Wasu Kalaman Da Duk Wata Mace Take Son Jinsu Daga Bakin Masoyinta:
SHARE 🔔
Ba wai maza bane kadai ke jiran mata su kodasu ba. Suma mata suna son jin zuga da kirari daga bakunan masoyansu.
Ga wasu Kalaman da duk wata mace tana son jinsu daga bakin Masoyinta.
1: Ina sonki tsakanina da Allah
2:Kina da matukar kyaun da kunya nake ji ace nine kika zaba a cikin miliyoyin mazan dake wannan duniyar.
3: Ko a Aljanna banida wacce tafi ki
4: Duk lokacinda naji muryarki a zahiri ko ta waya sai naji hankalina ya fita daga gareni na wasu dakikoki saboda zakin muryarki
5: Kece zabina
6: Da duk maza zasu yi sa’a samun mace Irina da babu saki.
7: Burina mutu ka raba
8: Samunki a rayuwa, kyautace mafi girma daga Allah.
9: Yarana sun dace da uwa
10: Kece farin ciki na.
Wadannan kalmomin da irinsu da dama kalmomine da duk wata mace ki bukatan jinsu daga bakin habibinta.