Kalamai Masu Ratsa Zuciyar masoya

Kalamai Masu Ratsa Zuciyar masoya

Na maza

-Za ki fahimci ma’anar soyayya, da kuma
irin muhimmancin girman son da nake
nuna miki, a lokacin da aka ce na mutu ba
na raye. Har Yanzu Ni Dai Ina Son Ki.
-A kullum zuciyata kan nutsu ta yi tinani,
domin tsara sakon da zan aikowa da abar
tinanina a dare ko rana, domin ganin
yalwatuwar murmushi a saman fuskarta.
Ina fatan sakonnin nawa suna yin tasirin
sanya ki farin ciki? Ina Son Ki
-A dukkan lokacin da masoyi ya rabu da
abar ƙaunarsa, ya kan tsinci kan sa cikin
kaɗaici da damuwa na tsawon lokaci, ya
kan tsinci kan sa cikin rashin yarda da
gujewa amincewa sauran mata. Ki kasance
tare da ni na tsawon rayuwa, karda ki bari
zuciyata ta ɗanɗani raɗaɗin zafin rabuwa
da abar so. Ina Son Ki
-So shi ne abu mafi tasirin warkar da
kowane irin ciwo a cikin zuciya, kuma shi
ke sanya mu jin kanmu a matsayin wasu
mutane na musamman, a dukkan lokacin
da muke tare, Na Yi Kewarki.
Shigowar ki cikin rayuwata, gami da irin
tsantsar son da kike nuna min, sun zama
dalilan yin murmushina a kowane lokaci.
Ba ni da wata da nake so sama da ke. Ke ce
ƙarfina, ke ce karsashina. Ina Son Ki

-Kowace soyayya da kike gani, tana
samuwa ne a bisa wasu dalilai, saboda
haka, ina son bayyana miki cewa, ina son
ki ne saboda kece da ma wadda zuciyata
ta daɗe tana jira. Ina tare da ke a duk
inda na shiga, Ina Son Ki.
-Matsayinki a gare ni, tamkar na wani
dutse ne na musamman da yake jikin wani
zobe, wanda ya kasance a dukkan lokacin
da babu shi, zoben zai zamo mummuna
mara daraja abar nunawa. Ki kasance tare
da ni masoyiyata. Ina son ki, so mara
misaltuwa.

Na mata

-A lokacin da ka shigo cikin rayuwata, na ji
tsoron kar ka raunata zuciyata, amma
yanzu da na same ka, ina jin fargabar rasa
ka. Ina fatan zuwan ranar da zan zamo
mata a gare ka. Ina Son Ka.
-Ina son kasancewa ne tare da wanda zai
kasance cikin saka ni farin ciki, ya sa ni
murmushi a lokacin da nake cikin
damuwa, wanda zai kasance cikin so na a
kowane irin yanayi. Na san babu wanda
zai iya hakan sai kai, a saboda haka nake
kara bayyana maka cewa, ina son ka.
-Ina fatan zuciyata da taka su narke su
zama abu guda, har zuwa ƙarshen rayuwa.
Zan kasance cikin yi maka addu’ar samun
nasara a dukkan al’amuranka, kuma zan
kasance cikin son ka har ƙarshen
rayuwata.
-Idan har da a ce wasu zasu tambaye ni
wanda nake fatan na aura, amsar ba zata
wuce kai ba, domin kai ne wanda zuciya
ke fatan ta kasance tare da shi har abada.
-Wanda nake fatan na aura, mutum ne na
musamman mai baiwa ta musamman a
cikin dubunnan samari, shi ne wanda zan
iya kasancewa tare da shi a cikin wuya ko
daɗi, domin na san tinaninsa a kullum, bai
wuce neman hanyar da zai inganta
rayuwata ba. Ina Son Ka.
Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top