Hirar Soyayya Masu Dadi Da Ratsa Zuciyar Masoya
Farin Cikin Dake Sauka Cikin Farin Ganin Da Idanuwa Sukayi Akanki Shine Samuwar Samun Garkuwar Shaukin Dake Bugun Numfashin Raina
❤❤
❤
Ke Kyakkyawace Tunda Kyawunki Yakai Matakin Kurewar Kallon Masu Tukun Kasaita Da Nuna Isah Bisa Mizanin Kyau Acikin Jerin Masu Kyau Kinyi Gaba Shiga Gaba Ya Mai Martabar Nuna Isah Da Tamkar Kyawun Fuska
❤❤
❤
Allah Yasa Banyi Sauri Ba Cikin Tafiyar Da Ba Gajiyawa So Shine Silar Haduwarmu Har Gashi Muna Kwadayin Zama Na Har Abada
❤❤
❤
Cikin Sauri Da Salon Sarrafa Harshe Wajen Daidaituwar Haruffan Dazasuyi Ladabin Rubutun Gaisuwar Aminci Agareki
❤️❤️
❤
Kalaman Farko Cikin Alkaluman Rubutun Haruffan Zanen Gaisuwar Bangajiya Daga Tushen Jinin Dake Yawo Acikin Jijiyoyi Jikina
❤️❤️
❤
Da Sallama Zan Fara Assalamu Alaiki Yar Halak Jinin Albarka Sakone Daga Zuciyar Dake Miki So Guda Daya Wanda Babu Muradin Kasantuwar Yimiki Kishiya
❤️❤️
❤
Idan So Ya Motsa Dolene Zuciya Tayi Aman Abinda Ke Cikinta Hakanne Yasa Bana Gajiya Wajen Shaida Miki Irin Yanda Nakeji Alokacinda Shaukin Begenki Yakama Zuciyata
❤️❤️
❤
Walwalin Walkiyar Hakoranki Sunyi Daidai Da Fitowar Murmushinki Cikin Tsakiyar Ranar Dana Fara Dora Idona Akan Kyakkyawar Halittarki
❤️❤️
❤
Kinada Kyau Na Halitta Kyawun Diri Da Kyawun Tsayuwa Kinyi Daban Da Sauran Mata Tafiyarki Kadai Abun Koyice Garesu Domin Kin Gagari Hadu Cikin Ni,imar Haduwa Da Iya Salon Sarrafa Murmushin Alfarma
❤❤
❤
abokai da kawaye!!
Allhmdlh!Allhmdlh!Allhmdlh!
ina mai farin cikin sanar da ku cewa nayi sa’ar samo masoyiyata wacce na dauki tsawon lokaci ina nemanta (i .e 5yrs ),tsawon shekaru biyar ina fama da tarin dakon sonta wanda ban san ranar saukewa ba amma Allah cikin ikonsa sai gashi na sameta don yanzu ina waya da ita time to time.Sai dai na sameta a kurarren lokaci don ta girma ta isa aure gashi ni kuma bani da komai kuma garinsu da nisa,tace mini ita zata iya zama da ni aduk wani hali da ake ciki kuma ko a ina nake zata zauna da ni,ta kara da cewa ko bani da kowa bani komai ba zata taba guduna ba.to abun gaskiya i was confused and don’t know what to do,pls need ur advices.