KALAMAN SOYAYYA WACE KALMA KI/KA TABA FADAMA SAURAYINKI KO BUDURWA ??
ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA |
Amincin Allah da kariyarsa da yaddarsa su tabbata ga sarauniyar kyauwa Tauraruwa mai haskaka duniya.
Gani nazo gareki ko na samu jin daddadan kalamanki masu sanya nutsuwa ga mai sauraro. Sannan naga tsura surar da Allah ya baki wanda ke samar da farin ciki da nishadi ga mai kallo.
Taku kike tamkar sarauniya, ina so nayi amfani da wannan damar na bayyana miki yadda sonki yake a cikin zuciyata, sonki yabi jijiya ya ratsa tsoka ya fasa kashi da bargo da ke rayuwa rayuwa sonki shi ne ya zamto jinin jikina.
Yabonki shi ne abincina begenki shi ne ruwan shana, kaunarki ita ta zamto min numfashi na, my one ba zan iya rayuwa idan babu kece farin ciki na da girmanki nake kwana da yabonki nake tashi da zancenki nake yini duk motsina naki ne kece farin cikin zuciya ke ce abar alfaharina kece kadai idaniyana ke iya gani, ki tallafawa dan marayan da ya rasa duk wani farin ciku don ganin ya sameki. Kece kadai zaki iya dawomin da farin ciki na da walwalata da dariya idan kikace bakya sona zan rasa rayuwata.
Zuwa ga bakuwar zuciya mai saurin fuska hadi da labaran suna mai dadin kamshi mai Murmushi mai zazzakar murya, ita ke sani na manta komai. Haka kula idanuwanki sukansa na zamanto makaho a yayin da suke shan yokar mace tana kusanto almajirinta, idan an kira sunanki sai naji wani nishadi tamkar an yimun albishir da aurenki, duniyar masoya kizo muyi shigewa ki sani a hannun dama domin jini da jijiya hadi da duk kaina farin ciki ciki da idan na tunaki sai naji wani shauki ko aiki ki yarda da ni ki sani a cikin zuciyarki sarauniyar mata.
Sallama da fatan budewar kofofi tare da farin ciki a gareki tare da farin cikin mai girma gami da annashuwaa gareki diyar girma a wajena, Boyayyen sirri ne zan bayyana a gareki saboda lokaci da nayi akanki my dear, duk-kan bishiyoyi da girmaaye da ruwan sama Allah ya halicce su ne dan mu mutane mu rayu haka kuma numfashi da lafiya ba’a cewasu saboda sun zama dole rayuwa haka ita soyayyar gaskiya ba’a siyanta da kudi baiwa ce daga Allah yanzu idan nace kin dauke kaso mafi tsoka wajen sanyaya farin ciki cikin ya zaki ji? Tun lokacin dana fara cin karo da ke kwarjininki yake ta bugun zuciyata, da yawa saina ji murmushi ya cikan fuskata idan na tunoki, me yasa hakan?
Ni dai nasan a kowanne lokaci ina jin halayen halayen musamman sanin girman mutane da kula, amma idan nace sunanku shine mafi yayi da yawan ambato a cikin zuciyar zuciya ya zaki ji?
ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA
ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYA |
kalamaina zuwa gareki a yanzu da kuma wadanchan ba baya,da wadanda zan rubuto maki a Chan gaba,Ina furtasu NE da tsantsar gaskia, irin gaskiyar da Mutum zai fada a lokacin da yam fashi suka Dora masa wuka a wuya,
Ina sanar dake cewa lokaci ya Dade yana hadani da yammata iri iri a shekarun baya,yau da gobe kuma ta ringa janye min baragurbin cikinsu, Kaddara kuma ta dauki wasu ta kaisu dakin aure,yau gashi mun hadu dake har ma Na Fara Jin KECE WADDA zan baiwa ajiyar ZUCIYATA,
Ni ba attajiri bane kuma ba Mai tarin dukiya bane,amma inada tarin Kaunarki a cikin ZUCIYATA, wadda ke hauhawa a kowane kankanin lokachi,
Idan har Na zama Wanda zaki zaba a matsayin mijin aure banyi maki alkawarin yin rayuwar aure irinta gidajen masu kudi ba,Alkawarina gareki shine zan Kula dake irin kulawar da marubuta ke kwatantawa a tsakanin taurarin cikin litattafansu,
So da Kaunarki sun samu nasarar zama manyan fadawam ZUCIYATA NE a dalilin tarbiyyarki,Ina rokonki ki dore akan hakan,wannan zaisa soyayyarmu taci gaba da habaka,