FIBROID SHRINKER!
MAGANIN ‘KARIN MAHAIFA (FIBROID)
——————————————————————–
MINENE FIBROID?
SHARE
Kafin bayanin alamomin, mu fara da minene “fibroid”? Fibroid wata matsalace a mahaifar mace, wato wani yanayi ne da wani curin nama yake fitowa kuma yana girma a mahaifar mace. Ƙululun naman mai cutar da lafiya yana É—anfare da wani sashen mahaifar (uterus) da wasu igiyoyinsa matakam. ” Fibroid” kalmar turanci ce, domin sauÆ™in furuci da Hausa, zamu cigaba da amfani da lafazin FAIBIROD a cikin bayanin mu anan . Anyi Æ™iyasi cewa cikin mata 100, kashi 20 zuwa 50 na matan suna da fibroid, musamman a shekarunsu na samun haihuwa – wato daga shekara 16 zuwa 50. Wani Æ™iyasin kuma ya nuna cewa mata 30 zuwa 77 suna samun matsalar fibroid a lokacin shekarunsu na samun haihuwa, wato lokacin Æ™uruciyar balaga zuwa lokacin tsayawar al’adar mace saboda manyanta ko tsufanta (menopause). Mafi yawan nau’in faibirod da ake samu bayada alaÆ™a da ciwon-daji / kansa (not cancer). Ƙululun ko Æ™wallon irin wanda baya da nasaba da ciwon-daji ne (benign/non-cancerous). Yana iya fitiwo fiye da É—aya a mahaifa, kamar guda uku, huÉ—u koma fiye da haka a wurare daban-daban cikin mahifa.
ALAMOMIN MATSALAR FAIBIROD
Wasu daga cikin alamomin sun haÉ—a da:
1. Zubar jinin al’adah mai yawa, ko na tsawon lokaci
2. Zubar jini a baƙin lokutta ko tsakanin lokuttan haila
3. Ciwon ƙugu, saboda ƙululun yana danne wani sashen jiki cikin mahaifa
4. Yawan fitsari
5. Ciwon baya daga ƙasan baya
6. Jin zafi /ciwo lokacin yin jima’i
7. Rashin jini a jika saboda yawan zubar jini
8. Rashin jin dadi a mara, musamman saboda girman ƙululun a ciki
9. Basur maisa tsugunni a bayi saboda rashin fitar bahaya
10. Ciwon ƙafa
11. Girman ciki kamar mace tana da juna biyu amma ba juna biyu bane, musamman idan faibirod din ya girma
12. Koma rashin ganin wasu ko daya daga cikin alamamomin da muka yi bayani
WASU DAGA CIKIN MATSALOLIN DA FAIBIROD ZAI IYA HADDASAWA:
– Matsala wajen haihuwa/lokacin naÆ™uda
– Matsala yayin fama da juna biyu
– Matsalar rashin samun juna biyu / rashin É—aukar ciki ga mace saboda Æ™ululun ya toshe/taushe ko danne wani bangaren mahaifa
– Yawan bari/zubewar ciki
Yana da matuƙar muhimmanci mai jin daya ko fiye daga cikin wadannan matsalolin yaje asibiti domin binciki ko tana da matsalar faibirod ko akasin haka. Idan kuma kin riga kin sani to sai a nemi magani.
MINENE KE KAWO MATSALAR FAIBIROD?
Har yanzu dai masana ilimi a fannin lafiya na Æ™oÆ™arin fahimtar cikakken dalilin daya sa ake samun fibroid. Saidai an gano cewa yawan sinadarin ESTROGEN (estarojin) a lokacin shekarun da mace ke iya samun haihuwa yana da nasaba da lokacin da mata ke samun matsalar faibirod. Daga shekara 16 zuwa 50 shine lokacin da sinadarin yafi yawa a cikin jinin mace. ESTROGEN daya ne daga cikin manyan sinadaran jikin mace, wato ESTROGEN sinadari ne na jinsin mace dake tafiyar da girman jikin mace, rayuwar mahaifarta da yanayin halittarta daya shafi jima’i . A lokacin balaga sinadarin na taimakawa yasa nonuwa da gashin mara da hammata su fito, kuma shine ke saka sha’awa ko yawan sha’awa ga mace idan yayi yawa. A lokacin balaga Æ™wayayan mahaifa (ovaries) zasu fara samar da sinadarin. Za’a iya kiran ESTROGEN da suna MAƘERIN ƳAN MATA , domin kuwa shine ke taimakawa wajen sauye-sauyen halittar jikin mace yayinda take girma. A taÆ™aice, ESTROGEN shine sinadarin da faibirod suka dogara dashi domin samun daÉ—a girma a mahaifa, wato makamasin faibirod. Faibirod zai cigaba da girma har sai lokacinda mace ta bar yin al’ada saboda girma (menopause), daga nan sai ya fara Æ™anÆ™ancewa.
WASU DALILAI DA KA IYA SA YIWUWAR MACE TA SAMU FAIBIROD:
– Gado : Idan mahaifiyarki ko Æ´ar uwarki ta taba samun fibroid zai iya yiwuwa ki samu saboda gadon jini.
– Jinsin baÆ™ar fata: Mutanen Africa ko Æ™asashen bakar fata, wato jinsin baÆ™ar fata su suka fi kowanne jinsin mata a duniya samun matsalar faibirod. Kuma matasa mata baÆ™ar fata sune suka fi samun matsalar a shekarunsu na matasa. A Æ™asashen turawa, Indiya da Chana da sauran wasu Æ™asashen, ba kaso ake samun matansu da matsalar ba.
– Amfani da hanyoyin tsaida haihuwa (Æ™wayoyin tsaida haihuwa wani lokacin zasu iya sa faibirod ya girma), Æ™iba, Æ™arancin sindarin vitamin D, yawan cin jan-nama, rashin cin abincin ganye da yayan itatuwa, shangiya da sauransu.
Hanyoyin asibiti na magance matsalar asibiti ya Æ™unshi: aikin tiyata (surgery) domin cire Æ™ululun tare da cire wani bangaren mahaifa “uterus” [Hysterectomy] wanda zai hana samun haihuwa, sa’annan wani nau’in aiki tiyatar [Myomectomy]wanda baya hana haihuwa a gaba, Æ™wayoyin magani da wasu hanyoyin. Musamman idan ya girma aikin tiyata ne akafi yi domin rabuwa da matsalar.Girman faibirod na iya zama kwatankwacin girman dutse karami ko Æ™asa da haka , ko girman lemun tsami ko na zaÆ™i, ko girman Æ™wallo, girman jariri koma fiye da girman jariri, musamman idan ba’a cire shiba ko magance saba. Wasu likitocin naganin idan faibirod yakai girman inci 4 (4 inches/9-10 cm) to akwai buÆ™atar ayi aikin tiyata domin a cire shi. Idan Kuma bai kai hakan ba insha Allahu akwai maganin da zai narkar da shi (FIBROID SHRINKER).