Kalamai mafi sauki Da Zaka Dauki Hankalin kowace irin Budurwa Dasu.

Kalamai mafi sauki Da Zaka Dauki Hankalin kowace irin Budurwa Dasu.

Kalaman soyayya

A daidai cikin wannan darasin na yau zamu koya muku yadda zaku shawo kan mace ta hanyar janta da wasu irin kalamai a wajen hira hira.

Da farko dai Duk yadda kake son yarinya matukar bazata baka lokacinta ba to bazaka taba samun danar shawo kanta ba. 

Su kuma yan mata da dama daga cikinsu sai anyi amfani da dabaru ake iya samun janyo hankalinsu harma su saurareka.

Ga wasu kalolin hirar da cikin dan lokaci kalilan zaka zaka iya jawo hankalinta a matsayinta na diya mace. KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA MASOYA MURMUSHI GUDA (9)

1- Idan kana bukatar janyo hankalin diya mace ta hanyar janyo ta zuwa hira, kazo mata da hiran abubuwan da suke faruwa a wannan lokacin. Labarin da ya zagaye gari ko jaha ko duniya da kowa yake yi a daidai wannan lokacin.

Idan kuma kai ka fahimci cewa tasan labarin to nemi ta sanar dakai abunda ke faruwa. Idan kuma kai ka fita sanin labarin to ka bata labarin.

Mata da yawa daga cikinsu suna bukatar jin labari a kowane lokaci, wannanne yasa zake son jin labarin ga wanda yake yasan labarin.

Kada kazo mata da kalaman soyayya a irin wannan lokacin. Sai dai ka nuna mata cewa ga irin matsayinta a wurinka shi yasa kake irin wannan hiran da ita a daidai wannan lokacin. https://www.agajahub.com.ng/2022/02/hirar-soyayya-masu-dadi-na-2022.html

2- Kawai ka nuna mata tana burgeka akan natsuwarta da kwalliyarta da kyawawan dabi’unta.

Ka gaya mata cewa wannan ne yasa a kowane lokaci kake ta zumudin ku gaisa da ita. 

Sannan kuma ya kamata ka Dauki lokaci mai tsawo kana ta  yimata bayani irin abubuwan da suke ta burgeka dangance da ita da ita. 

Da yawa daga cikin Mata suna bukstar kuga ana yaba musu. Shine yake sa suke son sauraron duk wanda zai nuna musu kaunarsa garesu koda ba ta soyaya bace.

3- kuma Idan cewa ita ‘yar bokoce kazo mata da hiranda ya shafi boko da karfafamata akan karatu da kuma nuna mata irin matar da kake so kenan. Haka nan kuma idan Islamiya take yi ka mata zancen tare da yi mata fatan alheri a lokacin zancenku da ita.

Kuma har yanzu da yawa daga cikin Mata suna son duk wanda zai karfafa musu gwaiwa akan abunda suke burin zama arayuwarsu. Wannan ne yasa zata baka kowace irin kulawa tare da tuntubarka akan neman shawararta neman fahimtar wani abu data kasa fahimta na karatu ko na rayuwa.

4- Haka kuma Idan kana son kaja hankalin mace ta hanyar hira da ita. 

Kayi kokarin kirkiro hirar da zata saku yin musu da juna tsakaninka da ita.

Zaka Iya  musanta wani abu wanda ta fika gaskiya akanshi, koda misale ace a tambayi wani shima ita zai bawa bawa gaskiya.

Sannan wannan musanta abunda ta san gaskiyansa da zaka yi, ita zata nemi ta dage cewa sai taga ta gamsar da kai wannan abun saboda ita tasan tana da hujjoji akan magananr.

Ita mace matukar tasan cewa ita tana kan gaskiyaryarta, ba zata taba hakura da barin hirar ba sai wanda take yin musun da shi ya gamsu da gaskiyar tata.

5- Idan cewa kai zaka zowa da mace da hiran yadda zata tainakawa rayuwarta saboda cimma burinta. To Zata iya ajiye komai da take yi domin sauraranka.

Duk lalacewar mace, tana son taji wani ya bata shawarwarin da zasu amfaneta koda kuwa ba aiki dasu zata yi ba.

Ba duk mace bace takke son namiji yace mats yana sontu kai tsayeba ba tare da ta fahimci akwai abunda yasa ka furta mata wannan kalmar so din ba.

Mace tana iya ganin girmawarka kawai taji tana sonsa. 

Toshi kuma namiji yana kamuwa da son mace ne saboda wadansu abubuwanda ya gani tattare da ita. Shine yasa idan kacewa diya mace kana matukar sonta a lokacinda kuka hadu wato ma’ana haduwarku ta farko bazata yarda da kaiba ba.

Ina fatan maza zaku yi amfani da wadannan dabarun da muka lissafo a sama domin sace zuciyar kowacce diya mace kake so.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top