SANARWA: DAUKAN KURATAN YAN SANDA DUBU GOMA (10,000) NA SHEKARAR 2021 ZA’A GUDANAR DA HEALTH SCREENING

 SANARWA: DAUKAN KURATAN YAN SANDA DUBU GOMA (10,000) NA SHEKARAR 2021 ZA’A GUDANAR DA HEALTH SCREENING A KOWACE CIBIYAR GUDANAR DA HARKAR LAFIYA TA JAHA

Rundunar Yan sandan jihar Gombe na farin cikin sanar da jama’a musamman Yan asalin jihar Gombe wadanda suka samu nasarar rubuta jarrabawar gwaji ta kwamfuta da aka gudanar, Computer Based Test (CBT) da ya gudana a ranar 20 ga watan Afirilu na wannan shekarar ta 2022 a Cibiyoyi biyu na horar da naura mai kwakwalwa ta, El-Lawanti da kuma cibiyar ilimi ta Educational Resource Centre dake fadar jihar Gombe.

2. Mataki na gaba na horarwar daukar aikin zai zama tantance wadanda suka samu nasara a bangaren lafiya wato medical screening wanda za’a gudanar daga ranan Juma’a 20 zuwa Litinin 23 ga watan nan da muke ciki na mayu (May) 

Read This Also

PRESS RELEASE: 2021 RECRUITMENT OF POLICE CONSTABLES – MEDICAL SCREENING HOLDS TO HOLD NATION WIDE

WURIN TARO :- Cibiyar lafiya ta Yan sanda dake garin Bauchi a jihar ta Bauchi (Police Clinic Bauchi) Bauchi state.

LOKACI:- da karfe 8:00am na safe a kowacce rana.

   

3. Wadanda suka fafata a matakin baya za su duba sunayen su a yanar gizo na hukumar yan sanda www.policerecruitment.gov.ng sannan su yi printing slip dinsu wato takardar lafiya medical slip da kuma takarda dan kasa mai dauke da lambar NIN.

Wadanda za su je tantancewar za su sanya farar Riga T- Shirt da farin gajeren wando a wajen tantancewar.

4 Kwamishinan Yan sandan jihar Gombe Ishola Babatunde Baba’ita Psc, FDMSS ya taya Yan asalin jihar ta Gombe da suka samu nasarar tsallake gwajin na CBT murna.

Dan karin bayani sai a tuntubi lambobin wayar salular nan 08068508998 ko kuma 07036564060

Sanarwar ta fito ne daga hannun 

ASP MAHID MUAZU ABUBAKAR, Jami’in hulda da jama’a na rundunar Yan sandan a madadin Kwamishinan Yan sandan jihar Gombe.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top