SAKONNIN SOYAYYA NA BARKA DA SALLAH MASU DADIN GASKE WADANDA YAKAMATA KUTURAWA MASOYANKU RANAR SALLAH
NA MAZA DA MATA
KINA DA KYAU MASOYIYATA.
Shin wani ya taba sanar da ke cewa murmushin
ki abin so ne? Sannan kuma a duk lokacin da kike
yin murmushi ya kan mayar da fuskar ki tamkar
wata fitila mai haske? Ke kyakkyawa ce, hakan
ya sanya kwakwalwata ta zana mini kyakkyawar
fuskar ki a cikin zuciyata wadda ta zamo abar
nazarta a gare ni a duk lokacin da nake zaune ni
d’aya cikin kad’aici a dare ko safiya. Ke ce abar
so na.
Read this also
Hanya 10 Masu Sauki Dazaki Jawo Hankalin Tsohon Saurayinki Ya Dawo Miki
BARKA DA SALLAH
Sababbin Kalaman Soyayya Masu Dadi 2022
FATAN ZAN SAMU ABUN DA NAKE NEMA?
A koda yaushe ina fatan nasara ta kasance a tare
da ke, na kasance mai yin fatan kasancewar farin
ciki a cikin zuciyar ki a safiya ko rana, amma shin
zaki iya tinawa da wani abu wanda zuciyata ke
muradin samu daga gare ki? Ba komai bane face
ki mallaka min zuciyar ki ta hanyar sanya ni a
cikinta ni kadai ba tare da kin hada ni da kowa
ba. Ina son ki.
BARKA DA SALLAH.
Read this also
Sababbin Kalaman Soyayya Masu Dadi 2022
ZAN BAYYANA MAKA SIRRINA
…………………………………………………
Amincin Allah ya tabbata a gare ka sahibina,
a
yau ne nake son na kara bayyana maka matsayin
ka a gare ni, tabbas IBB ka zamo wani jigo na
dorewar farin ciki a zuciyata.
Fuskar ka ce abun
da nake kallo na samu farin ciki .
Bana tinanin A lokacin da kusa dani sai tunaninka,
ranar sallah
kuma ranar farin ciki da murna ,
Nayi maka tanadi a lokacin da Namke ganin Zan baka shi
kasancewar yau ce ranar farin ciki
ina son ka! Ina son ka!! Ina son ka
IBB!!! Daga masoyiyarka Meerat
BARKA DA SALLAH.