Yadda Zaka Gane Budurwa tana Sonka Amma Tana Boyewa

 Yadda Zaka Gane Budurwa tana Sonka Amma Tana Boyewa

Alamun Tana Sonka Amma Tana Boyewa:
SHARE 🔔
#tsagayarmalamtonga 
Ba duk mata bane suke iya bugun gaba su cewa namiji suna sonshi ba.
A dabi’a irin na mata duk irin son da take maka ba zata iya furta maka ba. Sai dai akwai wasu alamomin da mace idan tana sonka takan fito dasu a fili.
A darusan mu na baya mun kawo wasu daga cikinsu. Yanzu ma ga wasu alamomin da zaga gane mace tana sonka amma ta kasa furta maka.
 
1:Yawan Fara’a: Macen da take sonka taba iya boye farin cikinta a duk lokacin da kuka hadu.
Fara’a, murmushin sune kawai zaka ga suna bayyana a fuskanta. Sabanin mace idan bata ra’ayin ka.
2: Yawan Ambatarka: Mace idan tana sonka cikin kalamanta 10 dole sai ta ambaci sunanka koda kuwa misali zata bayar.
3: Kokarin Sanin Halin Da Kake Ciki: Duk irin yadda zaka boye rayuwarka macen da take sonka sai ta gano halin da kake ciki.
Bazata iya yin wuni gudaba ba tare da ta ji lafiyarka ba.
4: Dabi’un Ta: Duk yadda zata yi kokarin boyewa ta fatan baki, dabi’un mace mai sonka baya iya boyuwa musamman idan gaka gata.
Mace idan tana sonka kuna haduwa duk wanda zai lura sai ya fahimci akwai soyayya a tare da ita wajen yadda zata yi mu’amala da kai.
5: Yiwa Abokanta Zancenka: Mace idan tana sonka bata shakkar fadawa abokanta irin yadda take jinka a zuciyarta.
Irin wadannan mata akasari ta wajen kawayensu kake samun labarin soyayyar da suke maka.
6: Zaka Tayi Kokarin Dadada Maka: A duk inda ka hadu da mace mai sonka bazaku rabu ba sai ta tabbatar koda da kalmane ta dadada maka. 
Ko da wasa kaga wani abu a tare da ita kana cewa ta baka zafa mika maka, sai dai idan daga baya ta maka bayanin nata ne ko kuma aikenta aka yi.
7: Kishi: Macen da take sonka koda wasa taga kana kula wasu matan sai ka ga fuskanta da alamun rashin jin dadi.
Macen dake sonka bata iya boye kishin da take yi akanka koda kuwa akan na kusa da ita ne.
8: Kwalliya: Macen dake sonka idan zaku hadu sai goma sai kaga tayi wani shigan da zata burgeka.
Macen datake sonka bata yarda ta hadu dakai har sai idan ta tabbatar taci kwalliyar da zaka yaba mata.
9: Rashin Mantuwa: Macen datake sonka bata manta duk wani magana da kukayi. Wasu hatta kalmar da kayi amfani da ita sai ta haddacesu.
Alamun gano mace tana sonka shine ta tabbatar maka bata manta wani bayani ko alkawarin da kuka yiwa juna ba.
10: Mace idan tana sonka duk wani kalmar da zaka furta mata farin ciki yake sakata.
Koda mara Fara’a ce kana mata Barkwanci zata tuntsire da dariya.
 
Wadannan wasu ne daga cikin dubannin alamomin da mace zata iya nuna maka tana sonka ba tare da ta furta maka kalmar so ba.
Maza sai a kula domin kada a yi sakaci da damar da aka samu.
Agajahub publishers

3 thoughts on “Yadda Zaka Gane Budurwa tana Sonka Amma Tana Boyewa”

 1. Gaskiya Nima irin wadannan alamomin daya daga ciki ta taba faruwa dani(ban mantawa lokacin da muna islamiyya tin 2014 akai wata yarinya sunan ta hafsat to a islamiyya din akwai wani hadisi ana arawa dalibai shi idan ka gama karatu sai ka maida toni ki kafin in maida sai nawa ya bace shine malamin islamiyyar yace idan ban nemo Shiba saiya dokan to inajin haka kawai sai nabi sauran aji na kannen mu ina cigiya ina zuwa ajin su wannan yarinyar dayin cigiya sai tace gashi nan bayan kwana daya zuwa 1 week sai naji ance wai itama nata ya bace Wai ashe nata ne ta bani,to inajin ance za'a doketa sai na maida mata Amma ni gaskiya nayi wasa da damata Kuma sai yanzu daga baya tin 2015 bayan na gano hakan sai Kuma santa na kasa mantawa da ita yarinyar tana nan har yanzu kuma ina da number dinta amma idan na kira ta da zarar ta fahimci nine (Faisal) saiya sa number din a blaclist 2022 dinnan na fara kiranta 25/03/2022 yau 7 years kenan Kuma batayi aure ba,gaskiya nayi matukar dana sani😭😭😭😭.
  DOMIN SHAWARA
  Facebook
  Faisal g yari
  Ko
  Faisal garba
  Then
  WhatsApp
  08108192077 Or 0808 029 6357.
  Thank you

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top