Hukumar zabe mai zaman kanta INEC Ta Bude Shafin Daukar Ma’aikata, Ga Cikakken Bayanin Yadda Zaku Cike Aikin

 Hukumar zabe mai zaman kanta INEC Ta Bude Shafin Daukar Ma’aikata, Ga Cikakken Bayanin Yadda Zaku Cike Aikin

Hukumar zabe mai zaman kanta INEC zata dauki sabbin ma’aikatan wucin gadi na zaben da zaa gudanar 2023 za’a bude manhajar yanar gizon daukar ma’aikatan da safiyar yau laraba karfe 8:00 14 ga watan satumba 2022 

Ku tabbatar kun cike dukkan ka’idojin da hukumar ta gindaya domin samun nasarar cin gajiyar shiga aikin. 

Dalilai barkatai da suke hana mutanan mu samun duk wani abu da gwamnatin tarayya ta bude, Abu na farko shine rashin karanta sharudan dake cikin yanar gizon wanda hukumar ta gindaya ,

Wurin neman aikin ko cike wani abu daban da gwamnatin tarayya ta bude ba’a bukatar mutum yayi gagawa abu a hankali wurin cikewa, ka tabbata abun da suka tambaya kasa a wurin kada ka sanya musu abun da basu bukata ba. 

Karanta ka’idojin yana da mutukar mahimmanci ga mai nema domin ta nan ne kadai zaka iya gano abubuwan daya dace ya nema dasu,dole mu bi a hankali mu natsu wurin karanta bayanai da hausa ko da turanci duk abun daka gani ba kayi tambaya ga wanda kasan ya fika ido a harkar abu mafi dacewa ga wanda ba zasu yi cikawa ba suyi Hanzari suje cafe mafi zama kusa dasu Domin cikewa.

Shawara ga masu nema aikin ko wani abu daban. 

Ku sane wani bawa bai isa ya baku abun da Allah bai kaddara ba, kada kace ka dade kana nema baka samu ba ka cigaba da nema ka sanyawa zuciyarka cewa Allah ne kadai zai kaddara ka samu ko rashin samun. 

komai lokaci ne a wannan rayuwar da kuke gani idan lokacin samun aikin ka baiyi ba wallahi tallahi ko shugaban kasa ne ya haifi ka ba zaka samu ba, idan ko lokacin samun aikin ka yayi zaka raina kaddarar silar samun aikin ka. 

Komai zamuyi mu nemi shawarar iyaye don su sanya mu acikin addo’in su Allah ka cigaba da ciyar damu alheri. 

Ga masu sha’awa sai su yi rijista ta wannan hanyar yanar gizo domin karantawa Dakuma yin rijistar http://www.inecnigeria.org

Domin cikewa direct Application ga portal

https://pres.inecnigeria.org/app/inec-iasd/how-to-apply

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top