Kalaman Soyayya Masu Ratsa Zuciyar da Sanyaya Zuciya 2022

 Kalaman Soyayya Masu Ratsa Zuciyar Masoya da Sanya Zuciya

.

Amincin allah ya tabbata gareka masoyina kana Raina❤️❤️
💙💙💙💙💙💙
Sallama mai dauke da karuwar imani ya tabbata gareka rabin Raina🌹🌹
💐🌹🥀🌷🌺🌸🏵️☘️
Kullum tambarin sonka dukawa yake a masarautar ruhina tare da sake sabon dammara cigaba da tafiya cikin soyayyarka mara fashi annurin raina 🌺🥀
☘️☘️☘️☘️🌹🌹
Kakasance na musamman acikin mazaje wanda zuciya ta zabeka acikin ma zaje na musamman 💜💜
💜💜💜💜
Zuciya ta baka yarda da amincin ruhi fatan kana cikin koshin lafiya da wadatar zuci jarumina ❤️❤️
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

Read this also

Soyayyarka tayi ambaliya a masarautar zuciyata taho cikin sauri dan kamin agajin gaggawa muradin raina 🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷
Kaine likitan da dae iya warkar dani da ga matsanacin rashin ganinka kusa dani ina zaman jiranka jarumin jarumai kuma farin cikin zuciyata 💐💐
💐💐💐💐💐
Shi yasa koda yaushe tsananin kaunarka yake ta ta tsiri a kaina hakan yasa kullum farashi sonka yake ta hawa a cikin zuciyata ☘️☘️
☘️☘️☘️
Murmushinka yana sakani farin ciki da annushuwa 🌸🌸
🌸🌸🌸
Ganinka yana sakani farin ciki mara adadi kana da kyau kana da tsafta gashigar alfarma wadda zuciya ke so❤️❤️
❤️❤️❤️❤️❤️❤️
Kana matukar burge idanuwana da zankadediyar kealliyarka jarumina 🏵️🏵️
🏵️🏵️🏵️🏵️🏵️
Ni takace har abadan abada 🌸☘️🥀
KAHUTA LAFiYA FARIN CIKIN RAYUWATA 🌹☘️🌸🏵️❤️💐🌷💜🌹🌺💙🌷💜🌹🌸☘️
                            SHIRIN
               ✉WASIKAR MASOYA✉
           _____________________
                          [015]
   Barkanmu da kasancewa a cikin wannan shiri mai albarka. 
Shirin da yake kawo muku ZAFAFAN WASIKUN SOYAYYA da martaninsu. Wasikar neman soyayya, na neman yafiya da kuma na jaddada soyayya. Ku kasance tare da ni Ridwan a duk irin wannan rana ta Alhamis, na gode.
Wasikarmu ta yau za muji yanda Safwan ya rubuta sakon soyayya ga abokiyar karatunsa Ummul-Khairi.
ASSALAM ALAIKI WA RAHMATULLAH.
UMMUL-KHAIRI.
      Da fatan kina cikin koshin lafiya tare da kyakkyawan yanayi na farin ciki, Allah Yasa haka amin.
Kiyi hakuri daga zantukana a kanki, ina cikin wani yanayine da dolena na furta hakan gareki, duk da cewa kila kin taba ji daga wani bangaren. A cikin wannan tunanin zan bayyana sirrikan zuciyata ga mafi soyuwar cikinta.
Ummul-Khairi ba tare da neman izini ko jin ra’ayina ba, ganin farko da idanuwa sukayi a kanki zuciyata ta harbu da tsanrsar kaunarki lokaci guda. Dukkannin hankali da nutsuwata take suka karkata zuwa ga kyakkyawar fuskarki wacce ke cike da haiba, kamala da kwarjini, a sa’innan dukkannin burikana na nemesu na rasa, sanadin shigowar burin mallakarki. A tsawon lokacin zuwa yanzu babu abin da yake kai-ka-kawo a zuciyar tawa face zallar tunaninki dare da rana.
Babu alamun dakatawar soyayyarki a zuciyata domin kullum kara tasiri yake a gareni, hatta a mafarkaina ina yawan mafarkinki a mabambancin lokuta. Gaba ɗaya dai ina cikin kaunarki Ummul-Khairi.
Ban sani ba ko kin fuskanci hakan, amma ina yawan nuna miki a lokutan karatunmu. Koma dai meye a yanzu kin ji daga gareni. Ina fatan jin kyakkyawan martani wanda zuciyata za tayi farin ciki da shi Ummu. Sannan zanyi uziri gareki idan har wani ya rigani mallakar zuciyarki.
Ki huta lafiya.
Safwan Ibrahim.
___________________________________
                   MARTANI
___________________________________
Assalamu alaika wa rahmatullah.
SAFWAN.
  Ina cikin koshin lafiya, da fatan kaima haka, Allah Ya tabbatar da hakan, amin.
Hakika ita kalmar so ko a bakin makiyi tana da daɗi, sannan abu mafi soyuwa shi ne ka mayar da martani cikin kyakkywar siga ba tare da muzantawa ga wanda ya furtama kalmar so ba. Duk hakan mutumta mutumne da kalmar da ya furta ta soyayya. Dan haka ba sai ka bayar da hakuri gareni yayin furta kana sona ba.
Safwan na ji daɗin sakonka, kuma nayi farin ciki dashi. Tuntuni na fuskanci yanayinka gareni saidai ban tabbatar da cewa neman soyayyata kake ba sai a yanzu. Duk da cewa ka furtamin amma ina mai baka shawarar ka daina zurfin ciki a soyayya hakan cutar da kai ne.
Ka cancanci zama masoyi Safwan dan haka ina ji a jikina na gamsu da sakonka. Sai dai kada kayi amfani da zaman tarenmu ka cutar da ni. Ka sani babu kyau yaudara, kada ka aikata ga wani domin zai dawo gareka.
Zan jirayi karin bayani idan mun haɗu, na gode.
Ummul-Khairi Junaid.
Anan shirin namu ya zo karshe, sai wani satin idan Allah Ya kaimu.
Ku aje tambaya ko neman shawara a soyayya cikin tsari da ma’ana, na gode.
Aradu sanyi ya hanani posting da wuri.

.
                            GAREKU MASOYA
Wacce kalma ce tafi bakanta rai anan ?
1. Dama bani nace ina sonka ba kai kace kana sona.
2. Dama ai ni ba sonka nake ba kawai kudinka nake ci.
3. Dama ai ni dawasa nace ina sonka sonka bai kai zuciba.
4. Nifa ina da wanda nake so.
5. Da can ban taba sonkaba.
6. Allah ya hada kowa da rabon sa.
7. Nifa anyi min miji.
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top