Kalaman Soyayya Masu Ratsa Zuciyar Masoya na Wannan Shekarar 2022
WASIKA
❤️❤️
Rubutattun Sakonnine Daga Dausayin Zuciyata Zuwaga Malamar Zuciyar Dake Shayar Dani Zumar Shauki Da Annashuwar Farin Ciki Da Jindadi
❤️❤️Cikakkiyar Sallama Irin Ta Addinin Musulunci Daga Zuciyar Dake Rayuwa Tana Kara Shiga Cikin Fadar Sonki
❤️❤️
Read this also
Hakika Haske Annurin Fuskarki Bai Gushe Ba Face Yayi Awon Gaba Da Dukkan Wani Kuzarin Dake Jikina
❤️❤️
Aminci Agareki Ya Sarauniya Mai Kyakkyawar Sura Da Cikakkiyar Nutsuwar Sautin Zance Wanda Ke Fita Tamkar Busa Irin Na Sarewa
❤️❤️
Matsayin Girman Daraja Biyayyar Da Zuciyata Takewa Kaunarki Tawuce Adadin Busawar Iska Cikin Adadin Tafiyar Kwanakin Numfashi Na
❤️❤️
Ina Mika Sakon So Daga Zuciyata Zuwaga Zuciyar Danake Neman Hada Zumunci Wanda Muke Fatan Kasantuwa Har Zuwa Karshen Rayuwar Numfashi
❤️❤️
Ya Mai Martaba Sallama Da Kalaman Gaisuwar Aminci Agareki Tare Da Hadadiyar Daular Murmushin Fuska Mai Cike Da Nuni Da Isar Da Muhimmin Sako Zuwa Gareki
❤️❤️
Ki Agaji Zuciyata Da Kalaman Sonki Ki Yayyafawa Ruhina Ruwan Sanyin Murmushinki Mai Fitowa Cikin Tsakiyar Labbanki Masu Daukar Hankali
❤️❤️
Ina Cikin Tsakiyar Sonki Sabuwar Duniya Ta Musamman Mai Dauke Da Kayan Alatu Masu Faranta Ruhin Jikina
❤️❤️
Ina Mika Sakon Gaisuwa Mai Dauke Da Fatan Amincewar Ruhin Zuciyarki Fatana Kawai Kicemin Kin Karba
❤️❤️