MAGANIN CUTTUKA GUDA 20

 MAGANIN CUTTUKA GUDA 20 

     

         

Ai share Dan Allah. 

1- MAGANIN ULCER:-

A dafa ganyen zogale atace asa zuma agarwaya asha kofi🥛 daya sau biyu arana zuwa kwana bakwai

2- MAGANIN CIWON KAI:-

Adaka ganyen zogale🌿 ko amurtsaka arika Shafawa agoshi. 

3- MAGANIN ZUBAR JINI;-

Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo sai ya daka danyen zogale🌿 ya shafa jinin zai tsaya.

4- MAGANIN KURAJE:- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale🌿 da man zaitun ya rika Shafawa kullum.

5- MAGANIN GYAMBO:-

Ana zuba garin zogale🌿 akan wani rauni ko gembo domin saurin warkewa.

6- MAGANIN HAWAN JINI:-

Arika barbada garin zogale🌿 a cikin abinci ana ci yana maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.

7- MAGANIN SHAWARA:-

Ana dafa ganyen zogale tare da jar kanwa ‘yar kadan asha rabin kofi🥛 sau biyu arana zuwa kwana biyar. 

8- MAGANIN CIWON IDO:-

 A diga💧 ruwan danyen zogale, sau daya arana zuwa kwana uku.

9- MAGANIN CIWON KUNNE:-

Arika diga💧 ruwan ganyen zogale sau biyu arana zuwa kwana uku. 

10- MAGANIN KARA RUWAN NONO:-

Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale ta tace ta zuba zuma ta sha Kofi☕ daya sau biyu arana zuwa kwana bakwai.

11- MAGANIN YAWAN FITA FITSARI:-

Wanda ke fama da yawan fitsari ya dafa furen zogale tare da citta ya tace ya zuba zuma ya garwaya ya sha rabin kofi🍵 sau biyu arana zuwa kwana bakwai.

12- MAGANIN SANYI:-

A tafasa furen zogale da albasa a sha kofi🍵 daya sau biyu arana zuwa kwana bakwai. 

13- MAGANIN TSUTSAR CIKI TA YARA:-

Arika basu ruwan danyen ganyen zogale cokali biyu🥄🥄 sau daya da safe zuwa kwana uku.

 

14- MAGANIN CIWON HANTA:-

Ana daka ganyen zogale da ‘ya’yan baure a sha cokali biyu🥄🥄 acikin nono sau biyu arana zuwa kwana 14

15- MAGANIN SANYIN KASHI:-

Asoya ‘ya’yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa ko man-ja sai arika Shafawa.

16- MAGANIN KARFIN MAZA:-

A daka zangarniyar zogale da ‘ya’yan da ke ciki tare da kanumfari, citta, masoro da kuma kimba arika Shan Kofi🥃 daya sau daya arana zuwa kwana bakwai.

17- MAGANIN TSAKUWAR CIKI:-

A daka saiwar zogale da ‘ya’yan kankana arika shan cokali day🥄 acikin nono sau biyu arana zuwa kwana bakwai.

18- MAGANIN ZAZZABI:-

Adafa ganyen zogale atace asa zuma agarwaya asha rabin kofi🥃 sau biyu arana zuwa kwana uku.

20- MAGANIN BASIR:-

Adafa ganyen zogale tare da sassaken marke atace asha rabin kofi🥃 sau biyu arana zuwa kwana.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top