FITATTUN FINA FINAN KANNYWOOD GUDA (10) GOMA 2023

 FITATTUN FINA FINAN KANNYWOOD GUDA (10) GOMA NA 2023

(1) LABARINA

Labarina Series shiri ne da kamfanin Saira Movies na Malam
Aminu Saira ya dauki nauyin shiryawa
Takaitaccen bayana akan presdo da lukuma da kuma sumayya, shi presdo yana nuna kamar yafi lukuman qaunar sumayya to amma lukuman ganin yakai karyane shike yi Mata Soyayya ta gaskiya yana É—aukar presdo baida hankali ita kuma sumayya haryanzu bata yanke shawara akansu ba.

(2) IZZAR SO

Izzar so shiri ne mai dogon Zango na Bakori TV da jarumi Lawal Ahmad ke shiryawa, dubban masu kallo na zuwa su kalla,
 
Bayani akan hajiya Nafisa da matawalle da kuma hajiya sarah, hajiya Nafisa Tana nuna izza kwarai Wanda yasa ta jawo ma kanta makiya ciki harda hajiya sarah, to itadai hajiya sarah abin da tafi so shine ta mallaki dukiyar matawalle, shi kuma matawalle abin da yafi so shine yaga ɗansa Aliyu ya bayyana Wanda ya ɓata.

 Related Topic

(3) ALAQA

ALAQA na daya daga cikin fina-finan da ake
nema ruwa a jallo a masana’antar kuma
yana daya daga cikin fitattun fina-finan
kannywood na mako. Eh, wannan fim din
ALAQA fim ne na shahararriyar fim din FKD
wanda ke ci gaba da yi wa Ali Nuhu wanda
ake yi wa lakabi da Ali Nuhu Sarki.

Related Topic

ALAQA fim ne Wanda ke nuna cakwakiyar cikin gida misali, kamar Nameer da hisham basu jittuwa da juna, ita kuma anti hauwa abinda take so Nameer ya aure É—iyarta siyama shi kuma ba ita yake so ba.

(4) GIDAN BADAMASI

Gidan Badamasi sabon fim din wasan barkwanci ne da ake dauki ba daɗi a tsakanin wasu irin ‘ya’ya masu kunnen kashi da mahaifinsu Alhaji Badamasi.Badamasi dattijon attajiri dan kimanin shekaru saba’in ya yi aure-aure da dama a rayuwarsa, inda ya haifi ‘ya’ya masu
yawan gaske, wasu ma bai san ina suke ba a halin yanzu, A wannan wasan kwaikwayo an fara kai ruwa rana ne daga lokacin da Alhaji Badamasi ya kasa cika alkwarin kudin da ya yi wa ‘ya’yansa, Yaki ya barke a
tsakanin marowacin uba da hadamammun ‘ya’ya. Ba a taba yin fim kamar gidan badamasi a kasar hausa ba, Fim ne na barkwanci mai dauke da nishantarwa da
ilmantarwa ta hanyar amfani da gwanayen ‘yan wasan barkwanci ta yadda mutum zai yi ta zura idanu yana jiran ganin abin da zai faru a nan gaba.

(5) SANDA

Sanda Shirin daya kunshi, soyayya, bashin gaba, daukar fansa, cin amana, zalinci nuna fin karfi da yaudara.
Sanda Episode ne Wanda yake nuna wa mutun yanda zai dinga mu amala da mutanen kwarai da kuma yanda É—a zai nunawa uwarsa Soyayya da kuma budurwar sa, Sanda Film Ne na Daddy Hikima wato abale.

(6)ADUNIYA

Series din A duniya yana da matukar kayatarwa ga kuma dadin kallo, bugu da kari, duk sati suke sakin sabon episode.
Shirine Wanda Tijjani asase ke shiryawa Wanda akafi sani kanabaro shirin yana nuna yanda ake zaman duniya, Wanda ya kunshi komai, kamar sata, ‘yan daba, iskanci, sayarda kwaya da sauransu.

(7) UKU SAU UKU

Uku sau uku Shaharraran shiri mai dogon zango, daga kampanin Anfara Multimedia’
Shirin uku sau uku yana nufin  yanda zakayi hakuri da talauci kuma Kabi maganar iya ‘yenka sannan kuma Ka gudani cin amana.
Mai shirya Fim din shine, misbahu Anfara da kuma jarumi Abale.

(8) ASIN DA ASIN

Asin da Asin labarine na wasu mata biyu yaya da kanwa wanda suke soyayya da saurayi daya kuma kowacce su Tana Soyayya dashi amma ita guda bata son sa kawai suna maganane da saurayi kanwarta domin ita batasan yin aure yanzu.
Shirine na Shaharren jarumi wato adam a zango.

(9) WUFF

shiri ne daya hada chakwakiya iri daban
daban,Siyama da lilin baba.shirine daya Sami kyakkyawan aiki daga shahararren director Mai shirya Fina finai masu mutukar burgewa,lilin baba shine produced din wan nan film wanda ya hada da Ummi Rahab,Abdul M Sharif,Sarki Ali Nuhu,Dadai
sauran su kuci gaba da kasan cewa damu Dan cigaba da kallon shahararren Shirin Nan Mai suna WUFF.

(10) INA DA MATA

Ina da mata wani shirine mai dogon zango dake nuna abubuwa iri daban daban acikin rayuwa ayanzu tabbas wan nan shiri yana nunawa mata illar kishi mai yawa mace tace ita Sam baza akara mata kishiya ba tabbas hakan ba dai fai bane shirin yana fahim Tar da mata illar yin hakan.
Wanda ke shirya shi Shine Nazeer alkanawy.
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top