DA DADAN KALAMAN SOYAYYA

DA DADAN KALAMAN SOYAYYA

-Kowa ne dare nakan koma gida ina kuka saboda nasan bazan kara ganin kiba har sai gobe Shin rana ce ta fito ko murmushin kine.


-Matata Uwar ‘ya’yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki ɗaya.


-ina cike da zumuɗin son dawowa domin cin girkin ki mai daɗi, ki kula min da kan ki, sai na dawo, Ina son ki matata.


-KUZO MU YABI UBANGIJI! Ya zama wajibi mu bude safiyarmu da fara salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, muyi Tasbihi da Hamdala a wajen gwani wajen iya tsara halitta, gwanin da idan ka kalli halittarsa sai ka rasa ta wanne wuri zaka fara yabo a gareshi, saboda yakai makura wajen kagar halittar da kyawunta ke ɗaukar hankalin duk wani me lafiyayyen tunani da idanun gani!

-Tabbas Gwanina Allahu, shine Allahu, shine me halittar akwai daga babu, ya samar da kyawu a inda babu shi, ya samar da nagarta a wurin da babu ita, ya samar da daukaka a cikin makaskanta, ya saukar da baiwarsa ta kamala da cikar haiba tare da zunzurutun Kyau akan wanda ya zaba a cikin halitta,


-Kyakykyawar zuciyar kice ta bayyana kyawawan halayyar ki, waɗanda suke sakamin cikakkiyar nutsuwa a cikin ruhina Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare.


-Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki. kasantuwar mu a raye cikin ruhi guda ɗaya ya sanya zuciyoyin mu bugawa cikin lokuta makamanta juna.


-Komai na mu ya kasance yana faruwa ne a lokaci guda hatta bakin ciki da kuma farin-ciki, wato ruhi ɗaya gangar jiki kuma biyu, Farin cikin ki shi ne nawa, ina son ki.


-Tabbas Ubangijina ya cancanci yabo ta kowacce fuska, bayan ni’imar rayuwa da ta lafiya da yayi mana, sai kuma ya kara mana da baiwar kasantuwar sanyin idanun mu a cikinmu, wadda muke kalla muji nutsuwa ta sauka a jikinmu, muji tabbas muma wasu mutane ne masu daraja, saboda kasantuwar me daraja a cikin mu.


-Barka da kasancewa cikin wannan rana masoyiyata. Dukanin rayuwata na karanta, nayi Mafarkinta, na jirata, nayi kuka don ita,


-yanzu haka na gano kece kadai abar kaunata, Tun farkon haduwata dake zuciya ta aminta dake a matsayin mai debe mata kewa, Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada.


-Nasan burina zai cika matukar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yanaba, Ina son ki fiye da zinariya.


-Wa kafi ƙauna? na ce, wannan da ta ɗauke ni wata tara a cikinta, ta haife ni tana farin ciki, sa’annan ta kyautata tarbiyata….

Wannan itace soyayya ta har abada, ba ta tsufa balle ta mutu.

 -Furannina furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai ɗauke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyoyi masu ɗauke da tsintsaye, sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki. Masoyiyata kece wadda zuciya ta ta aminta da ita.


-Ina son ki kara sani cewa babu wata ‘ya mace wadda zuciyata ta gama aminta da dukkan soyayyar ta face ke, Ina son ki.


-Ina Son Ki, ba da Zuciyata ba kuma ba da tunanina ba, Zuciya za ta daina aiki, tunani zai mance, Ina Son Ki da Ruhina ne, saboda Ruhi bai daina aiki, kuma ba ya mantuwa.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top