GARE KU MASOYA KALAMAN SOYAYYA MASU DADI

GARE KU MASOYA KALAMAN SOYAYYA MASU DADI

Assalamu alaiki abin alfahari Na jinin dake yawo acikin jikina, 

“Kin kasance abar so da muradin mallaka ga duk idaniyar da tayi arba da kyakkawa Mai cike da siffofi kyawawan da sun wuce kwatance,misali,da duk wani kiyasin mai kiyasi. 

Kina da kira da sura irin ta matan izza,matan mulki, matan isaa da tinkaho. Fahimta fuska,zuciya ma’aunin mizani. faidar darasi da ilimi. 

 fa’idarsoyayyah cikar burin zukata biyu. kin kasance abar kaunata da bege a yayinda zuciya ta ta bace kuma ta makance a cikin duhu da surkukiyan tausayin kaunar ki Babu kamar ki a wajena kin sani, ke ce muradi na kuma ke nake gani naji zuciya tay sanyi.

kin sace min zuciya a yayinda na kasamallakar kaina. dubun gaisuwa ma tashi tare da fiffiken so ta tabbata a gareki ya ma’abociyar dukkan ni’ima,kin fice kin barsu, ba yadda suka iya,zinariya abar son kowa, barin ruwa kin fi a kwashe, 

Inayinki tawa wanda yayi arba da su atasayen nutsuwa kina da siririya, tattausa kuma zazzakan murya mai sanyi mai sauraro a cikin tausayin kauna burina naji ki a kusa dani a lokacin da numfashin mu zasu rinka gauraya ta yadda zamu rika jin sautin bugawan zuciyoyin mu atare. ke sarauniya ce, gimbiya, kuma tauraruwa mai haskawa a cikin jerin taurari

Ina son yadda ki ke so na, kada ki yasar da ni, kada ki taba juya min baya. Ina sonki,

Tabbas,‘ ina matukar ka’unarki, kuma ina son kasancewa miji a gare ki har abada, don Allah ki kasance tare da ni,

Ina _fatan kin fahimci cewa zan so ki har karshe, saboda ba kin kasance budurwata kadai ba, ke ce Aminiyata. 

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top