Gidauniyar MTN Ta Bude Shafin Bayarda Sabon Tallafin Kudi Da Horo Mai Taken “MTN Y’ellopreneur” Za’a rufe shigarwar a ranar 8 ga Yuli, 2022
MTN Y’ellopreneur wani shiri ne na gidauniyar MTN da aka tsara don ba da damar ingantawa da samar da kudade ga kwararrun ‘yan kasuwa mata na Najeriya, tare da hadin gwiwar bankin masana’antu.
Gidauniyar ta himmatu wajen cike gibin basirar sana’o’in mata, ta hanyar shirin horar da mata na tsawon mako 4 da nufin karfafawa mata da yawa, a dai-daita da shirin Gwamnatin Tarayya na ci gaba mai dorewa.
Mahalarta horon da suka cika sharuddan zabar manyan ‘yan kasuwa 100, Za su karbi lamunin kayan aiki har naira miliyan biyu, domin su samu ci gaba da dorewar sana‘o’insu. Bayan cikakken biyan lamunin kayan aiki, za a ba da tallafi ga wadanda suka cika tsammanin sharuddan kiredit.
Read this also:Updated About RRR (NASSCO Rapid Response Transfer) Payment Today Tuesday 28/Jun
Apply For Jobbarman Jobberman Soft Skills Training
Bayan da kuka dauki lokaci don ziyartar wannan shafi, kuma ku mace ce mai sha’awar kasuwanci mai sha‘awar habaka kasuwancin ku, dauki matakai don nema kuma ku cika fom din da ke kasa. Ana rufe shigarwar a ranar 8 ga Yuli, 2022. Za a tuntubi Yan takarar da aka zaba kawai. Na gode.
Yadda Zaku Cike
Idan kunada ra‘ayin cike wannan tallafin kuyi amfani da shafin yanar gizo-gizo da ke a kasa domin cikewa kai tsaye https://apps.mtn.ng/yellopreneur/
Tuntuba ko Karin Bayani
Address: MTN Plaza, Awolowo Road, Ikoyi 101233, Lagos, Nigeria
Call From an MTN line: 180
From other networks: 08031000180
From outside the country: +2348031000180
Email Send us an email: customercareng@mtn.com