Gurbin Karatu: Gwamnatin India ta ƙarƙashin Ministry of External Affairs zata bawa ƴan Africa damar yin karatun online degree na farko da kuma na biyu (Masters degree) kyauta (100% scholarship)

 Gurbin Karatu: Gwamnatin India ta ƙarƙashin Ministry of External Affairs zata bawa ƴan Africa damar yin karatun online degree na farko da kuma na biyu (Masters degree) kyauta (100% scholarship)

Gwamnatin India ta ƙarƙashin Ministry of External Affairs zata bawa ƴan Africa damar yin karatun online degree na farko da kuma na biyu (Masters degree) kyauta (100% scholarship) daga manyan jami’o’i daban-daban na ƙasar kamar irinsu: Lovely Professional University (LPU), Indira Gandhi National Open University, Chandigarh University, Guru Jhambheswar University of Science and Technology, Aligarh Muslim University, da sauransu. 

Related topic:Call For Application: Apply For The Government of India under the Ministry of External Affairs will allow Africans to study online first and second degree (Masters degree) for free (100% scholarship)

Zasu baka damar yin karatun a fannoni daban-daban kamar: Science, Commerce, Computer Science, Management, Economics, Languages, Humanities and Arts, da sauransu. 

Da farko sun sanya international passport ya zama dole saida shi mutum zai iya cikewa, amma sakamakon ƙorafe-ƙorafe da akayi musu sun maidashi optional, ba dole bane yanzu. Katin zama ɗan ƙasa (National identity card) ya wadatar. 

Wannan dama ce babba da ya kamata ƴan uwa na ƴan Arewa suyi amfani da ita tun kafin ta kuɓuce mana. 

Degreen su iri ɗaya ne da na National Open University (NOUN), zan iya ce maka ma yafi nasu daraja domin shi wannan is recognized worldwide. 

Indai kana da lokacin da zaka hau Facebook, Whatsapp, twitter, dss, to ina tabbatar maka kasuwancin ka bazai hanaka yin wannan karatun ba. 

Da farko sun sanya 31st July, 2022 ta zama itace ranar ƙarshe, amman saboda maslaha sunyi extending ɗin died-line ɗin har zuwa 15th August, 2022. (yau saura sati biyu su rufe).

Wani abun burgewa da wannan degreen shine, a cikin shekara uku zaka gama, kuma babu ruwanka da yajin aiki (strike).

Site da zaka shiga domin applying shine: ilearn.gov.in

Idan ka shiga kayi register zasuyi verifying ɗin email ɗinka sannan zasu baka damar shiga cikin site ɗin nasu ka zaɓi course ɗin da kake so da kuma Jami’ar da sukeyi sai Kayi applying kawai. 

A ƙarshe ina fatan zakuyi amfani da wannan damar kafin ta kuɓuce.

NB:

Bana cikewa, zaka iya cikewa da kanka a wayarka, kokuma kaje Cafe mafi zama kusa dakai

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top