SADUWA, SOYAYAYA, BUDURCI !!!…
Yanmata dayawa suna qorafin cewa Gayu sukan Kaurace musu da zarar sun nemi su sadu dasu sunqi, wassu kuma sukanyi qoqarin bayarda budurcinsu ga Gayu don kawai kada su gujesu.
– Bari nayi 6alo-6alo anan . Budurci bashine ke zama dalilin da Gayu ke guduwa ba kadai, dukda cewa Gayu dayawa suna buqatar saduwa da macen, idan basu samu daman hakan ba, sai su gudu …
Matsalar bawai budurci bane ko saduwa …
Yanmata dayawa basu samun hali nagari da zai tallafawa budurcinsu domin zama yayi kyau wassu kuma suna alfahari da hakan domin abunda da zasu iya kaiwa mazajensu kenan gidan aure
Ku tuna bakowa bace ake xina da ita a layi sannan ta rasa budurcinta, wassu sun rasa.
Kuma bayan budurcinki, meye kuma zaki iya bawa mijinki?
– Zaki iya tallafamar spiritually?
– Zaki iya tallafamar physically?
– Yaya tallafamar mentally kuma?
Babu abinda kikayi sai roqon kudin jaka, takalma, sutura, da kuma fita kashe kudi batareda dalili ba.
Shin kin ta6a zamar da Gayenki domin nunamar ya daina kashe miki kudi domin gyara future dinshi?
Shin Gayen naki ya ta6a ganinki a matsayin wacce zaiyi zama na amana da ita?
Sau nawa ya ta6a shiga halin rudani yazo gareki domin neman shawara?
Keba karuwa ammana kina tara Gayu a kofar gidanku da sunan farin jini.
Suma masu kai budurci gidan aurensu su sani kina kaiwa gidan auren shikenan budurcin ya kau, ammana halinki nagari shine zaici gaba da wanzuwa.
Tabbass kowa yanada nashi gazawar.
AMMA….
Yi qoqari kizamto irin mace wacce kowani namiji zaiyi kewa idan akace babu ke tattare dashi.
Yi qoqari kizamto irin mace wacce Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace irin Macen aljannah kenan.
Gina Gayenki irin yadda kikeso yazama ki daina neman miji ready-made.
Ki tusa kanki ga wannan ready-made Gayen dakika gani da kudi domin kinaga zaki more, Watarana zakiji labarin kanki da gori daga gareshi wanda baki ta6a tsammani ba.
– Tare dake muka nemi arzikine?
– Tunda kika shigo gidannan meye naci gaba kika kawomin?
Mata ku kiyaye kwadayin abun hannun Gayu domin duk wanda ya hau motar kwadayi, zai sauqa a tashar wulaqanci.
Allah Ya mana jagoranci.