Ankusa kulle Registan Neman Tallafin NG-CARES Yayinda Ake Kokarin Fara Aiwatar da Shirin a Sauran Jahohin Nigeria, Gajerin Wasu Abubuwa Masu Amfani Daya Kamata Kutanda Kafin Enumerator Su Fara Tantancewa
Neman shiga jerangiyar masu neman tallafin na NG-CARES na cigaba da gudana a tashar neman yayinda ake dab da rufewa.
Tuni wasu jahohi suka rufe nasu neman ga masu sha’awar amfana da shirin.
Read This Also
Anriga an tura kudi kimanin Naira Biliyan 35 da Miliyan 500 ga jahohi talatin da shida da babban birnin tarayya Abuja inda jahar Lagos ta samu Naira Miliya Dari Tara (N900,000,000) kudin an riga anbadasu ga kowace jaha da Abuja.
Bayanin sakar kudaden masu nauyi yafito ne daga bakin wani kwararren jagora na babban bankin duniya na Nigeria a ofishinsu dake Abuja Mr. Foluso Okunmadewa a wani taro karo nafarko don aiwatar da shirin na NG-CARES wanda ya gudana a garin Ikeja na jahar Lagos.
Wallafawan Jaridar businesspost.ng
Ana sa ran cikin watan gobe na Aprilu wakilai na shirin zasu fara tuntuba domin daukan bayanan mutanenda suka nuna sha’awar cin gajiyar ta hanyar register.
Yi kokari ka mallaki wani shaida na registan kasuwancinka kamar CAC, SMEDAN ko TIN certificate domin akwai yiyuwar su bukata domin shaida ka a matsayin mai kasuwanci ko sana’a.
Allah sa munada rabo a cin gajiyar tallafin