Ku zabeni 2023 ni matashine “Tinubu”

Idan kuka zabeni zan magance matsalar tsaro a wannan kasar

Ni matashine Tinubu

 

Dan takarar shugaban kasa kuma jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa shi matashi ne kuma har yanzu yana da karfin da zai jagoranci kasar nan.

Tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da wasu ‘yan jam’iyyar APC da magoya bayan sa a karshen mako.

Tinubu ya ce jam’iyyar APC za ta ci gaba da kare muradun ‘yan Najeriya na gida da waje da kuma tabbatar da cewa kasar nan ta dore.

Ya kara da cewa yana da ikon yiwa Najeriya hidima da kuma daukaka kasar.

“Ina nan tsaye a gabanku… kuma ni matashi ne,” in ji Tinubu yayin da magoya bayansa ke murna.

Yaya kuke ganin wannan Maganar ta Bola Ahmad Tinubu?

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top