Abubuwa 5 da ke fitar da soyayyar namiji daga zuciyar mace:

 Abubuwa 5 da ke fitar da soyayyar namiji daga zuciyar mace:

So gamon jini inji bahaushe. Akwai matukar dadi da annashuwa idan soyayya ta kasance tsakanin masoya har karshen rayuwa. Kauna da kular da ke zama a zukatan masoya ba gama-gari bace kuma ba abar dauka da wasa bace.

Soyayya na bukatar kulawa, raino, lokaci da kuma abubuwa da yawa da ke iya sa ta dade na tsawon lokaci.

A wannan rubutun, zamu tattauna a kan abubuwan da ke sa son namiji ya fita daga zuciyar mace kwata-kwata. Ga kadan daga ciki:

1. Rashin Kula: Yawan lokacin da ka ba kowanne abu ke bayyana makomarsa. A misali, yawan lokacin da ka ke ba wa aikinka na bayyana yawan abinda zaka samu a karshe. Hakazalika soyayya kuwa, yawan lokacin da ka ba ta na nuna yadda za ta girma tare da habaka. Rashin kula kuwa na iya tarwatsa soyayyar namiji daga zuciyar mace.

2. Rashin Yabo: mata na son a nuna musu idan har abu ya birge ko kuma sun yi dai-dai. Mata na son a yaba kwalliyarsu, girkinsu, maganarsu da sauransu. Rashin yabo na sa soyayyar namiji ta fita daga zuciyar mace.

3. Kunci: Kunci na kawo rashin zaman lafiya a kowacce irin alaka. Ba soyayya kadai ba, hatta kawance babu mai son yi da mutum mai matukar kunci. Kunci na taka rawar gani wajen wargaza soyayyar namiji daga zuciyar mace.

4. Kalubalanta akai-akai: Mata basu kaunar namiji mai yawan kalubalantar su. Kalubalanta na fara shiga tsakanin masoya ake samun babbar matsala tsakaninta da masoyinta.

5. Yi wa mace rikon sakainar kashi: Wasu mazan na soyayya da mace amma kiran mintoci kalilan na gagararsu. Wannan nuna halin ko in kula din na sa mace ta daina son namiji kwata-kwata.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top