AN BUƊE SHAFIN ƊAUKAR JAMI’AN ƳAN SANDA GA BAYANIN YANDA ZAKU CIKE
A yau Litinin 15 ga watan Augusta ne, hukumar ƴan sanda ta ƙasa, ta buɗe shafin ta na yanar gizo, domin ɗiban dukkannin masu sha’awar Aiki da rundunar a matsayin ”Constable”, inda kuma ake tsammanin rufe shafin a ranar 26 ga watan Satumba mai kamawa (za a shafe makonni shida ana cikewa).
Ga Abubuwan da ake buƙata, ga dukkannin mai sha’awar wannan Aiki :
•Wajibi ne ya kasance haifaffen Najeriya, kuma ya mallaki lambar shaidar zama ɗan ƙasa ta NIN;
•Kada shekarun sa su gaza 18, kuma ka da su haura 25 (Daga 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Disambar 2022);
•Ka da tsawon sa ya gaza Mita 1.67 (ga Maza), haka zalika kada ya gaza 1.64 ga Mata;
•Kada faɗin ƙirjin sa ya gaza 86cm (Inci 34) ga Maza kawai;
•Wajibi ne ya kasance sakamakon gwajin lafiyar sa, daga Asibitin Gwamnati, ya bayyana bashi da wata matsala a zahiri, ko a ƙwaƙwalwar sa;
•Ka da ya kasance yana da wata nakasa;
•Ya kasance ba a taɓa kama shi da laifin satar kuɗi, ko zamba cikin Aminci ba;
•Wajibi ne ya kasance mai kyakykyawar ɗabi’a (wanda ba a taɓa tuhumar sa da Aikata wani laifi ba);
•Wajibi ne a samu shaidar kyawawan ɗabi’un sa, daga biyu a cikin waɗan nan mutanen : Mai Sarautar Gargajiya (Hakimi, Dagaci & Mai Unguwa), Alƙali, Shugaban ƙaramar hukuma, Shugaban Makarantar da ya kammala, Ma’aikacin Gwamnatin da ya kai Matakin Albashi na 12, Jami’in ɗan sandan da ya kai matakin CSP, ko Jami’in Sojin da ya kai Matakin Lieutenant Colonel.
åTAKARDUN KARATU :
Wajibi ne dukkannin wanda zai nemi wannan Aiki ya kasance ya kammala Sakandire, da sakamakon ɗaya daga cikin jarrabawoyin kammalawa (SSCE/GCE/NECO/NABTEB), kuma wajibi ne ya sami aƙalla Credits biyar (5 Credits), da su ka haɗar da Lissafi da Turanci (English & Mathematics) a jarrabawar ta sa.
√•ABABEN DA AKE BUƘATA YAYIN CIKEWA:
A ya yin da ka ke shirin cike wannan Application Form, kana buƙatar waɗannan Abubuwan :
a. Adireshin Email wanda ya ke amfani (Ka sani wannan Adireshin email ɗin da za ka bayar da shi hukumar ƴan sanda za ta dinga amfani wajen tuntuɓar ka);
b. Lambar katin zama ɗan ƙasa (NIN);
c. Sakamakon jarrabawar ka ta kammala Sakandire, wanda ka yi Scanning ɗinsa, da kuma takardar haihuwar ka (Birth Certificate);
åTSARIN YADDA AKE CIKEWA :
Bayan ka mallaki Soft copy na waɗancan takardun, sai ka ziyarci Adireshin www.recruitment.psc.gov.ng, Sannan ka aiwatar da Ayyuka kamar haka :
1• A shafin farko da zai nuna maka, sai ka danna wurin da aka rubuta ”Apply”, Sannan ka yi Sign up, ta hanyar amfani da Email Address ɗin da aka buƙa ci ka tana da, da kuma Password ɗin da ya kwanta maka a rai (ka yi amfani da Password ɗin da za ka iya tunawa);
2• Sai ka koma kan Email ɗinka, ka danna Link ɗin da za ka ga an turo maka, domin tabbatar da ingancin Email ɗin, da kuma Activating na Account ɗin ka;
3• Daga nan, zai mayar da kai shafin hukumar ƴan sandan, sai ka yi Sign in da Email da Password ɗin ka;
4• Bayan ya buɗe, sai ka shigar da dukkannin bayanan da ake buƙata, ka kuma yi Uploading ɗin takardun da aka buƙaci ka tana da, Sannan ka tabbatar lambar wayar da ka saka a shafin ka haɗa ta lambar katin ɗan ƙasar ka (idan akwai);
5• Ka duba bayanan da ka sanya da kyau, ka tabbatar ba bu kuskure, Sannan ka yi Submit;
6• Bayan ka yi Submitting ne kuma, za a Aike maka da saƙon da ya ke tabbatar da karɓar Application ɗin ka;
7•Bugu da ƙari kuma, Email ɗin yana ɗauke da Link ɗin da idan ka danna shi, zai jagorance ka zuwa wurin da za ka yi Printing ɗin Application Form ɗin ka, kana daga ɗakin ka, a kwance, wanda kuma da shi ne za ka halarci wurin Physical Screening, idan ka yi gamon katar ɗin samun gayyata.
KU SANI : Ba a biyan ko sisin kobo, a ya yin cike wannan Form, na neman Aikin Constable ɗin ɗan sanda (Sai dai idan ba a wayoyin ku ku ka cike ba, to za ku biya masu Cyber cafe abin da bai taka kara ya karya ba, a matsayin ladan cike mu ku da za su yi).