Zafafan Kalaman Soyayya: Ka Gwada Furtawa Masoyiyarka Wadannan Kalaman Kaga Yadda Zaka Rikita ta Saboda Jin Dadi.

Zafafan Kalaman Soyayya: Ka Gwada Furtawa Masoyiyarka Wadannan Kalaman Kaga Yadda Zaka Rikita ta Saboda Jin Dadi.

Kalaman soyayya

Kalamanda zaka ko zaki iya fadawa masoyiyarka ko masoyinki ya sata farin ciki.

Ga wasu kalmomin da lokacin furta su da ya kamata duk namiji da mace su sansu.

1: Duk diya mace tana son ka yaba muryarta. 

.Ka Nuna mata misalin yanda dadin muryarta yake sakaka nishadi, shine yasa aka haramta bayyana muryar diya mace.

.Irin Wadannan kalmomin yana da tasiri ne musamman ga macen da baka taba haduwa da itaba ba.

.Idan kuma wadda kuka taba haduwa da itace ko matarka ta aurece ce. Sanar da ita yadda dadin sautin muryarta yake sakaka samun kwanciyar hankali.

2: Maca tana son ka Yaba gashin kanta.

.Duk wata diya mace gashin kanta abun alfaharinta ne a wurinta.

.Saboda haka a duk lokacinda zaka kai matarka gyaran gashi ta salon, ko kitso. Yi mata wasa dashi. Zuga mata shi ta yanda ya dace da kanta. Kayi kissing dinshi.

.Duk namijin da yake yawan yiwa matarsa wadannan abubuwan da gashin kanta sai riashiga ranta.

.Maca ta tsani tayi gyaran gashi ko kitso namiji yayi burus da ita kamar bai gani ba.

3: Ba telanda yayi mata dinki zaka rinka zugawa ba, ko yanda kayan suka mata kyau ba. Kiran jikinta shi zaka yaba ka kuma nuna mata telolinda ke yimata dunki kawai kudinta suke ci amma baiwa da Allah (SWT) Ya mata sune suke dacewa da duk wani suturan data saka a jikinta.

.Mace tana son jin wadannan koda kuwa ragga ne a jikinta.

4: ka Tabbata mata kalar baiwa da basiran da take dashi ba duka sauran mata ake samunsu da su ba.

.Diya mace tana son wanda ya nuna yana sonta ya tabbatar mata tanada wani abu na musamman na baiwa da ba’a samunsu a wajen sauran  mata.

5: Idan a wannan ranace ta farko da  ka soma ganinta gaba da gaba ko ganin hotunanta. Yaka mata ka Siffanta ta da wasu jinsin mata mafi kyawo a duniyarnan.

.Tabbatar mata da cewa tana da wata alaka da Larabawa saboda kyawon siffanta. Idan ta fada maka kabilanta.

.Kuma diya Mace komai muninta tana son wanda ke sonta ya tabbatar mata tafi sauran mata kyawu a idanuwansa.

6: Duk diya mace tana son ka gaya mata cewa ka yaba da natsuwarta, hankalinta da kyawawan dabi’unta.

.Idan wannan shine haduwarku karo na farko ko kuma mu’amalar ku ko ta charting ne. Ka Nuna mata duk da bakasan mahaifinta ba kasan wadannan kyawawan abubuwan daka lissafosu dukansu daga wajen mahaifinta ne ta dauko su.

7: ka Nuna mata cewa zaka so ace ka rabata da duk wasu masu sonta da zaka gano sirrin da zaka bi ka mallaketa. Idan ka samu shiga a wajenta  zata ce maka ai batada wani saurayi ko kuma ta nuna maka ko furta maka wani abunda zaka mata na sace soyayyar ta cikin raha kamar yanda zaka mata bayanin cikin raha.

.Diya Mace tuna son namiji ya nuna mata  a shirye yake a yi duk abunda zai iya yiwuwa domin samun soyayyarta.

8: yaba irin girkinda tayi maka idan matarka ce ta aure. Ka Yaba da duk abunda ta kawo maka daga gidansu koda kuwa ace ruwan sha ne, idan kuma budurwar kace.

.Nuna mata yadda baka sha’awar cin abinci a waje idan ka tuna da cewa babu kalar girkin da bata iya ba.

9: Idan matarka ce ka Sanar da ita irin rokon Allah da kayi tayi kamin kayi dacen aurenta. Ko haduwa da ita da kayi idan budurwar kace.

.Ka Tabbatar mata da cewa ita zabine na Ubangiji a gareka bana son rai ba.

10: ka Furta mata burinka shine kayi rayuwa da ita na har abada.

.Diya Mace idan tana sonka ko tana son aurenka bazata taba tunanin akwai ranar da zaku rabu da iyaba. ka Tabbatar mata da hakan taji daga bakinka yin hakan zai kara mata shaukin amincewa da kai.

.Yaka mata duk da namiji ya rinka gayawa budurwarshi irin wadannan kalamai suna kara dankon kauna.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top