Kimanin Manoma 40,000 ne a Kano za su amfana da shirin noma na Gwamnatin Taraiya a wannan shekarar ta 2022.

Kimanin Manoma 40,000 ne a Kano za su amfana da shirin noma na Gwamnatin Taraiya a wannan shekarar ta 2022.

Tallafin noma a kano

Manoma 40,000 ne a Jihar Kano za su amfana da shirin noma na Gwamnatin Taraiya, wanda a ka sani da Anchor Borrowers Programme, ABP domin bunkasa noman shinkafa.Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa, RIFAN na jihar, Abubakar Aliyu ne ya baiyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da Kamfanin Dillacin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Lahadi a Kano.

Ya ce shirin zai raba taki da sauran kayan noma ga manoman shinkafa na rani 15,000, yayin da za a tallafa wa wasu 25,000 ɗin a kakar girbi ta 2022.

Read also:

Aliyu ya ce ƴan ƙungiyar ba su shiga shirin na rani ba a bana sakamakon matsaloli da a ka samu tsakanin Babban Bankin Nijeriya, CBN da wasu Ma’aikatun hada-hadar kuɗaɗe, inda ya ƙara da cewa gwamnatin ta yi niyyar ta maida gaba daya Makka 40,000 zuwa noman damina.

A cewar sa, ko wanne manomi zai karɓi kayan noma da su ka kai N 160,000 domin samun damar noma hekta ɗaya ta noma, ya ƙara da cewa za su biya bashin da amfanin gonar da su ka girbe.Shugaban ya koka da halayen wasu kaina na ƙin biyan bashin da a ka basu, inda ya ƙara da cewa gwamnatin taraiya ta bada kayan noma ga manoma wajen 150,000 a jihar.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top