Kalaman Soyayya Da Dabarbarun Sarrafa Zuciyar Masoya

 Sinadaran Kalaman Soyayya

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. A wannan karon in sha Allah za mu tattauna kan sinadaran da suke kara dandano da zakin kalaman soyayya tsakananin masoya. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.

 1.Sarrafa Murya

Wata babbar ka’ida da take kara inganci da tasirin kalaman bayyana soyayya tsakanin masoya ita ce, yanayi da sigar da kalaman ke fita su isa kunnen mai sauraren su. Dole sai masoya sun rika sarrafa murya wajen bayyana shaukin kaunarsu ga juna; kowane kalami da irin sigar muryar da tafi dacewa da shi:

• Kalaman nuna so da kauna ana furta su garwaye da shaukin bege, cikin bayyanannun kalmomi, wata sa’in ana iya furta su cikin yanayin wake, ko a siririntar da murya ko a nauyaya ta don ta yi daidai da lokaci da kuma yanayi.

• Kalaman tausayawa, suna bukatar a tausasa murya wajen furta su, a cakuda murya kafin a bayyana jimamin abin da ake tausayawa dominsa.

• Kalaman ban hakuri na bukatar a nauyaya su da muryar da-na-sani, nadama da marairaicewa.

• Kalamana godiya na bukatar a kawata furucinsu da farin ciki da jin dadin abin da ake godewar.

• Kalaman wasa da zaurance kuwa sai a surka muryarsu da jin dadi da nishadi.

• Kalaman sha’awa, ko dai a sa murya ta yi taushi yayin furucinsu, ko a sanyaya ta, ko a siririnta murya, ko a sa murya ta yi kasa-kasa, ko a rika fitar da kalaman cikin rada, ko a rika fitar da su dai-dai cikin yanayi na jan hankali; abin nufi dai, ma’aurata su yi kokari su rika karya murya cikin siga mafi dacewa da lokaci da kuma yanayi. Kalaman sha’awa ba lallai sai sun yi ma’ana ba wata sa’in, ana iya caccakuda wasu kalmomi a fitar da su da wani irin karin muryar sha’awa wadanda zai sa su yi tasiri sosai.

• Kalaman neman alfarma sai a gauraya su da muryar kwantar da kai da marairaicewa.

2. Sarrafa Jiki

Sarrafa yanayin jiki ya dace da kalaman kaunar da ake bayyanarwa, shi ma yana matukar kara fa’ida da tasirin kalaman bayyana soyayya tsakanin masoya. Kowane kalami; kowane karin murya, akwai irin yanayin lauya jikin da ya fi dacewa da shi. Fuska ita ce madubin zuciya, duk abin da mutum ke ciki, za ka iya fahimtar hakan daga yanayin da fuskarsa ta alamtar; don haka sai masoya su rika kiyaye irin sakon da fuskarsu ke bayyanawa lokacin da suke kalaman soyayya.

• Lokacin furta kalaman nuna so da kauna, sai masoya su zanance fuskarsu da launikan kauna, ta hanyar marairaicewa da kallon juna cikin kwayar ido, da sa kwayar idon ta yi narai-narai da shaukin so.

• Wajen bayyanar da sha’awa shi ma sai a marairaitar da fuska cikin hayakin sha’awa, tare da lallauya wasu bangarorin jiki yadda za su fito da ma’anar cikin kalaman da ake furtawa; misali narairaitar da ido cikin ruwan sha’awa, da jujjuya kwayar idon, da sarrafa girar idon, da yin gatsine cikin yanayin shagwaba ko cikin yanayin tsiwa (amma tsiwar wasa), murguda baki, daga gira, yanayin tafiya, yatsina na yatsun hannu ko na jiki duka, yanga, kissa da kisisina da sauran abubuwa makamantan haka.

• Wajen nuna godiya da jin dadi, dole ma’aurata su barbada garin farin ciki da jin dadi a fuskokinsu.

• Wajen nuna tausayawa, sai ma’aurata su jike fuskarsu da jimami da shaukin tausayi.

Da sauran ire-iren yanayin sarrafa jiki don ya dace da kalami, yanayi da kuma bukata.

3. Hirar Kyautata Soyayya:

Yana da matukar alfanu ga masoya da su sanya wani lokaci a kullum, komai kankantarsa, wanda za su rika yin hirar jin dadi da debe kewa a tsakaninsu, yin haka zai yi matukar kyautata so da kaunar da suke yi wa juna, kuma zai matukar inganta dangantakar da ke tsakaninsu. Duk lokacin da suke irin wannan hira, ya kamata masoya su kiyaye wadannan muhimman abubuwan:

• Ya kasance ma’aurata sun mayar da hankalinsu ga dari bisa dari ga junansu, watau su saurari junansu da gaba dayan kafofin hankalinsu.

• Kallon ido cikin ido ya zama wajibi gare su lokacin da suke hirar, da kallon fuskar juna da fahimtar sakon da ke zayyane a fuskar wanda zai kara fito da ma’anar hirar da suke yi.

• Sauraran yanayin shaukin da ke cakude cikin kowane kalami a lokacin hirar, na miji ya kamata ya kiyaye da wannan, domin mata na da wani irin halin yin magana a murgude, watau su fadi magana alhali a cikin zuciyarsu ba hakan suke nufi ba, ta hanyar sauraren shaukin da ya cakudu da kalamin, ko yanayin zane da launin fuska, ko yanayin sarrafa jiki ne kadai zai sa a fahimci maganarsu ba iyakar maganarta ke nan ba.

• Ma’aurata su kasance masu lura da yanayin yaren jikin sunansu lokacin hirar, wannan zai kara kusanci da jin dadin hirar gare su.

• Sannan ma’aurata su lura kada su rika katse junansu yayin irin wannan hirar, duk wanda yake wata magana, komai rashin muhimmancinta a wajen mai sauraren, to ya yi hakuri ya bar shi har sai ya kai aya tukun, domin katse mutum lokacin da yake tsakiyar zance na haifar da jin haushi cikin zuciyar wanda aka katse din. Yana da matukar alfanu kowane daga cikin ma’aurata a ba shi cikakkiyar dama ya fadi dukkan abin da ke ransa, kuma a saurare shi cikakken sauraro.

4. Muhimman Abubuwa

• Yana da matukar muhimmanci sosai masoya su rika yaba wa juna ko da sau daya ne a kullum, kuma yabo na gaskiya ba na riya ba. Sai a lura da wani abu na musamman a yabi wanda ake aure da shi; kuma ya kasance ana dan caccanza abun yabon ba kullum a kama abu daya a yi ta maimaita yabo a kansa ba.

• Sannan a rika yabon wanda ake aure a gaban wasu daban wadanda za su iya sanar da shi wannan yabon, kamar a wajen ‘yan uwa.

• Sannan masoya su yi kokari wajen fahimtar ra’ayin junansu, kuma su rika yi wa juna uzuri game da ra’ayoyinsu da kalamansu.

• Haka kuma masoya rika kokarin tauna duk kalamin da zai fito bakinsu, don kauce wa fadar kalamin da zai iya haifar da husuma ko jin zafi a tsakaninsu.

• Sannan ma’aurata su rika zabar kalmomi mafiya dadi; mafiya dacewa da kowane zancen da suke yi.

5. Abubuwan Kiyayewa

• masoya su kiyaye fadar kalmomin kushe ko kasawa ga junansu; domin irin wadannan kalmomi suna saurin gusar da soyayya da haifar jin haushin juna tsakanin ma’aurata.

• Sannan masoya su kiyaye takaita surutu lokacin hira, sannan kada daya ya mamaye hirar ya kasance shi kadai ke zuba, ya ki bayar da dama ga dan uwansa shi ma ya fadi albarkacin bakinsa.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top