Wanene Bestie!, Ma’anar BESTIE Dakuma Yadda Ake gane Bestie
WANENE BESTY?
Besty shine amintaccen abokin mace wanda yake iya bata shawara ko umarni a wasu lokutan.
Matan aure, zawarawa da ýan mata da yawa suna da abokai (Besty) Shi besty mutum ne da mace bata gudanar da mafi yawan mu’amalar rayuwarta sai da sanin sa da amincewar sa.
Lokaci Yayi daya dace abar wannan kazamar Huldar, shiriritar 😂
Bestie wato shakikai maza da wasu ‘yan mata suke yi a yanzu na daukar hankali a baya-bayan nan, inda maneman matan kan kalle shi a matsayin barazana saboda yadda suke ganin ya na wuce makadi da rawa a mu’amulla tsakanin shi da ‘yan matan su.
Shin wacce barazana ka taba fuskanta daga bangaren Bestie? Ka aje lambar wayarka za mu kira ka don jin yadda ta kaya a shirinmu na Darasin Rayuwa.
FALALAR BESTIE.
Bestie,shike gane mana duk namijin da ke sonmu tsakani da ALLAH,da kuma mai yaudara🥳
Sannan yana daga cikin tsananin kaunar mu,da bestie gane duk wani mai binmu
da wata nufi da gane makiyan mu,a duk inda suke😁
Jinjina ga BESTIE mai daraja
Bestie Amanar BeBestie
*DUNIYA MAI YAYI*
Bestie Bestie
kowani lokaci akwai Sabuwar Tsurfa da take bijirowa al’ummarmu sai su kamata hannu bibbiyu ana yayatata a social media harma a fili. mekyau da mara kyau duk wadda tazo kawai ana ɗaukarta ne gaba gaɗi, kome kesa hakan?
Yan uwa musanifa ita Wannan kalma da ake ta furtawa ta Bestie.
Shi fa bestie babban masifa ce ga yarinya da kuma iyayenta har mijinta,, bestie kana da budurwar ka, kai ko hannu ba ka taba rike mata ba amma bestie shi. Al’amarin bestie Babu kyau sa’annan bestie yana iya yiwuwa har yarinya tayi aure duk wani sirrin gidan auren ta yana a hannun bestie ko kyauta kayi mata sai ta raba da bestie, Yarinyar kirki ba ta yin bestie, dayawa fa da za’a yi DNA da bestie ya shiga uku wannan bestie da aka maida wasa ba abun wasa bane, wai yarinya tana da bestie babu aikin sa sai koya mata ayyukan lalata,
Amma yanzu an maida abun wasa bestie zai rungumi bestie normal ce wurin ta bestie xai rike hannun bestie, bestie yafi ka sanin sirrin BUDURWAR ka ko matar ka da sauransu.
Mafi yawan masifofin da ke damun al’ummarmu a Wannan Zamani duk mu muke jawowa kanmu.
Ya ƴan uwana muyiwa kanmu karatun ta natsu mukoma ga Tafarkin magabata wala alla zamu gudi tare mu tsira tare.
Kamar yanda yake akowace irin ALAQA akwai nagari akwai baragurbi, haka yake acikin #BESTIE, Zalunci ne yimana kudin goro
Idan kaji ana cewa rijiya ta bada ruwa, guga ta hana, idan kaji ana cewa, dan hakin da ka raina, idan kaji ana cewa masoyi da soyayya wanda ke cin moriyar soyayya daban, ka tsane shi, soyayyar ka ta fara rawa, ka bishi ka kaskance, ka iske shi da budurwar ka kace wane in kun gama firar ka turo min ita. Wannan duk aikin #BESTIE ne, Kalma daya tak! akan #bestie
Wato yanzu na fahimci wanene #bestie#.
Duk wanda kaga yana jin tsoran yarinyar sa ta cigaba da kasancewa da #bestie# to kodai baya da gaskiya kokuma yana cikin wayanda ake kira samarin shaho.
Dan kuwa na shiga tsarin nan na #bestie# yanzu haka #besties# din danake tare dasu wato aminai na mata na yi binciki a samarinsu gabaki daya kaf babu wanda yake santa da aure nakuma gayamata ta dauki mataki nan take.
Ni zan bincikamata mijin aure wandaya dace da ita dakuma ni kaina.
Bestie alkairi ne duk da dai ni tawa bata san ma minene bestie ba.
Barkan mu da safiya.
Ya Tsalleke Genotype
Ya yayi Gwagwarmaya da Cousin
Ya murkushe Bestie
Ya kori latecomer
Yayi fito na fito da malamin Islamiyya
Duba da Irin artabun dayasha
Dole yayi Sujadar Godewa Allah