Ga wasu Zafafan Sakonnin Soyayya Masu Ratsa Zuciya

Zafafan Sakonnin Soyayya Masu Ratsa Zuciya

-Kin wadata zuciyata da farin ciki, kin haskaka rayuwata da haskenki, kulawarki agare ni ta musamman ce, hakan ya sa nakejin kaina tamkar sarkin wata masarautamafi girma da ƙarfin iko. Ina SonKi.

– Kece kaddarar da na jima ina tsimayin tararda ita a rayuwata, zan kasance a duk indakike, zan tsaya a duk inda kika tsayar dani. Ina son ki, adadin son da kalmomi bazasu iya siffantawa ba.

  -Inajin labarin soyayya ne a da, tamkar, tatsuniya amma a yanzu bayan na haɗu dake, na gaskata soyayya wata aba ce waddake da tasirin sanya farin ciki a cikin zuciya  Ina fatan zaki kasance tare da,ni domin zama maganin damuwata na tsawonrayuwa? Ina Son Ki.

 -Kodaa ce zaki sa wuta a jikina na babbake nazama toka, ba zan damu ba, matuƙar zaki ɗauke ni, ki kasance tare da ni a duk indakike. Fatana mu kasance tare da juna acikin wuya ko daɗi. Ina Son Ki.

 -Sonda nake yi miki, tamkar ruwan lemo neda ke rufe a cikin kwalba, irin wanda babuirin sa ko makamancin sa a faɗin wannan duniyar  Ina fatan zaki karɓa dominjin irin ɗanɗanon da ke kunshe a?cikinsa Ina son ki.

 -Tun ranar da na fara ganin ki, na ji a jikina wata rana hannuwanki zasu zamo masharin hawayena, kuma zasu kasance riƙeda ni na tsawon rayuwa  zuciyarki zata zamo makwancina na har abada. Na gode da irin kulawar da kike nuna min a.kullum Ina Son Ki Sosai.

 -Kinzamo cikin baitukan waƙar da zuciyata ke rerawa a kullum, waɗanda a dukkan lokacin da na ji su na kan ji dukkan damuwata na gushewa. Tabbas ina jinna kamu da son ki ne….. kai babu ko shakka matsanancin son ki ya shiga zuciyata Ina son ki ina kuma fatan zaki amince da ni a matsayin masoyi na hakika?

 -Sotamkar wutar murhu ne da ke ci a cikin zuciyar masoya Tini zuciyata ta babbake da son ki abar tinanina. Ina son ki, so mara. misaltuwa

-Ba zan taɓa mantawa da wannan ranar,ba wadda dare ya yi na kasa bacci a,cikinta saboda tsabar tinaninki, wato ranar da na fara ganin ki. Na Yi Kewar Ki.

 -Ke kaɗai ce nake gani kullum a cikin,baccina ke ce abar begena kuma ke ce wadda nake so, domin a gurin ki nake tsammanin samun farin cikin da nake fata. InaSon Ki

 -Akullum zuciyata kan nutsu ta yi tinani, domin tsara sakon da zan aikewa da abar tinanina a dare ko rana domin ganin yalwatuwar murmushi a saman fuskarta. Inafatan sakonnin nawa suna yin tasirin sanyaki farin ciki? Ina Son Ki

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top