Amfanin ganyen dalbejiya guda 16 a jikin dan adam
🌿- Itacen dogon yaro ko kuma dalbejiya ya kasance mai matukar amfani ko a la’adar bahaushe
🌿- Yana yin magunguna daban-daban na cutukan da ke addabar jikin dan Adam
🌿- Ganyen na tsarin iyali, maganin dafi, maganin kwari,hana kamuwa da cutukan jima’i da sauransu
Itacen dogon yaro ko kuma dalbejiya ya kasance ice mai matukar amfani ko a al’adar bahaushe. Ana kiran itacen da ‘Neem tree’ a turance. Tana da daci amma tana da matukar amfani a jikin dan Adam.
Ga wasu amfanin dalbejiya a jikin mutum:
1🌿. Ganyen dalbejiya na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawar zuciya, musamman idan aka dafa ganyen ana shan ruwan kamar shayi.
2🌿. Yana taimakawa wajen tacewa da tsaftace jinin jikin mutum.
3🌿. Ganyen na maganin cutar zazzabin cizon sauro da typhoid.
4🌿. Yana maganin cutar ciwon ciki, musamman idan mutum ya murde saboda wani abinci da aka ci.
5🌿. Ganyen dalbejiya da man shi na gyara fatar jikin mutum.
6🌿. Ganyen na maganain saiko, amosanin kai da kuma sa tsawon gashin kai.
7🌿. Ana iya amfani da man dalbejiya a matsayin dabarar bada tazarar iyali.
8🌿. Ganyen na kawar da cutar daji, musamman na nono da ‘ya’yan maraina.
9🌿. Ganyen na maganin cutar gyambon ciki da rauni a jiki.
10🌿. Yana rage kiba a jiki musamman ga masu fama da ita.
11🌿. Yana warkar da ciwon gabobi da ciwon kai.
12🌿. Yana kare mutum daga kamuwa da cutukan da ake samu ta hanyar yin jima’ai.
13🌿. Yana warkar da cutar kuturta.
14🌿. Yana maganin ciwon ido.
15🌿. Yana maganin guba da ake samu daga jikin dabba kamar cizon cinnaka, maciji da sauransu.
16🌿. Ganyen na maganin kwari musamman wadanda ke lalata amfanin gona.