HUKUMAR (NITDA) ZA TA BA DA HORAR GA ƳAN NAGERIYA MUTUM (MILIYAN ƊAYA 1) DOMIN YIN DOGARO DAKAI

 HUKUMAR (NITDA) ZA TA BA DA HORAR GA ƳAN NAGERIYA MUTUM (MILIYAN ƊAYA 1) DOMIN YIN DOGARO DAKAI

Hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ta ƙarƙashin cibiyar ƙere-ƙeren na’urorin zamani, “National Center for Artificial Intelligence & Robotics,” (NCAIR), za ta ba wa ƴan ƙasa horo akan yadda ake ƙera na’urorin fasahar zamani, gami da yadda ake sarrafa su.

Horon wanda za a gudanar shi rukuni-rukuni, na zaman wani fanni na wani shiri na musamman da hukumar ta (NITDA), ta tsara domin horar da ƴan Nageriya mutum miliyan 1.

Wannan wata dama ce ga duk wani ɗan ƙasa wanda ya kai shekaru 15 a duniya, ya ke kuma zaune a birnin tarayya, Abuja, ya ke kan karatun sakandire ko digiri ko ya ke kan aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC), da duk wani wanda ya ke da sha’awar samun horo kan fasahar zamanin, abin duba dai, horon a zahiri ne a birnin Abuja.

Waɗanda su ke matsayin ƴan koyo ko masu fara koyo, za su bi wannan mahaɗa, (Link) su cike buƙatar shiga: https://bit.ly/3SvJ2Zy

Waɗanda kuma su ke da ɗan ilimi akan fannin, za su bi wannan: https://bit.ly/3Szm17R

Tun daga yanzu ƙofa a buɗe take ga duk mai sha’awa, a kuma wannan wata za a gudanar kamar yadda aka bayyana hakan a shafin sadarwa na cibiyar ƙere-ƙeren ta ƙasa, (NCAIR).

Rubutawa

Idris kililin Hadejia

Kuci gaba da kasancewa da Shafin Agajahub publishers Domin samun ingantattun labarai Dangane da Daukar Ma’aikata Tallafin gwamnatin Tarayya dama Tallafin karatu Sana’a dadai sauransu.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top