ALAMOMIN MIJIN DARE

 ALAMOMIN MIJIN DARE

 

Daga cikin alamomin da mace zata gane tana da

wannan matsalar shine:-

・ Shi wannan shaidanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita cikin barci, yawanci mata suna tsintar kansu cikin wannan yanayin, amma sai su dauka shirmen mafarki ne kawai, to a gaskiya ba haka bane. Duk mata ko budurwar da take irin wannan mafarkin za ka same ta tana fama da wadannan matsalolin, ko da za ka tambaye ta wadannan matsalolin za tace maka tana fama da su. Daga ciki akwai:-

・:  Bacin rai ba a mata komai ba, ta ji tana jin haushin kowa har ma da mijinta ko kuma ta ji kamar mijin ya sake ta, ta gaji da auren, da za ka tambayeta laifin mijin ba zata fadi laifinsa ba, wata rana ma ta ji tana tsanar ‘yan’yanta.

・: Yawan ciwon kai daga lokaci zuwa lokaci kuma baya jin magani.

・: Tsananin ciwon kirji da ciwon baya.

・: Tsananin ciwon mara lokacin al’ada da kuma zubar wani ruwa daga farjin mace, shi ba al’ada ba ne, kuma ya kasu kashi 2; mai yauki da maras yauki ko mai kauri kamar koko tare da yawan kaikayi ko fitowar kuraje.

・: Ga yawan zubar ciki ko bari, ko kuma rashin samun ciki, amma za ta iya kasancewa ta dauki alamomi na masu ciki har ma ana zaton tana da ciki, amma ana kwana 2 sai ta canza kamar ba ciki ba, ko ta rinka yawan mafarki ta haihu.

・: Idan mijinta yana saduwa da ita tana jin zafi, ko kuma yana saduwa da ita ba zafi, amma bata samun biyan bukata.

・: Daf da magariba ta dinga jin zazzabi ko faduwar gaba ko yawan tsorata, ko kasala da bacin rai.

・: Idan ta dauki Alku’ani za ta karanta sai ta dinga jin kasala da hamma da hawaye da barci da zarar ta ajiye kur’anin sai ta ji wartsake kamar ba ita take jin barci ba.

・: Sannan kuma ko ta kwanta tana son yin barci sai ta kasa, ta yi ta juyi ta kasa barci, mijinta na zuwa kusa da ita sai ta dinga samun

firgita da tsoro.

・: Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga kadewa ko ya yi ja, bakinta ya dinga bushewa ko yayi ja.

・: Yawan kaikayin ido da kaikayin kai na amosani, amma ba amosani ba ne.

・: Yawan kaikayin kunne da yawan kaikayin hanci kamar mura, amma ba mura bane, ko yawan kunburin ciki..

・: Yawan zuban jini daba na al’ada ba, ko jini ya rika yi mata wasa.

Sannan kuma har ma wacce bata da aure budurwa ko bazawara za ta iya samun wannan matsalar, amma ita bambancin da ke tsakanida ita wacce take da aure shine kamar haka:-

☛ Ita marar aure za ta kasance duk lokacin da wani ya zo wajen ta da maganar aure kamar za a yi sai abin ya lalace daga wajen ta ko daga wajensa.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top