaci

Haka ne! Yanzu idan na fuskance ki kina nufin ki ce kin samu wani madadin wancan?

E! sosai ma don sai yanzu nake ganin wace kaddara ce ta sa na kula shi saboda shi ba wa ba ya kauce wa kaddararsa amma wannan da nake tare da shi shi ne wanda Allah ya zabar min shi ne Alkhairina.

Masha’allah! Wanne irin farin ciki kika taba fuskata da ita cikin soyayyarki tsakanin wancen masoyin naki da shi wannan sabon da kuke tare?

Sakonnin soyayya masu dadi

To farin cikin da na fuskanta a tsakanina dayan shi ne a lokacin da muke tare ya nunan so sosai kuma ya nuna ni kadai yake so to a lokacin ni kuma nakan tsinci kaina cikin farin ciki inna tuno ni fa yake so,shi kuma wanda da muke tare da shi yanzu farin cikin da na fuskanta tare da shi wallahi ba zai misaltu ba.

Da kyau! Wanne abu kika fi so a cikin soyayya?

Eh! to ni kam a soyayya ina son kulawa sosai kuma ba na so a hada sona da wata kuma ina so ka daraja dangina.

Me ya fi bata miki rai a soyayya?

Yaudara da rashin gaskiya da kuma rashin ganin girman juna.

Mene ne burinki game da soyayya?

To burina a soyayya shi ne idan aka fara soyayya ya kasance an auri juna wannan shi ne burina a soyayya

Gaskiya ne, mu je ga tambaya ta gaba wanne irin Namiji kike son aura?

To da farko dai ina son namiji wanda yake da ilmin boko da na addini,sannan mai tarbiyya wanda ya san mutuncina da kuma na iyayena, kuma dan dattawa kuma wanda zai rike ni amana ba don komai ba ko don tarbiyar yarana.

Masha’allah! Wanne irin Namiji ne kuma ba ki son aura?

Namiji jahili namiji mara kamun kai namijin da ba ya ganin girman kowa.

Wane shawarwari za ki ba wa masoya?

To ni dai shawarar da zan bayar shi ne kawai a yi soyayya don Allah ban da son zuciya da kuma a rinka ganin girman juna.

Da fatan masoyan sun ji kuma za su yi amfani da abin da kika fada, a gurguje su wa za ki gaisar?

To da farko dai ina gaida Nusaiba, akwai my bestie princess, akwai Muhibbah Ahmad ibraheem, akwai Aysha briged, sai Kannena duka ina gaishe su.

Munaya muna godiya da fatan za a ci gaba da soyayya ingantacciya.

Insha’allah ni ma na gode.

Wannan ita ce tattaunawar da na yi tare da Munaya inda muka ji irin kalubalen da ta fuskanta cikin Soyyarta.

Ku kasance tare da ni a mako mai zuwa domin jin da me zan tawo muku da shi.

Sanfuran Kalaman Soyayya

Masoyi in ina ganinka sai na runka jin wani farin ciki mara misaltuwa yana zaga ko’ina cikin zuciya ta, Ji nake tamkar babu mai jin wani farin ciki a duniya sama da ni. Saboda kasancewna da kai, A kullum nakan tsara fasalinka da kallonka da murmushinka amma fa duk da idanuwana yayin dana bude sai na ga kana mun gizau tamkar kana tsaye a gabana.

Ashe ba ni daya ba, In ina tare dake mantawa nake da kaina ma balle na kusa dani, tsabar farin ciki mantawa nake da wani abu bakin cik.

Ai ni tuni mun yi hannun riga da wani bakin ciki sabida kasancewarka tare da ni Ina alfahari da zamowa ta taka wadda ta take sauran ‘yan matan da suke rubibin zamowa naka, na zama ni day kwal gare ka.

Labaran soyayya masu dadi

Sufar ki zanariya ce a idanuwana irin zanen dutsin nan da ba batun gogewa, Nakan zama kamar zautace a duk sanda na ke ba dan mutane sai su zata ni kadai nake magana. Alhalin kuma a duk sanda na shiga irin wannan yanayi ke nake gani zaune gabana muna hira kina sakar mun tausasan murmushi masu mantar dani inda nake,

Ina so ka sani komai nawa naka ne, kallo na nakane, murmushina naka ne, duk wani motsina naka ne dan babu wanda ya dace na mallakawa su face kai daya. Ka kan dada sani nishadi a duk sanda naji kalamanka dan babu irinsu, godiya nake ga Allah daya mallakamana zukatan junan mu ina alfahari da kasancewar mu tare da juna.

Na tabbata ni nayi tsuntuwar soyayya, wacce nasan cewa ba azanci da dabara na ne suka ban ba. Ke kyauta ce daga Allah, Ki gode wa Allah don ya ba ki bàbbàr baiwa ta sarrafa zuciyoyin ba iya na maza ba har matan ba.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top