CIWON NONO GA MATA, YADDA AKE MAGANCE CIWON NONO TA HANYAR MAGANIN GARGAJIYA, GYARAN NONO DAKUMA YADDA AKE DAUKAR CIWON
Wato Sanqaran Mama ko kuma Kansar mama.
MA’ANAR ciwon nono shi ne samuwar wasu kwayoyin cuta acikin nonon mace, wandanda ke haddasa ciwo da canja yanayin nonon mace ko ya lalata shi gaba daya. Ciwon nono wani lokacin yana janyo ru6ewar nono ko yay sanadin a yanke shi gaba daya.
YADDA AKE DAUKAR CIWON
Abubuwan da ke kawowa mata ciwon nono.
1- Shekaru ko tsufa.
Idan mace shekarunta suka dan fara yawa, to yana da kyau ta fara daukar matakan kariya daga ciwon nono.
2- Sinadarin ‘iyistirogen’, idan yay yawa ajikin mace.
3- Fara jinin al’ada kafin mace ta kai shekaru sha biyu, za ta iya gamuwa da ciwon nono daga baya.
4- Mace ta zarce shekaru hamsin da biyar tana jinin al’ada, shi ma zai iya janyo mata ciwon nono.
5- Rashin haihuwa. Matan da sam ba su haihu ba, har su ka wuce shekaru talatin, za su iya kamuwa da ciwon nono.
6- Jinkirin haihuwa.
Idan mace ta dauki shekaru da yawa da aure ba ta samu haihuwa ba za ta iya kamuwa da ciwon nono.
7- Girman jiki.
A binciken likitoci, mace mai tsawo da mace mai kiba, sun fi shiga hadarin kamuwa da ciwon nono, musamman masu tarin kitse a jikinsu ko a kugunsu.
8- Gado.
Idan iyayen mace suna fama da ciwon nono, to itama zai iya yiwuwa ta yi gado.
9- Idan nonon mace guda daya ya ta6a yin ciwo, to zai iya yiwuwa dayanma ya kama ciwo daga baya.
10- Matar da aka ta6a cire mata tsiro a mamanta, yana da kyau ta dinga zuwa asibiti tana samun shawarwari don gudun kamuwa da ciwon nono daga baya.
ALAMOMIN CIWON NONO
1) Canjin yanayin girman nono.
Haka kawai ki ga nononki yana kara girma ko ya yamutse, ba tare da wani dalili ba.
2) Jin kullutu acikin nono.
Za ki ji kamar wasu abubuwa suna tsirowa daga nononki, har suna kara girma.
3) Canjin kalar fatar nono. Za ki ga fatar nonon tana komawa kamar yalo-yalo ko jaja-jaja ko wata kala daban.
4) Canjin kalar fatar kewayen nono (nipple), ki ga fatar wajen ta yi jajawur.
5) Kan nonon mace (nipple) ya zama ya kumbura haka kawai kuma yana ciwo.
6) Fitar wani ruwa kamar ruwan ciwo haka kawai daga nonon mace. Ba sai lallai matar aure ba, ko da budurwa ce.
7) Radadi da ciwo mai zafi akan nonon da kuma hammata ko da yaushe kuma haka kawai.
8.) Kumburin hammata tsakanin allon kafada zuwa sashin nonon.
9- Jin ciwo mai tsanani idan kika matsa nonon.
RIGAKAFI YA FI MAGANI.
Yadda za ki gane kina dauke da cuta a mamanki, tun kafin ya fara ciwo.
1- Za ki ga wani dan tsiro akan nononki amma ba ya ciwo kuma ba ya zafi, wasu matan ma suna dauka kamar wani abin ado ne.
2- Yana iya farawa da jin ciwo kadan a maman.
3- Ya kan iya farawa da ciwo ko kaikayi a fatar da ta zagaye kan nonon.
4- A wasu matan kuma, kan nonon ne yake fara shigewa ciki, za ki ga kan nono daya ya shige ciki, dayan kuma ba haka yake ba. Likitoci suna ganin idan har kan nonon ya lo6a ciki, to cutar ta fara ha6aka kenan.
5- Wasu ya kan fara da fitar wani ciwo a karkashin maman, wanda zai dinga kara yawa, yana kewaye kasan maman kuma ba lallai ne ya zama yana yin zafi ba.
Karin bayani.
★ Idan akayi sake ba a dauki mataki da wuri ba, zai iya yiwuwa ciwon yayta ci daga ciki, har ya taso fatar maman, ya zama gyambo wanda yake fitar da jini da ruwa mai wari.
★ Zai iya yiwuwa ciwon nono ya fara ta saman fatar, yana kuma iya farawa daga can cikin nonon, don haka da an ji canji to a gaggauta tuntu6ar masana.
YADDA AKE MAGANCE CIWON NONO TA HANYAR MAGANIN GARGAJIYA.
1- Sakiya. Idan nonon mace ya kumbura har ya ja ruwa, ana iya yin sakiya, wato a yi amfani da kayan aiki wajen huda ruwan ya tsiyaye. Kwararrun masu magunguna ne kadai suke yi.
2- Idan nonon mace yana kaikayi ne, sai a hada Man Zaitun da Man Hulba, ta dinga shafawa.
3- Wacce nonon yake mata ciwo da radadi kuma sai ta samu Garin Ararra6i, ta dinga jika cokali daya, tana sha, kullum, har zuwa kimanin sati daya zuwa biyu.
3- Idan kari ne acikin ciwon, sai a samu Garin Sabara cokali daya, garin Bakin Kajiji rabin cokali, a jika a ruwa, ta sha. Tsallaken kwana daidai, ta sha kamar sau biyar.
Amma dai mafi kyau shi ne aje asibiti ko wajen kwararren mai hada magungunan gargajiya.
GYARAN NONO.
Kara girmansu, cikowarsu, mikewarsu, kara musu sheki da kuma hana su zubewa.
Sai a gwada daya daga cikin wadannan hanyoyi.
1) Wacce nononta ya zube a sakamakon shayarwa, ko kuma su ka zube sakamakon rashin samun abinci mai dauke da sinadaran da ke gina nono, sai ta yi wannan hadi.
1- Habbatussauda
2- Hulba
3- Alkama
4- Gyada
5- Ridi ko Kantu
6- Danyar shinkafa
7- Busasshen karas.
A hada su waje daya, a markada ko a nika. Sai a dinga diban cokali biyu a sha da madara, kullum, safe da yamma.
2) Masu karamin nono kuma
Wacce kuma ta ke asali nononta dan karami ne amma tana so ya kara cikowa, ya taso sosai, to sai ta yi wannan hadi.
1- Albasa madaidaiciya
2- Zuma
3- Garin gero
4- Madara
Yadda za a hada.
Ki samu albasa madaidaiciya, ki yanyanka, sai ki
saka a tukunya da ruwanki ta tafasa shi sosai
har sai ruwan ya koma baki, sai ki juye ruwan ki
sami zumar ki mai kyau, garin gero ludayi daya,
madara ta gwangwani daya na ruwa sai ki juye
su kan ruwan tafasasshe albasa nan ki sha .
Amma fa karki bari ya kwana baki shanye ba.
Wannan hadine da zai gyara miki nono
3) Wacce ta ke so nononta yay kyau da laushi da sheki.
Idan Ana so nono yayi kyau yayi laushi da santsi
da girma sai ayi wannan hadin.
1- Aya
2- Gyada
3- Ayaba (plantain)
4-Alkama
5- Madara
Yadda za a hada.
Zaki wanke ayarki, sai ki hada da gyadarki ki
markada su, ki tace, dama kin yanyanka ayabarki, kin busar, kinyi gari da ita, kin tankade sai ki rikka
diban garin plantain din kina hadawa da ruwan
ayaba gyadarki kina sa madara ta ruwa kina sha.
Zai gyara miki nono domin wannan hadi ne wanda sai kin sha mamaki.
4) Mai shirin shiga daki.
Idan za ay bikinki amma kina so nononki ya cicciko, ya tsaya, kara kyau, sai kiyi wannan.
A samu garin Hulba, sai ki tankade, yay laushi sosai. Sai ki dama ta da ruwan dimi, ki shafe nonon, ki saka rigar mama wacce ta matse ki. Da safe sai kiy wanka da ruwan dimi, ki shafe su da man hulba. Kiyi haka kamar sau uku zuwa biyar ko bakwai. Ki kuma dinga dama hulba kina sha cokali biyu kullum da madara ko zuma.
Nonuwa za su cicciko tare da yi kyau kuma jikinki zai kara kyau da kumari.