Ga Jerin kalaman Soyayya maza da mata

Jerin kalaman Soyayya maza da mata 

💓💔💪💕💖💜😄💞

Na maza

-Inaneman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.

-SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.

-Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!

-Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.

-Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!

-A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.

-masoyiya ta ina sonki fiye da yadda kike sona inason kasancewa tare dake domin kina faranta wa zuciyata kallon idonki kadai kan sani in samu kuzari duk wata kasala da lalaci inji ta gushe.

-Kece farin ciki da ina nan rike da amanar soyayyar ki har karshen rayuwa ta na saka araina bazan taba mantawa dake ba.

-Sonki tamkar wani fure ne da idanuwa ke kawatuwa da kallonsa, hanci yaji kamshi, ruhi kuma ya samu natsuwa.

-Idan rayuwa bazata yiwu ba tare da iska ba, haka nima bazan iya rayuwa ba tare dake ba Jindadi da walwala bazasu taba samuwa a tattare dani ba matukar babu soyayyar ki a cikin zuciya ta Kinzama tauraruwar dake haska ilahirin bishiyoyin da furannin da suke lambun zuciya ta.

Na mata

💙💘💟💞

-Tsuntsaye na bukatar fukafukai domin tashi, kifi na bukatar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bukatarka domin na yi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!

-Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka!

-A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son Ka!

-Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa fad’uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.

-Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ‘karshe, saboda kai ba saurayi ne kawai a waje na ba, ka zama ruhi na, sonka na yawo ne a cikin jinin da ke gudana a jiki na. Ina Son Ka!

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top