Shugaba muhammadu Buhari Ya Bada Umarnin Bude Layukan Waya Sama da Miliyan Saba’in 70,000,000 Da Aka Rufe.
![]() |
Gwamnatin Nigeria |
Shugaba muhammadu Buhari Ya Bada Umarnin Bude Layukan Waya Samada Miliyan Saba’in 70,000,000 Da Aka Rufe.
To maganar gaskiya dama nasan maciya amanar tsaron kasar nan bazasu so wanan hukuncin da gwamnatin taraiyya ta dauka karkashin ma’aikatar sadarwa da professor Isa Ali Ibrahim pantami ke jagoranta ba maganar da masu hankali yakamata su fahimta ba mahaukata makiya zaman lafiya shine:
(1) Ta’addancin kasar nan na gudana ne kaso 90% ta hanyar amfani da wayar salula yau da ace za’a gudanar da wannan shirin da ake da zummar yi wallahi sai ansamu nasarar dakile Ta’addanci kaso 85% cikin 100% amma dayake Wanda suke da Alhakin daukar nauyin gudanar da ta’addancin sun san wanan ce babban hanyar gudanar da kasuwancin su da rayukan jama’a yasa suka fara kaiwa gwamnati kushe da nuna cewa tana kara ta’azzarawa talakawa wanda manufar su kawai suke karewa ta hanyar yakar kyakyawar manufar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu BuhariBMuhammadu Buharimai gaskiya da amana.
(2) Kungiyar SERAP bawai talaka takewa aiki ba a’a tana yakine da aiyukan alkhairan da gwamnati ke shiryawa talakawan ta serap takarbi kwangilar wasu tsirarun mutanen akan maganar kulle layukan wayan da akeyi Dalili kuwa shine a iya kwanakinnan da aka kulle layukan wayoyin da basu hada shi da katin zama dan kasan suba ansamu _nasara akan yaki da yan bindiga da kuma yan ta’addan boko Haram hakane yasa makiya sukaga Za‘a raunata hanyar kasuwancin su yasa suka hadakai da kungiyar serap.
Kirana ga yan uwana talakkawa ku kula ku kama Adu’a itace kadai gatan mu bawai wannan gwamnatin da Azzalumai suka kewaye masu gaskiya da munafurci ba domin shi munafuki kullum a matsayin masoyinka yake tare dakai amma kuma cin dunduniyar ka kawai yake da rusa duk wani shirin Alkairi da zakayi don mutane su amfana.
Allah yasa mu dace.