KALAMAN SO DA ƘAUNA MASU SANYAYA RAI

KALAMAN SO DA ƘAUNA MASU SANYAYA RAI

 -BudeminNashigo Kofar Zuciyarki Da Sannu Zan Zamo Dauwamammen Farin Cikin Da Zai Bunkasa Dukkan Wani Farin Cikin Rayuwarki.

-Assalamu Alaiki Yake Haƙiƙar Halittar Da Bayananina Suke Nufi, Nazo Da Murna Zuwa Murmushi Da Farin Cikin Shaukin Samun Damar Ganin Kyawun Nasabarki.

Kicemin Marhabun Yaka Taho Dan Gata Zuciyata Kazo Zan Baka Ruwan Hawayen Idanuwana Suna Kwaranyane Sanadin Nemanka.

Annashuwa Da Shauki Ne Zasu Biyo Baya Farin Ciki Marar Misalin Adadi Shine Zai Rufe Dukkan Wasu Kofofin Damuwata.

-Zuciyata Tana Miki Sallama Ta Masoya Jinin Dake Kara Kuzari Ajikina Shima Yana Ladabin Gaisuwa Agareki.

-Yar Asalin Kyau Mai ƙirar Hanci Siriri Matsakaici Kinada Kyawun Halitta Da Tsarin Iya Kwalliya Akan Burgewa.

-Sonki Ne Kadai Akan Tsarin Dukkan Tunanina Komai Nisan Dare da Tsawon Wuni, Iya Wuya Tunaninki Ne Akan Kwakwalwata.

-Kallon Tsakiyar Idanuwanki Suna Saukar Da Sabuwar Ni,ima Acikin Jikina Ta Hanyar Hakane Nake Kara Kaimi Wajen Ganin Nasamu Ganinki Akowace Rana.

-Sallama Agareki Tare da Sako Na Musamman Wanda Ya taso Daga Farkon Numfashin Zuciyar Dake Kiran Sunanki Akowane Bugun Numfashi.

-Kin Isa Ayi Miki Komai Shiyasa Na Mallaka Miki Abin da Yafi Komai Muhimmanci Acikin Jikina Wato Zuciyata.

-Na Gamsu Kuma Na Aminta Da Yawan Amanarki Shiyasa Na Damka Miki Amana Mafi Girma Acikin Rayuwata Kici Gaba Da Bani Kulawa Ni kuma Zan Cigaba Da Kyautata Miki Iya Tsawon Adadin Kwanakin NumfashinRaina.

-Kin Samu Kyakkyawan Matsuguni Acikin Raina Ina Alfahari Da Kasantuwata Acikin Rayuwarki Komai Wuya Zan Cigaba Da Kyautata Miki.

-Rabbi Sarki Mahallicin Bayi Nake Roko Yasanya KinaCikin Koshin Lafiya.

-tsamanin Son ki ne Yake Dauke Da Al”adun Kafuwar Tarihin Rayuwar Kaunarki Wadda Ta Nashe zuciyata Nakamu Da Tsananin zillar Azabar zumudin Sonki Wadda Hakan Ya Haifar Da Aukuwar Karuwar Begenki.

-Barka da kasancewa cikin wannan rana masoyiyata. 

-Dukanin rayuwata na karanta, nayi Mafarkinta, na jirata, nayi kuka don ita, yanzu haka na gano kece kadai abar kaunata. 

-Tun farkon haduwata dake zuciya ta aminta dake a matsayin mai debe matakewa. Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har, abada

-Nasan burina zai cika matukar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana. Ina son ki fiye da zinariya.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top