Kalolin Abincin Gargajiya da Yadda ake Sarrafasu.

Kalolin Abincin Gargajiya da Yadda ake Sarrafasu.

Abincin gargajiya

Abubuwanda ke ciki.

1.1 Gabatarwa.

1.2 cikakken Bayani akan abincin gargajiya.

1.3 Kalolin Abincin Gargajiya guda 8.

1.4 Bayani daya bayan daya akan yadda ake sarrafa wadannan abincin guda 8 na gargajiya.

1.1 GABATARWA

 Abincin gargajiya wani kalar abincine wanda da yawa daga cikin mutane suna son abincin amma basu san yadda zasu sarrafashiba.

A yau wannan shafi namu zayyi muku bayani yadda zaku iya sarrafa abincin da kanku ba tare da wata wahala ba.

1.2 Cikakken bayani akan abincin gargajiya.

A yau zamuyi bayani dangane da abincin gargajiya da yadda ake sarrafa abincin.

Kamar yadda aka sani abincin gargajiya wasu kalar abincine da malam bahaushe ya ta’allaka wajen amfani dashi a rayuwarshi ta yau da kullum, kuma shi wadannan kalar abincin sanada sinadarai masu gida jiki daban-daban.

Uwar gida sai ki biyomu daki-daki dalla-dalla domin ganin bayanai yadda zaki sarrafa wadannan kalolin abincin cikin sauki.

1.3 Kalolin abincin gargajiya guda 8, gasu kamar haka:

  1. Tuwon masara.
  2. Tuwon shinkafa.
  3. Tuwon ruwa.
  4. Tuwon dawa.
  5. Wainar kwai mai alayyahu.
  6. Taiba.
  7. Sakwara.
  8. Danbun shinkafa.

1.4 Bayanai dalla-dalla akan yadda ake sarrafa wadannan abincin guda 8 na gargajiya.

(1).Tuwon masara.

Tuwon Masara

Masara wani kalar abincin malaman bahaushene, wanda yana iya sarrafata ta hanyoyi daban-daban.

Abubuwanda ake buqata.

  • Garin masara.
  • Ruwa.

Yadda Ake Sarrafasu.

Da farko uwargida zaki saka ruwanki a cikin tukunya sai sun tafasa, a duk lokacinda ruwan suka tafasa dama kin riga kin tankade garinki sai ki zuba garinki cikin tukunyarki ta ruwan zafi bayan sun tafasa ki talgashi sai yayi kauri bayan haka sai ki jika kanwarki kisata a ciki kadan daga nan sai ki ajiye tukunyarki bayan an dau lokaci kamar minti 15 sai ki kwashe abinki cikin plate kiyi malmala-malmala da abinki.

(2).Tuwon shinkafa.

Tuwon shinkafa

Shinkafa na daya daga cikin abincin malam bahaushe wadda yake iya sarrafata ta hanyoyi daban-daban.

Masana sun bayyana cewa masara tana daya daga cikin abincinda ke gina jiki, kuma tanada wasu sinadarai daban-daban a jikin Dan-Adam.

Abubuwanda Ake Buqata.

  • Uwargida zaki samu shinkafa ta Tuwo.
  • Ki samu Ruwa.

 ake sarrafasu .

Da farko zaki aza ruwan zafinki sai sun tafasa, sannan ki wanke shinkafar tas idan ruwanki sun tafasa sai ki saka shinkafarki da kika wanke a ciki sai ki rufe tukunyarki.

A duk lokacinda shinkafarki ta fara dahuwa sai ki rage wuta kadan ta yanda shikafarki zata tsotse ruwanda ke ciki sai ki tuke shinkafar ki tuka sosai sai ta tuku daga nan sai ki kwashe tuwonki a plate kiyi mai malmala-malmala.

(3).Tuwon Ruwa.

Tuwon Ruwa

Tuwon ruwa wani kalar abincine da malam bahaushe yake so wannan kalan abincin yanada matukar amfani ga jikin Dan-Adam kuma yanada sinadarai daban-daban.

Abubuwanda Ake Bukata.

  • Uwar gida zaki samu gero.
  • Ki samu Ruwa.

Yadda ake sarrafasu.

Da farko dai uwar gida zaki jika geronki ya kwana 2 zuwa 3 a jike amma zaki rinka canza Ruwa lokaci bayan lokaci, misali kin jika geronki yau da dare banda gobe da safe sai ki markado geron naki ki tace abinki sai ki dora ruwanku saman wuta. Idan ruwanki sun tafasa sai ki juya geronki ki motsa shi daga nan sai ki zuba cikin ruwan zafin ki rinka turawa sai kahwarki tayi karhi sosai kiyi ta jujjuyawa ki maidawa cikin ruwa.

Sai ki kwashe tuwonki a cikin kwano ko leda kiyi mai malmala-malmala.

(4). Tuwon Dawa.

Tuwon Dawa

Dawa dayace daga cikin abincin malam bahaushe. Kuma yana iya sarrata ta hanya kala-kala kuma tanada sinadirai daban-dabab

Abubuwanda Ake Buqata:

  • Uwar gida Ki samu nikakken garin Dawa.
  • Ki samu kanwa.
  • Ki samu ruwa.

Yadda ake sarrafasu.

Daga farko uwagida zaki dora ruwan zafi sai sun tafasa, bayan ruwan ya tafasa dama kin riga kin tankade garinki sai ki debo ruwa yan kadan ki saka a cikin garin dawarki da kika tankade sai ki dama sai ki zuba dawarki da kika dama cikin ruwan zafin.

Zakici gaba da tukawa kada yayi gudaji sai ki samu ruwan kanwan kadan ki saka a ciki sai ki kyaleshi yayi ta dahuwa idan yayi sai ki tuka zakiga har wani yauki yakeyi, idan kin gama tukawa sai ki kyaleshi kamar tsawon minyi goma sha biyar 15 zakiji har wani kamshi yakeyi sai ki kwashe kiyi masa malmala malmala.

(5).Wainar Kwai Mai Alayyahu.

Wainar kwai

Abubuwanda ake Bukata.

  • Kwai.
  • Attarugu
  • Albasa.
  • Hanta.
  • Alayyahu.
  • Mai.
  • Carry.
  • Magi.
  • Gishiri.

Yadda ake sarrafasu.

Da farko uwargida zaki yanyanka alayyahunki kanana-kanana, Hantarki zaki dakata bayan kin dahesu sai ki fasa kwanki ki zuba hantar a ciki da albasa, idan kinaso kina iya soyawa kamar yadda ake soya wainar kwai.

(6).Taiba da miyar miyar akushi.

Taiba

Abubuwanda Ake Bukata.

  • Garin kwaki.
  • Ruwa.
  • Agushi.
  • Nama.
  • Manja.
  • Busashen kifi.
  • Attarigu.
  • Albasa.
  • Sunadarin dan-dano.
  • Ganyen ugu.
  • Bitter leaf.

Yadda ake sarrafasu.

Da farko uwargida ki tabbatarda kin tsintsi duk wata datti dake a cikin garin sannan a zuba garin cikin tukunya a kyakeshi.

Sannan a samu wata tukunya a aza ruwan zafi sai ya tafasa sai a juye cikin tukunya mai Gari a tabbatarda an saka ruwan da yawa ta yadda zai kai ko’ina a cikin garin a barshi misalin minti 15 sai a tukashi a dora bisa wuta a rage wuta a barshi ya turara sai a sake tukashi a sauke.

(7). SAKWARA

Sakwara

Da farko dai sakwara abincine wanda ya samo asali daga doya.

Kuma tana daga cikin abincinda ke gina jiki, kuma ta kara kuzari a jikin Dan-Adam.

Abubuwanda ake bukata.

  • Uwargida xaki samu Doya.
  • Sai ki samu Ruwa.

Yadda ake sarrafasu.

Da farko za’a fede doyar baki dayanta a yayyankata kanana-kanana zaki zuba ruwa kadan kiyi blending dinta.

Idan ta nuku sai a dorata akan wuta ana jujjuyata da micciya har saita shanye ruwan jikinta ta koma kamar tuwo sai a kara ruwan zafi kadan a ciki a kara tukawa shike nan sai a saukarda tukunyar.

(8). Danbun Shinkafa.

Dambun shinkafa

Danbun shinkafa wani kalar abincine mai dadin gaske musamman idan an tsaftaceshi wajen yinsa.

Abubuwanda Ake Bukata.

  • Shunkafa.
  • Zogale.
  • Albasa.
  • Mai.
  • Attarugu.
  • Gyada.
  • Spice.

Yadda Ake Sarrafasu.

Da farko uwargida zaki kai  sakasu cikin shinkafarki ki juyasu har su hade ki saka maginki da spice da mai kadan.

Ki sake turarawa idan ya dahu zakiji kamshi yana tashi sai kibajiye tukunyarki a kasa shiekenan.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top