Kalaman Soyayya Masu Dadi

Kalaman Soyayya Masu Dadi

Kamar yadda kowacce bishiya keyin rassai a sama, kuma tayi saiwa a kasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina, idan na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki, sai nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki su mamaye zuciyata, har in iya mantawa dakaina, ina matukar kaunar ki a raina.

Assalamu alaiki farin cikin zuciya ta kuma sanyi idanuwana, hakika kece mace ta farko wacce na yi gamo da ita,
bantaba zato ko tsammanin za’ayi wata ‘ya mace wacce zata sace min dukkanin ruhi a mafi kankantar lokaci ba sai ke,
amma sai gashi ba tsammani nayi kicibis da kyakkyawar fuskar da na kasa dauke wa kallo,
Hakika kyauwun ki yakai ayi misali dashi, kinsha gaban duk mai tinani, zuciyar ki Kyakkyawa ce, tafiyar ki mai tsari ne,
Rayuwar ki abar kallo da koyi ne, lallai nayo matukar Sa’ar samun mace kamar ki a cikin rayuwata Muradina, Annuri na, Kuma Shalelen Zuciyata.🥰🥰🥰
Happy valentines day 💝💑
By Prince Muhammad😍
My people🤩🤩
My friends🥰🥰

All my life I have searched but never found a girlfriend who is so perfect for me. With you I do not need to worry about the future ♥
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top