Kalaman Soyayya Domin Masoya Maza Da Mata

Kalaman Soyayya Domin Masoya Maza Da Mata

ZUWA GA MASOYIYA TA

KIN YI WA SAURA NISA

-Son Ki ya mamaye dikan zuciyata. Ina kallonki ne tamkar tauraruwar nan da ta yiwa saura nisa, Ki huta lafiya.

BANIDA KAMAR KI

-Kalmomin da a kowane lokaci nake farin cikin furta su gare ki su ne, Kodan na san tini kin daɗe da sanin adadin yadda nake son Ki, nake kuma ƙaunar Ki sai dai kawaina ce bani da kamar KI, Burina a kullum bai wuce na ganin na mallake ki ba harabada.

KIN ZAMO FITILAR ZUCIYA

-Na kan ji wani abu a cikin zuciyata, ba komai bane face fitila wadda ke kunnuwa adukkan lokacin da na sanya idanuwana acikin naki, Ina son Ki fiye da yadda alamunhakan ke bayyana a saman, fuskata Ki huta lafiya.

KIN ZAMO CIKIN TINANINA

-Kina daga cikin mutanen da ba zan taɓa mantawada su ba a rayuwata, Kin zamo cikin tinanina, Bana fatan zuwan wani abu dazai zamo silar rabuwar mu, ko da a ce mutuwace. Ina Son Ki.

KI KALLI SAMANIYA

-Ki kasance mai ɗaga kanki Ki kalli sararin samaniyaa cikin kowane dare, karda ki furgitaa lokacin da kika hango wata mai tsananin haske, ni ma na yi hakan kuma nasamu ganin wata tauraruwa mai haske idaniyada kore damuwar zuciya wato ke. InaSon Ki.

KE CE A ZAHIRI KUMA KE CE A CIKIN BACCINA

-A kullum na kan kwanta da tinaninki, na kuma farka a cikin mafarkina, na gan ki zaune kusa da ni, a cikin wani lambu ma’abocin tsintsaye da furanni, Tabbas a lokacin murmushinki ya fi komai jan, hankalina muryarki kuma ke samar da, nutsuwata Ki Huta Lafiya.

ZUWAGA MASOYI NA

ZAN YI RAYUWAR ƘUNCI IDAN BABU KAI

-A dukkan lokacin da ka furta baka so na, babu inda ya fi dacewa da na ci gaba da rayuwaa cikinsa face kabari, domin kuwa nasan daga ranar duniya za ta zamo wajen zubar hawayena, Ina Son Ka.

AKWAI WANI SIRRI CIKIN IDANUWANKA

-Rayuwata ta kasance rataye cikin tarkon, soyayyarka ka ɗana kuma ya kama ni. A dukkan lokacin da na kalli ƙwayar, idanuwanka na kan ji wani shauƙi mara, misaltuwa Ina Son Ka.

KAI NE ABUN SON KALLON IDANIYATA

-Ina cikin kewarka, ina cike da ɗaukin son ganinKa, a cikin kowace rana son ka na lunkuwa a cikin zuciyata, fiye da yadda fatar bakina za ta iya furta hakan, Ka huta lafiya

BANA FATAN CANJUWAR RA’AYINKA A KAINA

-Abu mafi tsanani wajen sanya zuciya a damuwa shi ne, ka samu wanda kake so shi kuma a lokacin ya faɗa a son wata. Banafatan hakan ya kasance a tsakanina dakai, Ina Son Ka! Ina Son Ka!! Ina SonKa!! Masoyina.

FATANA MU KASANCE TARE HAR ABADA

-So abu ne mai wahalar da zuciya da kuma sanyata nishadi, Zan so ka kasance cikin bani kulawa domin gujewa faɗawa wahalarta so, Ba zan taɓa canja ra’ayina a kanka ba har abada, Ina Son Ka.

Agajahub publishers

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top