AMFANIN ZOGALE GA DAN “ADAM ( MORINGA ):

 AMFANIN ZOGALE GA DAN “ADAM ( MORINGA ):

๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

SHARE ๐ŸŒฟ

1๐ŸŒฟ- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer). 

2-๐ŸŒฟ Ana shafa danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai. 

3-๐ŸŒฟ Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya.

4๐ŸŒฟ- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.

5๐ŸŒฟ- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin sauri warkewa. 

6๐ŸŒฟ- Sanya garin zogale a cikin abinci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari. 

7-๐ŸŒฟ Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa โ€˜yar kadan domin maganin ciwon shawara. 

8๐ŸŒฟ- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne. 

9-๐ŸŒฟ Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono. 

10๐ŸŒฟ- Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi. 

11๐ŸŒฟ- Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka sha kamar shayi yana maganin sanyi. 

12-๐ŸŒฟ Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga yara. 

13๐ŸŒฟ- Ana daka ganyen zogale da โ€˜yaโ€™yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta. 

14๐ŸŒฟ- Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya โ€˜yaโ€™yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa. 

15๐ŸŒฟ- A daka zangarniyar zogale da โ€˜yaโ€™yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da kuma kimba domin karin karfin da namiji da sa masa kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi. 

16๐ŸŒฟ- A daka saiwar zogale da โ€˜yaโ€™yan kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendis). 

17๐ŸŒฟ- Haka kuma idan mutum yana fama da ciwon AIDS zogale kan radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale. 

18๐ŸŒฟ- Haka kuma mai fama da Typhoid da malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.

๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top