MINENE HANYOYIN TSUKE FARJI ?

 MINENE HANYOYIN TSUKE FARJI ?

Akwai hanyoyi da dama na matse gaba musamman bayan haihuwa wanda sun hada da hanyoyin magani, motsa jiki (exercise), tiyatar likita domin rage girman farji da sauransu. Wasu hanyoyin nada illa ga lafiya , wasu kuma hanyoyin basa da wata matsala ko hadari kamar dai yanda likitoci ke bayani. Wasu daga cikin hanyoyin:

1. Kamar yadda Ibrahim Y. Yusuf ya fara fada Motsa jiki , hanyoyin motsa jiki na zamani domin matse gaban mace suna da yawa (such as kegel exercises) da sunaye. Motsa jikin ya shafi horo da mace zata iya bawa jikinta domin ya zamanto tsokokin gabanta masu motsi sun kara ƙarfi da tsukewa. Misali, wata kwararriyar likita a India Dr. Sangeeta Gomes ( Consultant Obstetrician and Gynaecologist) , ta nuna cewa mace zata iya inganta tsukewar gabanta idan tana yin motsa jikin dauke numfashi (breathing exercises). Zaki dauke numfashinki na tsawon ‘yan daƙiƙoƙi (seconds) kadan sannan ki tsuke (tsokokin) farjinki matakam na tsawon wani lokaci a lokacinda kike mai dauke numfashin. Za kiyi hakan a kowace rana, sau 10 ko 15. Zaki iya yin hakan a kicin lokacinda kike aiki, a ofis, a tsaye ko a zaune , a ko ina kuma a ko wane wuri bata tare da ma wani yasan abinda kike yi ba. Sa’annan zaki yawaita cin Ƴaƴan itatatuwa (kayan marmari) da abincin ganye (vegetables). Wannan ko shakka babu zai taimakawa mace wajen matse gaba domin gyara aurenta. Wani nau’in motsa jikin kuma shine ake cema “Kegel exercise”. Toh yaya ake yinshi? Dr. Gomes ta nuna cewa idan kina yin fitsari sai ki tsaida fitar fitsarin, wato ki riƙe fitarin, ki danne sa na tsawon daƙiƙoƙi 10 , wato ki ƙirga 1 zuwa 10 sa’annan ki saki fitsarin a hankali a hankali. Zaki iya yin hakan sau 2 ko 3 a rana idan za kiyi fitsari. Shima wannan nau’in motsa jikin na tsuke gaban mace.

2. Hanya ta biyu shine wanke gaba da ruwan sanyi mai ƙankara. Yana taimakawa wajen matse gaba amma sai an hada da motsa jikin da muka yi bayani. Wannan yana daga cikin hanyoyin da Dr. Gomes ta zayyana. Amma zaifi dacewa ace sai mace ta gama wankan jegonta na kwana 40 kwatakwata sa’annan tayi amfani da ruwan sanyin , wato bayan ta koma “normal”. Saɓanin yanda al’adar Bahaushe tayi imani dashi cewa ruwan sanyi na lalata gaban mace ,wasu likitocin a wasu al’adun na ganin yana matse gaba.

3. Yin amfani da aluf (alum). Aluf yana matse gaba sosai sai dai likitoci na tsoratarwa akan yin hakan saboda da sinadarin kemikal ne.

4. Yin tiyatar likita domin rage budewar farji. Wannan ma hanya ce ta zamani amma ana tsoratarwa akan yin hakan saboda wasu dalilan lafiya.

5. Yunƙurin tsuke gaba a lokacin saduwa, wato ki matse farjinki ta ciki lokacinda mijinki yake kaikawo. Zaki yawaita yunƙuri domin tsuke gabanki domin mijinki yaji alamun ana riƙe masa al’aura tamkar zobe zagayen gabansa. Idan mace na yawaita yin da haka to zai zama ɗabi’arta kuma nan gaba ba zata san ma tanayin hakan ba saboda ta riga ta horar da jikinta, kuma hakan zai inganta jin daɗin mijinta sosai. Allah Ya taimaka.

6. Da sauransu.

(Kabiru Danwuri)

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top