JERIN JARUMAI WADAN DA SUKAFI KUDI ACIKIN MASANAN ‘ANTA KANNYWOOD GUDA GOMA (10)

JERIN JARUMAI WADAN DA SUKAFI KUDI ACIKIN MASANAN ‘ANTA KANNYWOOD GUDA GOMA (10)

(1).NAZIR M AHMAD SARKIN WAKA

Nazir M Ahmad mawaki ne a masana’antar Kannywood jaruma a wani bangaren, mawaki ne wanda akayi yayinda kuma ake yayin sa a harzu haka, kuma yana taka leda a matsayin jarumi a fim din LABARINA, Kuma yana daya daga cikin jaruman da keda maƙudan kudade a masana’antar, Sarkin Waka yana samun kuɗi ne ya hanyoyi kamar haka.
Kamar yanda muke gani Sarkin Wakar ya fara fitowa a fim duk da ba shine lokacin sa na farko ba, kuma dashi ake shirya shirin LABARINA, tabbas Sarkin waka yana samun
kuɗi ta hanyar fim. Kuma Naziru ya kasance ana gayyatar sa dina ko fati idan ana daurin aure, yanayin waka kuma a biya shi, Akwai wasu hanyoyi da dama wanda Sarkin Wakar yake samun kuɗi bayan wadannan.
Darajar Naziru Sarkin Waka tana kaiwa kimanin,
net worth of 230 million Naira.

(2). Ali Nuhu

Ali Nuhu jarumi ne kuma darakta ne a masana’antar Kannywood, wanda aka fi sani da Sarki Ali, ambasada ne na akalla kamfanoni guda bakwai a Najeriya cikinsu akwai Glo, Omo, Samsung da dai sauransu.
Bayan kungiyar Kannywood da Ali Nuhu yake taka rawa akwai kuma kungiyar Nollywood dake kudancin kasar nan wadda
dan wasan yake nuna bajintarsa a can. Jarumin yayi fina-finai a kamfanin Kannywood sama da guda dari, irinsu Jinin Jikina, Matar Aure, Gani Gaka, Mansoor, Adamsy, Dawo Dawo daidai sauransu.
Sannan kuma jarumin an nuna shi a fina finan Nollywood irinsu, Last Fight to Abuja, Memories of my Heart, Beautiful
Soul, Hamza, Brothers Apart, Widow Tears, Royar Treasure da dai sauransu.
Wannan dalili ne yasa jarumin ya zama na farko a cikin jaruman da suka fi kudi a masana’antar ta Kannywood.
Kimanin Darajar kudin Ali Nuhu yana kaiwa kimanin,
net worth  of 180 million Naira

(3). DAUDA KAHUTA RARARA

Dauda Kahutu Rarara wanda aka fi sani da Rarara, mawaki ne na siyasa, wanda yake da kusanci da manyan ‘yan siyasa na kasar nan, an bashi mukamin babban darakta na mawakan shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin yakin neman zaben shugaba Buhari a shekarar 2019, Wannan suna da kuma daukaka da Dauda Kahutu Rarara yayi shine yasa ya zama mutum na uku a cikin jerin wadanda sukafi kudi a kungiyar ta Kannywood.

Darajar kudin Dauda kahutu Rarara ya kaiwa kimanin,

Net worth N160 million

(4). ADAN A ZANGO

Adam A Zango mawaki ne kuma jarumi wanda aka fi sani da Prince Zango, Yana da wani katafaren gida a jihar Kaduna, yana kuma da masoya da yawan gaske.
Adam A Zango ambasada ne na kamfanin MTN, a shekarar 2016 Adam A Zango ya wallafa wani rubuta a shafinsa na Instagram cewar ya bar fim, inda ya ce zai koma bangaren waka da shirya fina-finai, sai dai kuma wani labari ya fito daga makusantansa cewa yayi amai ya lashe, Zango yayi fina finai shima sama da guda dari irinsu Nas,
Gwaska, Basaja, Gamdakatar da dai sauransu. Wannan ne ya sanya jarumin Adam A Zango ya zama na biyu a cikin jerin
jaruman.

Kimanin Darajar kudin adam a zango ya kai wa kimanin, net worth 130 million Naira. 

(5). NURA M INUWA

Nura M Inuwa mawaki ne a bangaren soyayya, yana daya daga cikin masu kudin kungiyar Kannywood, yana fitar da wakoki
masu yawan gaske kowacce shekara, kyakkyawa ne, kuma shine na hudu a cikin jerin jaruman.
Kimanin Darajar kudin Nura M Inuwa yana kaiwa kimanin, Net worth N45 million

(6). Sani Musa Danja

Sani Musa Danja wanda aka fi sani da Sani Danja shine ya zo matsayin na shida a cikin jerin jaruman, jarumi ne kuma mawakin siyasa, yana da wani katafaren gida a babban birnin tarayya Abuja.
Kimanin Darajar kudin sani Danja yana kaiwa kimanin, net worth of 75 million Naira 

(7). Sadiq Sani Sadiq

Sadiq Sani Sadiq wanda aka fi sani da Gambo Uban Tani, yana daya daga cikin wadanda suka fi kowa iya kwalliya a cikin
jaruman Kannywood, sannan ya karbi lambar yabo ta gwarzon dan wasa a kungiyar, hakan ya sa ya zama na bakwai a cikin jerin jaruman.
Kimanin Darajar kudin Sadiq sani Sadiq yana kaiwa kimanin,Net Worth N35 Million

(8). Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi ita ce ta zo ta takwas a cikin jerin jaruman da suka fi kudi a kungiyar ta Kannywood, sannan kuma ita ce ta biyu a cikin jarumai mata a kungiyar.
ba iya fim da talla kawai jarumar keyi ba harda kasuwanci, domin kuma itace mamallakiyar kamfanin NafCloset kamfanine na siyar da kayan sawa da takalma da jakun kuna na mata, da kuma kayan kwalliya da sauran su. 
Darajar kudin Nafisa Abdullahi yana kaiwa kimanin, Net worth N21 million

(9). Hadiza Gabon

Hadiza Gabon jaruma ce ita ce kuma ta zo ta tara a cikin jerin jaruman sannan kuma ita ce ta uku a cikin mata, Tana daya daga cikin manyan jaruman da suke son ganin sun taimakawa al’umma.
Darajar kudin hadiza gabon yana kaiwa kimanin, Net worth N25 Million

(10). Aisha Aliyu Tsamiya

Aisha Aliyu Tsamiya wacce aka fi sani da Aisha Tsamiya, kyakkyawa ce ta gaban kwatance tayi fina-finai masu tarin yawa, ita ce ta samu nasarar zuwa ta goma a cikin jaruman sannan kuma ita ce ta zo ta hudu a cikin jarumai mata na masana’antar ta Kannywood.
Darajar kudin Aisha Aliyu Tsamiya yana kaiwa kimanin, Net worth of  N5.7 million naira

Wanan Bayanin anyishine bisa hasashe bawai tabbatattun alkaluma ne Suka sanar ba, dafatar kun ilmantu da wannan hasashe na Agajahub publishers

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top